← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 52

Sashe 30

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ta saki wanda har fararen haƙoranta da suke ƴan ƙananu masu ban sha'awa sai da suka fito, sai ta soma murza hannun nata da ke kan ƙirjinsa tana mishi yawo dashi a jikinsa, cikin salo take mishi wani irin kallo wanda ke ƙara tsulma shi a gogin tafkin ƙaunarta da sha'awarta, duk wucewar second ɗaya yana jin wani irin feelings ɗin da bazai iya misaltuwa ba, sauke hannunta tayi saman fuskarsa tana zagaye mishi ƙaramin sajen sa da faɗin, "mene ne aibun shiga na after all you know I didn't start today? Ina da tarin samarin da kai ka san cewa ba kai kaɗai bane, Ni allura ce a cikin ruwa har yanzu mai rabo bai ɗauka ba, kuma shigana ba shi ne zai sa ka rasa Ni ba..." Sai ta ja wani irin numfashi tana hura mishi iska a kan fuska, inda ta ɗaga kanta sosai tana kallon cikin idanuwansa cikin wannan shu'umin murmushin nata ta sake cewa, "abu ɗaya na sani, kai ne ka kawo Ni nan, don haka muna tare da kai a kodayaushe; I will never pay attention to anyone, ka kwantar da hankalinka sweetie ba na son ina ganin damuwa a kan fuskarka..."

Bata ida maganar ba ya haɗe bakin su waje ɗaya yana mata wani irin tsotso tamkar zai cinye mata baki; sabida kawai bakin nata ne ya fi ɗaukar mishi hankali a time ɗin

Duk yanda ta so ta ƙwace bakinta ta kasa haka ta bar shi yana ta sarrafa ta son ransa, ganin yana son wuce gona da iri ne sai tayi ƙarfin halin zare bakin nata tana kwantar da kanta a ƙirjinsa saboda baza ta iya tsayuwa da ƙafafuwanta ba a halin da ya saka ta

Shi kansa ya kasa haƙura shafa ta kawai yake yi yana sake ƙwaƙume ta kamar wacce za'a ƙwace mishi ita, a hankali ya raɗa mata cikin wani irin hali da yake ciki yace, "Baby mu fasa zuwa don Allah, ina tsananin buƙatar ki bazan iya fita a haka ba."

Zare jikinta tayi daga jikinsa tana shirin wucewa

Sai ya damƙo hannunta yana kiran sunanta tamkar zai yi kuka

Kallonsa tayi tana ɗan nazartan shi, sai kuma tace, "I don't run I am always with you, but I want to go to the party because I want to be there."

"So how do I do it? After all I want to be with you? I can't go out like that."

Guntun murmushi tayi tace, "idan Abokin ka kuma ya ji shiru fa? Kar ka manta ka zo nan ne don bikin sa sannan ka kasa halartan biki, and nima ka saka min rai Ina son zuwa wajen; because it will make me very happy."

"Shikenan zan haƙura." Ya furta yana lashe bakin sa, yayinda ya janyo ta kusa da shi yana ƙara cewa, "but you promise me we will be together today without sleep."

Fari tayi mishi da manyan idanuwanta tace, "kaima ka san hali na, Let's go time is running out."

Bai barta haka nan ba sai da ya sake laluba ta duk ya ƙarisa lanɗe mata lipstick ɗin bakinta before suka fice ba tare da ta sake saka wani ba

Sai a cikin mota ne ta sake shafa wani ta gyara kwalliyan nata. Yana ta mata ƙorafi but bata saurare shi ba har suka kai. Time ɗin ma an ɗauki mintoci da farawa.
[28/07, 9:06 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝‍♀️*

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

_________________________

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*
_______________Yana tsayar da motan kiran Umar ya shigo, nan yake tambayar sa, "har yanzu basu zo ba an fara?"

Sai yace mishi, "ga su nan a waje, yanzu zasu shigo."

A tare suka fito suka shiga Hole ɗin da ake taron. Lokacin party yayi zafi ana ta cashewa gunun sha'awa, su kansu wurin ya burge su don an shirya wajen ya haɗu

But yawancin mutanen wurin sai da idanuwansu suka koma kan Arab domin ba ƙaramin burge su tayi ba, musamman yanda take wani karairaya cikin yanga da jan aji sai idanu ya koma kanta, ga rigan da ta sanya dashi da babu duk ɗaya

Tariq kuma yana manne da ita don ganin idanun mutane yayi yawa a kansu, ya san bazai wuce Arab ce ta tsole musu idanu ba. Ai kuwa suna zama Abokan Ango suka soma mishi tsiya wai, "aina ya samo wannan tsaleliyar?"

Dariya yayi yace, "da abata na zo ai, dama nace sai a nan zan gabatar muku da ita, ita ce wacce zan aura."

