← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 52

Sashe 32

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dayake Inna ba ta hana su duk abin da suka yi ninya, bata damu ba da Arab ta sanar mata tafiyan, farin ciki ma tayi sabida jin zata koma wajen Alhajin nan, ta san zasu samu tagomashi ne shiyasa take murna, tunda duk abun da za'a ce kuɗi to magana ta ƙare, duk ita suka biyo ta koya musu son kuɗi da neman sa ko ta halin ya ya ne

Ranan Alhamis suka yi sallama da Tariq don a can gidan shi ma ta wuni. Yana ta mata ƙorafin tafiyan duk da bai san me zata je yi ba, kuma ta ƙi sanar mishi tunda ba kasafai ta cika ƙarya ba, ƙiri-ƙiri zata bayyana wa Mutum, "ba hurumin ka bane." Idan kuma zata faɗa maka to kai tsaye zata sanar maka don babu ɓoye-ɓoye a tare da ita, sai idan ta so ne take iya yin ƙarya, amma komai nata ƙuraratan ne don ba ta shayin ko waye ne

Shi kansa ya san halin ta a wannan ɗan ƙanƙanin lokacin da suka yi, shiyasa bai ja zancen ba tunda ta ƙi sanar mishi, kuma ya buƙaci, "zai bi ta can ɗin, su je tare."

But tace, "a'a ba ta buƙata."

Dole ya ƙyale ta suka sha love ɗinsu, sai dare ya mayar da ita gida

Washe gari kuma ta wuce Kaduna daga can ta hau jirgi zuwa Legos. Ta sauka da la'asar; kamar yanda wancan suka zauna a hotel wannan ma a can ne masaukin su. Gaskiya ta ji daɗin zuwa Legos ɗin don ba kaɗan ba rayuwar can yayi mata daɗi, irin rayuwar da take so kenan, shiyasa kullum sai sun fita, ko basu fita da Alh. Bashir ba zata fita ita kaɗai, a haka ne yasa ta samu friends irin gogaggun ƴan duniya asalin karuwan can, don har club take zuwa a can ta haɗu da su, zamanta a can ɗin ya sa ta sake wayewa idanuwanta sun buɗe sosai. Shiyasa bata so suka bar can ɗin ba sabida zaman yayi mata daɗi, musamman yanda suke fita outing da Abokanan ta, ga samari ƴan duniya masu hannu da shuni da ta sake cin karo da su. Kwanan su goma sha biyar suka wuce Jigawa, duk da ta so komawa gida amma Alhajin ya hana ta komawa, sai da ta ci kuɗi sannan ta amince mishi suka tafi

Koda suka je can ɗin ma kullum cikin hutawa suke da Alhaji tunda kullum yana gida suna manne da juna, sai yayi kwana biyu ma bai fita ba tunda meeting ya zo yi dama, kuma meeting ɗin ya ƙi ƙarewa ana ta cin lokaci

A ɗan wannan satikan da Arab tayi cikin hutu da jin daɗi ba ƙaramin canzawa tayi ba, ta sake yin ƙiba ta murmure hutu ya zauna mata tunda tana jin daɗi sai abun da tace tana so, bata da damuwar komai kullum cikin hutu take, sai dai ta aika wa su Inna da kuɗaɗe su ma su dangwali arziƙi

Babu abun da ya shalli Inna tunda burin ta ya cika, suna samun kuɗi sun fi ƙarfin komai, har kayan ɗakinta ta canza komai da komai, aka soma gyaran gidan ana ta canza filasta da penti, duka har su Ummu duk babu wanda ba ya taimakawa tunda su ma suna samun kuɗin samarin

Baba dai nashi ido ne tunda yanzu ba sosai yake fita wajen suyan nashi ba sakamakon jikin sa babu wani daɗi, ba komai yake tsinana musu ba domin shi kansa sai Inna ta dafa ta ba shi ya kan samu

Shiyasa kullum cikin gori take mishi, tayi ta tsiya bakin ta ba ya shiru ko kusa ba ta tausayin shi, wai, "kullum a haka zai ƙare zuciyarsa ta mutu yana gida ba ya tsinana musu komai sai dai ya ci, shi bai ji kunya ba ma ace Matarsa ce take ciyar dashi ko Yaranshi?"

To ta fi ƙarfin shi ba ya da bakin ma mayar da martani tunda ya san halin ta, amma kuma yanzu dai yana ɗan lallaɓawa ya fita ko ya ya ne ya samo duk da nashi ba a bakin komai yake ba, idan ma ya bata kuɗin sai dai ta amsa ta ajiye ba dashi zasu yi girkin ba

Ta kance, "uban me wannan kuɗin zai yi musu? Ta dai amsa don raba mugu da makami ibada ne; amma ba don wai zata yi amfani dashi ba."

Wannan jaraba na Inna Harira kullum gaba yake yi kwata-kwata ba ta tausaya wa Baba, duk wani ciwo ma da yake yi baƙin cikinta dana Ƴaƴanta shi yake haifar mishi, tunda kullum cikin damuwa da tunani ba shi da sukuni, a haka kullum yake shiyasa yau ciwo gobe lafiya abun ya ci ƙarfin shi, asibitin ma ba ya iya zuwa tunda ba ya dashi sai dai ya je chemist ya siya magani, Inna bata taɓa damuwa da damuwar shi ba ita dai idan bai kawo ba ta dinga jaraba kenan har sai wunin ranan ta gushe, ƙarshe sai dai ya bar mata gidan

Ko kuma tace, "ya ga don yaran suna samu ne shiyasa yake wani langaɓe wa a gida yana son dena fita nemowa, amma ada har dashi yake musu baƙin ciki da hassada yanzu kuma ya zo yana ci, ai da yayi zuciya ya barsu su ci kayan su kawai".

