Sashe 14
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai Auta kin cika ƙorafi wlh, yanzu fa kika ga na kira shi yace ga shi nan a hanya."
"To ai naga ba shi da alamar zuwa ne ya shanya mu sai kace bayin shi..."
Bata rufe baki ba sai ga sallaman shi sun shigo tare da Aliyu Abokin sa
A tare idanuwan su Arab da Zahra suka sauka a kan Aliyun da shima ya haɗa ido da su, sai kawai aka koma kallon-kallo da juna babu mai motsin kirki a cikin su, har shi Aliyun ya kasa jirgawa daga inda yake tsaye a bakin ƙofan hannunsa ɗaya a cikin Aljihun wandon sa.
[14/07, 8:42 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA TAKWAS*
_______________ Maganar da Nafi'u yayi mishi ne ya dawo da shi cikin tunanin sa, sai ya ɗauke kanshi a kansu yana isowa izuwa kan kujerun falon kamar yanda Nafi'u yayi mishi iso
A cikinsu babu wanda ya motsa duk da akwai wajen zama amma duk sun ciccika wurin
Arab da Zahra mamakin ganin shi kawai suke yi wanda yasa dukkan su babu me magana, yayinda suka ɗauke kai tuni
Musamman ma Zahra wacce gaba ɗaya zuciyarta ke faman bugawa sabida abun da take ji a game dashi, bata taɓa tunanin zata sake ganin kyakkyawar saurayin nan da ya ƙi fita mata a rai ba ya tsaya mata cak
Ita kuwa Arab tuni ta ɗaura ƙafa kan ɗaya tana wani shan ƙamshi sai kace bata san dashi ba; duk da kuwa itama tayi mamakin ganinsa tana tunanin meye haɗin shi da nan gidan?
Sai dai maganar Nafi'u duk ya shafe musu wani tantama har shi. Inda yake musu bayanin cewa, "Doctor waɗannan su ne ƙannin Matata Firdausi." Sai ya kalli Firdausin yana murmushi da cewa, "wai kin gane shi? Aboki na da nake ba ki labari yana zaune a Abuja?"
Murmushi tayi tace, "na gane shi mana tunda na san shi sau ɗaya." Sai ta gaishe shi cikin fara'a
A lokacin ne ya ɗago kansa shima da ɗan guntun murmushinsa ya amsa mata yana tambayar ta, "ya jiki?"
"Alhamdulillah jiki da sauƙi wlh."
"Masha Allah. Allahumma ya ƙara sauƙi." Ya furta yana ɗaukar wayansa da ke ƙaran shigowar text
Daga Firdausi sai Nafi'u suka amsa
Inda Firdausin take cewa Ummu, "please Ummu ɗauko mishi drinks a fridge mana."
"To." Tace tana miƙewa
Yayinda itama Arab da ke faman shan ƙamshi har yanzu, fuskarta babu walwala ko kaɗan ta miƙe tana yatsina fuska da cewa, "please get up and let's go, ba a nan zamu zauna mu ƙare ba muna da abun yi."
Duk kallonta suke yi sabida yanda take maganar da gadara tana wani ciccin magani, ba wanda bai san halinta ba
But sai Nafi'u da wasa da dariya yace, "haba Auta ki jira muyi sallama mana, ai yanzu na dawo."
"To wanne sallama bayan ga shi ka dawo? We will go, Aunty mun tafi." Sai ta suri jakarta tana cewa, "idan kun gama zaman ku taso mu wuce." Tayi hanyar waje zata fita, kamar an ce ta kalli inda Doctor Aliyu yake zaune, sai suka haɗa idanu, wani irin banzan kallo ta sakar mishi tana jan ƙaramin tsaki tayi waje da sauri
Shi kuwa tsananin mamaki da al'ajabi ne ya cika sa har ya kasa yin magana, sabida ba kaɗan ba yarinyar tayi matuƙar ɓata mishi rai da irin kallon da take mishi, a ransa sai ya ji wani irin tsanarta yana huda mishi can cikin jikinsa, a rayuwa ya tsani ya ga Mace mara tarbiyya sheɗaniya, ko da gani wannan yarinyar bata da kunya. Koda Ummu ta kawo mishi drinks ɗin ya kasa sha sabida ganin yanayin yaran babu ko kunya a tattare da su, da idanu a tsakar ka suna yi tamkar karuwai, ko ba'a faɗa mishi ba zubin su ya tabbatar mishi da hakan. Abun ya dame shi har ya kasa sakin jikinsa koda suka tafi, yana mamakin ya aka yi Nafi'u ya je ya auro ƴar gidan mara su tarbiyya? Duk da cewa ya ga bambanci mai yawa a tare da Firdausin da su, ko da gani ba tarbiyyar su ɗaya ba amma abun ya ba shi mamaki don ya san halin Nafi'u.. daga ƙarshe ce mishi yayi, "zai wuce sabida a kan hanya yake tunda yana son komawa Abuja ne yau."
A haka suka fito har haraban gidan Nafi'u ya rako shi, sosai yayi murna saboda yanda ya zo mishi ziyara, yana ta godiya a haka suka rabu cikin farin ciki cike da kewar juna
Motansa ya hau ya wuce gidan Auntyn shi Hussaina wacce take aure a nan ɗin; tare da yaranta da mijinta. Su biyu ne kaɗai mahaifiyar su ta haifa kafin ta rasu, sai Dad ɗinsu ya auri wata Matar itama ta haifa yara uku duka Mata. Doctor Aliyu da Aunty Hussaina duk likitanci suka karanta. Yanzu haka Doctor Aliyu shi yake kula da mahaifinsu da bai da lafiya yana ciwon Sigar da Cancer da suka taso shi gaba, yau jikin da daɗi gobe babu haka suke fama.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Sai da aka kira sallan magriba sannan su Arab suka isa gida. Sallah suka yi sannan suka shantake a farfajiyar gidan suna ta zubawa Inna labari har Zahra da ba ƙoshin lafiya ta cika ba, sai ƙarfin hali da take nunawa don kar a gane halin da take ciki
Baba ma da ya dawo yayi murna sosai, musamman da ya ji jikin Firdausin da sauƙi ba yanda yake zato ba.
