← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 52

Sashe 10

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Sinior ya bi shi da kallo yana cewa, "ina kuma zaka je?"

"Zan shiga ciki." Yayi maganar ba tare da ya juyo ba yayi tafiyar sa

Sinior shima ɗage kafaɗansa yayi before ya miƙe ya doshi hanyar fita gidan gaba ɗaya.

          Malik na zuwa babban falon su ya ci karo da Mummyn su

Ganin shi yasa tace, "Malik zo nan, me ya haɗa ku da Nawwara ne wai? Yanzu ta shigo tana kuka tayi ɗakin su Zainab."

Yatsina fuska yayi, sai kuma ya taho yana zama a gefen Mummyn tare da cewa, "me tace miki nayi?"

"Idan da ta faɗa min ai bazan tsaya ina tambayar ka ba."

Tamke bakin sa yayi before yace, "a kan kishinta na banza ne, Allah yarinyar nan ta soma ƙure Ni, da abun da yakamata da wanda bai kamata ba duk sai ta hau kai tana nuna kishi, to ni wlh ta soma kai Ni bango bazan jure ba."

Dariya Mummy tayi da cewa, "wai kana nufin Nawwaran naka ne yau ta soma kai ka bango? Lallai kam yau naga abun da ya fi ƙarfi na."

"Uhm Mummy ki dena ɗaukar abun nan da wasa, wlh abun da take yi ya soma isata, yarinya sai bak'ar kishin jaraba sai kace ita kaɗai ce aka halarta min in aura?"

"Tofa! Kace dai ka samu wata ce kake so ka juya mata baya? To ai da gaskiyarta tunda tana kishi ne a kan abinda take so, to bari kaji Ni kaina bazan taɓa goya maka baya a kan abun da kake shirin yi ga Nawwara ba, tunda har ka ɓata mata rayuwa ta zama yanda ta zama a yanzu dole ne ka aure ta."

"Wai ban gane ba Mummy, na ɓata mata rayuwa kamar ya don Allah? Me kike nufi?"

"Abun da nake nufi kaima ka sani, yarinyar nan dai tun tana ƙarama take tare da kai, ta ƙi kowa sai kai, ga shi yanzu har ta gama karatunta kuna tare, sai yanzu kuma da aka zo gaɓa ana shirin aurenku shi ne zaka zo da wani magana?"

"To yanzu Mummy wanne magana na zo da shi ne?" Yayi maganar kamar zai yi kuka

Hannu ta sa ta shafa kanshi before tace, "to idan baka zo min dashi ba ka faɗa min mene ne musabbabin abun da ya haɗa ku yanzu kuke faɗa? Sannan gaba ɗaya ka sauya a ɗan kwanakin nan ko fara'a ba ka yi, duk me ke damun ka ne?"

Shiru yayi yana kallonta, kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru yace, "ki bar zancen nan Mummy."

"Shikenan tunda yau Ni kake ɓoyewa abun da ke ranka, idan yayi wari zamu ji. Ina maganar mu da nace zaka je Kano?"

"Ki bari gobe sai in je tunda yanzu yamma tayi."

"Ok Allah ya kaimu rai da lafiya, akwai saƙon Mai martaba da zan baka sai ka wuce mishi dashi."

"To Mummy." Ya furta yana miƙewa tare da sake cewa, "Mummy bari in je in Yi wanka zan fita, but ki ce Zainab ta kawo min laptop ɗina tun kafin in karyata."

"Kun fi kusa ai, idan ka karya ta kuma kai da Abban ku." Tayi maganar tana mayar da idanunta a kan t.v

Yayinda shi kuma ya wuce ba tare da yace komai ba, ya haura sama inda ɗakin shi yake yana fito ya shige ciki

Nawwara da ta fito cikin ɗakin su Zainab ƙannin Malik, sai ta hange shi ya shige shiyasa ta bi bayan shi ta tura ƙofan ta shige itama.
[07/07, 11:32 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍*

_________________________

*BABI NA SHIDA*
_______________Har ya zauna a saman sofa ya soma latsa wayansa sai ya ji motsi, da sauri ya juya suka haɗa ido da ita, sai ya ɗauke kai yana sake tamke fuska ya ci gaba da abun da yake yi

Ita kuma tana tsaye tana faman kallon bayan shi, sai kuma ta tako a hankali ta iso kujeran da yake ta samu waje ta zauna tare da kama hannunsa tana ƙoƙarin shigewa jikinsa

Da sauri ya ɗago yana kallon ta yace, "stop it, I don't want you to be near me."

Ɗago idanunta tayi ta zuba mishi waɗanda a yanzu har sun tara ruwan hawaye, cikin sanyin murya tace, "me nayi maka?"

"Tambayana kike yi?"

"Yeah. Ban san me nayi maka ba."

"Ok." Ya furta yana ɓanɓare hannunta tare da miƙewa zai wuce

Da sauri ta tashi ta ƙanƙame shi ta baya tana sakin kuka me ban tausayi

Take ya runtse idanuwansa sabida jin yanda ta manne mishi a jiki, bazai iya jurewa ba shiyasa yayi saurin soma ɓanɓaro ta a jikinsa yana cewa, "Nawwara ba na son wannan abun, Please sake Ni."

"No bazan sake ka ba, wai me nayi maka ne kake so ka kashe Ni? Me nayi maka?" Tafaɗa cikin kuka sosai kuma ta ƙi sakin sa

Tamke bakin sa yake yi yana wani karkaɗa kai, sai kuma ya ja jiki a hankali ya koma saman kujeran yana cewa, "is ok mana, mene ne na kukan kuma?"