              **********

             Yau Arab ita kaɗai ce sabida Alh. Bashir ya fita tun safe, dayake yau ne zasu ƙaddamar da meeting ɗinsu na ƙarshe wanda suke sa ran samun matsaya a kan kasuwancin nasu da suke ƙoƙarin haɓaka shi, zuwa gobe ko jibi kuma sai su wuce

Arab kaɗaicin ya ishe ta shiyasa ta tashi ta zura dogon Hijab Robber purple a saman kayan jikinta, dayake kayan shan iska ne gajeren wando blue Black, sai vest pink color mai taushi da siraran hannu. Komai na jikinta ana gani duk da ta saka Hijab ɗin; don da shi da babu duk ɗaya ne, albarkatun jikinta tamkar a waje suke don yanda suke kaɗawa dole ne duk wani namiji mai lafiya ya ruɗe, but ita babu ruwanta haka ta fice tana kaɗa jiki cikin tafiyanta na yanga da ɗaukar hankali, duk inda ta wuce kuwa kallonta ake yi don majority mutanen da zata haɗu da su a hotel ɗin idanuwansu yana kanta. Ita kuwa hankalinta yayi gaba wajen waya da Bestyn ta, sai dariya take yi cikin nishaɗi har tana sanar mishi, "yanzu ne ma ta fito zata ɗan sha iska don ta gaji."

Yayi dariya yace, "ai na faɗa miki kin samu duniya yanzu babban yarinya, yanzu sai hutu da jin daɗi kike ba ki da wata matsala, Ni na ƙosa ma ki dawo don nayi kewar ki sosai, yaushe ne za ki dawo don Allah?" Ya ƙare maganar cikin narke murya da salon jan hankali

Dayake already ta fice daga hotel ɗin, ta fita zuwa bakin titi tana kallon mutane sai ta jingina da wata mota da ta gani, a nan ta tsaya tana ci gaba da waya dashi suna ta dariya da nishaɗi; wanda hakan ya ɗauke mata hankali har tana hayewa saman motan

Ashe na wani Alhaji ne yana ciki a zaune, kasancewar wurin akwai irin manya-manyan shagunan nan; yana tare da Matarsa ta tsallaka siyayya, hawa motan da tayi ne ya ja hankalinsa gare ta, sai ya fito daga cikin motan da ninyar yin mata masifa, amma yana yin tozali da ita ta ja hankalinsa, zuciyarsa nan da nan ta kwaɗaita da ita tunda shima ɗan hannu ne, har wani haɗiye yawu yake yi tsaban jaraba. Wajen ta ya nufa yayi mata sallama

Dalilin da yasa ta katse kiran tana mayar da hankalinta a kanshi tare da kallonsa sama da ƙasa

Shi kuma yayi mata murmushi yace, "sannu ƴan mata."

Murmushin itama ta maida mishi tana dirowa daga kan motan tare da amsawa

Yace, "But here you are or you will pass?"

"No, Ina nan ne. I am in this hotel."

Abun da yake son ji kenan shiyasa nan da nan ya washe baki yana cewa, ""If you don't mind, give me your phone number. I often come here; or we will meet together."

Dariya tayi mai jan hankali, sai ta ɗage kafaɗa tace, "ok fine." Daga nan ta soma karanto mishi Numban

Ashe fitowar matar shi tana hango su, kuma ita ga ta akwai shegen kishi, tunda ta hangi Arab nan da nan hankalinta ya tashi zargi ya ɗarsu a zuciyarta, tsaban kishi ya ci ranta tana zuwa wajen ta zubar da kayan hannunta bata yi wata-wata ba ta cakumi wuyan Arab

Basu an kare da zuwan nata ba shiyasa sai ganin ta suka yi

Kafin Arab ta farga Matar ta wanka mata mari tana cewa, "dan kutmar ubanki me ya haɗa ki da Mijina? Dan ubanki nace mai ya haɗa ki da Mijina iyee karuwan Banza?"

Da sauri Alhajin ya soma ƙoƙarin fincike hannunta yana cewa, "Ke.. ke Lubna mene ne haka? Ba ki da hankali ne?"

Ita kuwa Arab tunda taga Matar ta sake ta sai itama ta wanke ta da marin cikin zafin nama, tare da cewa, "uban ki ne ya haɗa Ni da mijinki dan durun uwar ki."

"Ni kika mara? Ni?" Matar ta furta cikin tsantsan mamakin Arab ɗin, musamman yanda ta ganta ƙaramar yarinya a kanta, but har ta cire hannu ta mare ta bayan ita tayi mata laifi

Hankalin Alhajin ya tashi don ya san halin matar shi, shiyasa yayi saurin shiga tsakani yana jan hannunta da cewa, "dama kin saba ja min magana Lubna, yanzu ma a nan sai kin kwance min zani a kasuwa? Ki wuce muje da Allah."

"Wlh bazan tafi ba, kana ganin yanda ta mare Ni kake cewa in tafi? Tunda ba ka da gaskiya mugu azzalumi ai dole ka ce in tafi." Sai ta fashe da kuka tana ƙwace hannunta

Ita kuwa Arab tana tsaye a wurin don ko gezau bata yi ba, kuma ba ta shakkar duk abun da zai faru, tana gani yanda mijin yake lallaɓa matar don su tafi amma ina ta kafe sai ta ci uban Arab; shi kuma ya hana ta ya shiga tsakani
Chapter 32 · 0% Book details