Bayan kwana biyu da dawowar su ne Alhaji Bashir ya matsa wa Arab sai ta biyo shi Abuja tayi mishi ko kwana biyu ne. Ai kuwa yanda ya matsa ɗin ne shiyasa tace mishi, "tana nan zuwa."
Ibrahim ta kira ta sanar mishi yanda suka yi. Shi ya sake kwaɗaita mata a kan, "ta je kawai ta wanki gara."
Hakan kuwa ta kasance, tace ma Alhaji Bashir, "zata zo gobe."
Tare da Ibrahim suka tafi super market ta yo siyayyan kayan da zata buƙata. Sai da suka gama suka tafi yawo tare, sai kusan magriba suka iso gida
Tana zuwa ta hangi motan Tariq a ƙofar gidan su, dama ya kira ta duk bata ɗauka ba a yau ɗin, da alamu yana da takura ne shiyasa take ba wa banza ajiyansa, ita ta tsani a takura mata, sam ba ta ɗaukar hakan. Sallama suka yi da Ibrahim tace, "ya tafi kawai sai sun yi waya." Sannan ta wuce zuwa gidan ba tare da ta kula Tariq ɗin ba
Yana ganin zata wuce sai ya fito da sauri yana kiranta, "haba Gimbiyyar mata kamar ba ki ganni ba?"
Wani kallo ta watsa mishi lokacin da ta juyo ta kalle shi, sai ta taɓe baki da cewa, "ban ganka ba, ashe kai ne?"
Murmushi yayi yace, "ko dai sarautar ne ya tashi? Don Allah ki zo mu shiga mota muyi magana, Please?" Ya ƙare maganar yana ɗan haɗe hannayen shi alamun roƙo
Kamar baza ta motsa ba, sai kuma ta gama shan ƙamshin ta cike da yatsina ta taho ta buɗe motan ta shiga bata ce mishi uffan ba
Shima sai ya shige ya rufo ƙofan yana kallonta da cewa, "wai Gimbiyyata me nayi miki ne kika share Ni kwana biyu? Kin hana Ni zuwa gidan ku tun sanda kika dawo bayan kin san da ƙishin ruwan ganin ki nake wuni a ko yaushe, ba na so kina min horo da rashin ganin ki zuciyata baza ta iya jura ba."
"Ko?" Ta furta tana latsa wayanta ba tare da ta kalle shi ba, kuma babu wata alamar damuwa a tare da ita
Hakan ne yasa ya ji babu daɗi, cikin kwantar da murya yace, "Arab wai don Allah me kike so in Yi miki da zai tabbatar miki da na damu da ke?"
Ɗago kai tayi ta zuba mishi, sai kuma tayi murmushin gefen baki da cewa, "Yallaɓoi me kake so in Yi maka nima? Meye damuwar ka?"
"Kin san ko meye damuwata Princess, kwata-kwata kin kasa bani dama na shiga rayuwarki sosai, ina so don Allah ki bani wannan damar ko kaɗan ne, tunda kin ce ba kya son ina zuwa gidan ku me zai hana mu samu inda kike buƙata mu tattauna?"
"Why not." Ta furta tana ɗage kafaɗa still tana ci gaba da murmushin nan nata da ba kowa yake gane ma'anar shi ba
Jin hakan sai shima ya yalwata fara'a a kan fuskar shi da cewa, "kin amince kenan?"
"Yes, I agree. But tomorrow I will travel. We will talk when I get back."
Fuskarsa ne ta nuna damuwa, cike da rashin jin daɗi yace, "ina za ki je kenan?"
Murmushi tayi tana ɗan kashe mishi ido da faɗin, "ba sai ka ji ba Yallaɓoi."
"Kina kashe min jiki idan kina min wannan kallon, meyasa baza ki fahimce Ni ba? Ni mai ƙaunar ki ne wlh ina matuƙar ƙaunar ki." Ya ƙare maganar kuma yana kai hannunsa a hankali ya kama nata, yayinda ya zuba mata lumsassun idanuwansa da suke ƙoƙarin sauya kamannin su
Ita kuma murmushi kawai take mishi tana ƙare mishi kallon ƙurilla, lokaci ɗaya ta gama saka shi a wani irin yanayin da ya soma ficewa a hayyacinsa, ba kaɗan ba ta san lagwon namiji musamman idan ta gama laƙantan shi.. sai da ta janyo shi jikinta yana ƙoƙarin haɗe bakin su sai ta hana shi damar hakan tana saka yatsarta ɗaya a setting bakin sa, still fuskarta na ɗauke da murmushin nan nata me zautar da duk wanda tayi masa, a hankali ta girgiza mishi kanta tana ɗan buga yatsan nata a laɓɓansa tare da cewa, "a'a Yallaɓoi mene ne kuma haka? Ka bari sai na ba ka damar yin wani abu dani." Sai ta saki dariya me sauti tana janye jikinta tare da zuba mishi rikitattun idanuwanta tana kashe mishi ido ɗaya
Ya kasa jurewa shiyasa ya sake damƙo ta yana cewa, "haba Princess I need you, please kar kiyi min wannan horon, ko nawa ne zan iya ba ki domin in kasance tare da ke a yau."