"Kai ne ai."

"Me nayi miki?" Ya furta yana kamo ta sosai ya sake mannata a jikinsa tare da yunƙurin share mata hawayen

Sai ta kawar da kai tana kallonsa tace, "wace ce yarinyar nan da na ganku tare? Kana nufin ka dena so na ne ko kuma ka gaji dani ne? Ka faɗa min mene ne alaƙar ku idan ba haka ba zan mutu?"

Shiru yayi kawai yana kallonta, shi ya kan rasa wacce iriyar Mace ce Nawwara, idan da ace zata san waye shi a zahiri ba ya tunanin zata iya kai wa anjima bata mutu ba, sai dai kuma komai nasa yana yi ne da taka-tsan-tsan bai taɓa bari ta san halayyarsa na bin Mata ba, a komai nashi tana bibiyan shi ba yau ba ya san duk abin da take yi, kuma ya san muddin ta gane yana tarayya da wasu Matan akwai daru, shiyasa shima bai taɓa yin kuskuren da zata sani ba. But yau kuma ga shi ta kama shi da hoton wata yana kallo... Ya kasa magana sabida tunanin da ke addabar sa a lokacin, sai da ta taɓa shi sannan ya dawo hayyacin sa, sai ya ja numfashi yana kama fuskarta tare da cewa, "wai meyasa har yanzu kin kasa yarda dani ne a rayuwa? Sau nawa zan miki alƙawarukan da zai sa ki yarda dani? Bani da wata Mace da zan aura face ke, meyasa kike min irin haka ne?"

"Na san cewa ba ka da wata macen da zaka aura bayan Ni, amma laifi ne don na tuhume ka a kan kallon hoton wata Mace bayan Ni ina da nawa hoton?"

Murmushi yayi sabida maganar nata, sai yace, "Nawwara kin cika kishin jaraba, ke kaɗai ce fa a zuciyata, kin sani ke kaɗai na soma ƙauna tun ba ki mallaki hankalin kanki ba, ke ce kika fara ɗanɗana min zumar da tunda nake a duniya ban taɓa jin makamanciyar ta ba, to me kike kokwanto ne?"

Shiru tayi sai kuma ta ɗan ja numfashi tana janye fuskarta daga riƙon da yayi mata, still tana kallonsa tace, "har yanzu ka ƙi sanar da Ni mene ne dalilin da yasa kake kallon hoton wata bayan Ni? Shi ne amsar da nake son sani."

Ƙura mata idanu yayi, sai kuma yace, "saboda kawai naga hoton ta ne a social media shiyasa nake kallo, amma bayan haka babu komai, sannan ban santa ba; ban san ma inda zan ganta ba bare kiyi tunanin zata ƙwace miki Ni."

Tura baki tayi gaba tana zare jikinta a nashi tare da cewa, "amma mene ne zai sa kana kallonta bayan ba ka santa ba? Meye haɗinka da ita?"

"Nawwara." Ya kira sunanta yana tsare ta da kallo

Sai ta kalle shi suka haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta

Hannunta ya riƙe yana ɗan mirzawa, sai kuma ya janyo ta sosai a jikinsa yana cewa, "da alamu kina kokwanto da irin ƙaunar da nake miki shiyasa har yanzu kike min irin wannan tuhumar." Ganin zata yi magana sai ya sanya hannunsa duka biyun ya matso da kanta ya haɗe bakunansu waje ɗaya. Bai saurara mata ba a haka ya ci gaba da tsotson bakinta cikin wani irin salo da yake saurin cin galaba a kanta, ko kusa ba ya ƙaunar ta ci gaba da wannan maganar don ya san halinta tamkar mayya haka take, shiyasa lokaci ɗaya ya soma birkita mata lissafi, cikin ƙanƙanin lokaci sun fita a hayyacin su

Itama abun da take buƙata kenan, domin kusan sati biyu ba ta samun kulawa daga gare shi,
shiyasa tayi tsananin kewar shi, hakan yasa itama bata saurara mishi ba sai da ta nuna mishi tsananin zalaman da take fama dashi a wannan lokacin. Sun shafe tsawon lokaci suna tare cikin wannan yanayin, until they were all satisfied sannan suka shiga cikin toilet suka yi wanka suka fito

Duk wani hanya da Malik ya san zai bi domin ya mantar da ita maganar haka ya bi, ya ƙi bata ƙofan da zata sake dawowa da wancan tunanin, soyayya kawai suke sha domin daga ƙarshe ma rufe musu ƙofa yayi suka kwanta a saman gado manne da juna, still suna romance ɗin junansu tamkar zasu haɗiye juna, dama abun da ya san tana so kenan samun kulawan shi gaba ɗaya. Haka kuwa ya mantar da ita komai, har yana sanar da ita, "zuwa gobe zai je Kano sai ta shirya su je tare."

Ai kuwa ba ƙaramin farin ciki ya cika ta ba, sai murna take yi sabida ta san bata taɓa samun wannan damar ba, basu taɓa yin tafiya tare ba, ta san cewa ita kaɗai ce a zuciyar Malik daga ita babu wata Mace, ita shi ne haka ma shi nata ne, kuma baza ta taɓa yin saken da wata zata shigo rayuwar shi ta raba su ba, idan kuwa hakan ta faru tayi alƙawari sai ta kashe ko wace ce; baza ta barta a raye ba.
Chapter 10 · 0% Book details