Farin ciki suka taya shi kowannen su ya kasa ɗauke ido a kan Arab, zuciyarsu cike da sha'awarta da tsananin birge su da tayi, sai dai babu daman faɗin abun da ke ransu tunda ga gwaninta a tare da ita, sai dai sun yabe ta suna ta mishi murna

Shi kuwa washe baki yake yi yana ƙara tarairayan abar sa. Komai tare suke yi cikin wayewa da nuna gogewan su

Musamman ma Arab wacce take sake shan ƙamshi tana karairaya. Har wurin Amarya ta je suka gaisa sai kallonta ake yi don majority idanun mutanen wurin yana kanta tunda sun samu t.v, shigan jikinta ya sa da yawan maza susucewa, babu Macen da suke gani idan ba ita ba, duk ta rikita su, sai ma lokacin da ta shiga rawa tana takawa tunda tana son rawa sosai. Zo kuga yanda ake liƙa mata kuɗi ana shewa

Sai da Tariq ya je ya janyo ta don kishi ya hana sa sukuni, musamman da ya ga ita kaɗai ake kallo, kowa idanuwansa na kanta, shiyasa ma yace, "gwara su tafi gaskiya." Haka suka koma masaukin su ba'a gama taron ba ma

Arab kuwa dariya kawai take mishi, don abun nasa ma dariya yake bata, idan tayi ninyar kula wani a wajen bai isa ya hana ta ba, sai dai duk a cikinsu babu wanda yayi mata ne, don ita ba ta harka da ƙananan mutane sai dai manya, ta fi son inda zata samu maiƙo sosai ba ɗan gutsiri ka tsoma ba, ita babbar Mace ce ba kowa yake iya shiga rijiyar ta ba sai mai Rabo, ta fi ƙarfin ƙananan Yara. Amma ganin yana son wuce gona da iri sai wani ciccin magani yake yi don haushi da kishi ke ɗawainiya dashi, sai ta taka mishi burgi da cewa, "ka ga Malam, Ni fa ba matarka bace da zakana min irin haka, Ni budurwan ka ce baka da ƴancin hana Ni kula wani idan na so, but abun naka yana son wuce gona da iri don na sanar maka ba na son takura. Please don't do this to me or we will get into big trouble."

Yanda ya ga ta tayar da jijiyar wuya ranta na son ɓaci sai ya koma bata haƙuri tamkar wani wawa, domin ko kusa ba ya ƙaunar ace sun ɓata har wani saɓani ya shiga tsakanin su, soyayyarta ta rigada tayi mishi zurfi a zuciya har ba ya son ganin ɓacin ranta. Dole ya lallaɓa ta daga nan kuma zance ya juya

Kusan ranan basu runtsa ba sai gab da asuba. Ƙarshe sai goman safe suka tashi suka yi wanka sannan suka rama sallan da basu yi ba, bayan sun karya ne suka wuce gidan Firdausi don Arab tace mishi, "tana buƙatar zuwa kafin su koma."

Ai kuwa tayi murnan ganinta don bata yi zaton zuwan nata ba, farin cikin ta ba ya misaltuwa, nan da nan ta tarbe su da lemuka da snacks sannan ta zauna suka gaisa sai kallon Tariq take Yi

Arab da ta kula sai tace, "oh! Ban gabatar miki dashi ba, saurayina ne."

"Allah Sarki!" Inji Firdausin tana murmusawa, duk da a ranta ta san cewa bazai wuce samarin ta irin waɗanda ta saba tarawa bane, don ta san halin ta, shiyasa tace, "yanzu tun daga gida ku ka zo nan gaishe Ni tare? Ko dai dashi ne za'a yi?" Ta ƙare maganar tana dariya

Shima Tariq murmushi kaɗai yayi yana sunne kai ƙasa

Ita kuwa Arab dayake ba kasafai take ɓoye gaskiya ba, abun da ke ranta shi ne a zahiri, shiyasa tace mata, "biki suka zo nan ɗin, kuma ba ta son ta tafi bata zo sun gaisa ba tunda Allah ya kawo ta garin."

"Biki? Bikin wane?" Firdausin tayi tambayar da mamaki

Tana kurɓan juice ta bata amsa da, "Abokin Tariq ne, shi ne na rako sa."

Shiru Firdausi tayi bata iya cewa komai ba illa kallon Arab ɗin da take yi

Ita kuwa tuni ta canza zancen nata ko a jikinta; ta mayar da hankalinta a kan Tariq tana ce mishi, "wai baza ka ci komai bane? Nan fa ba baƙon waje bane gidan Babbar Yayar mu ce, don haka ka saki jikinka ko Mijinta ne bazai hana ka abun da kayi ninya ba bare ita."

Tariq murmushi kaɗai yayi yana jinjina kansa; tare da mamakin halin Arab, kowa dai bata bari ba, a ɗan zamantakewar su ya soma fahimtar halin ta, ko meye a ranta faɗi take yi, ba ta da shakku ko tsoro, iskancin ta a fili ne ba ta tsoron uban kowa

Itama Firdausin bata ce komai ba jin abun da Arab ɗin tace, don ta san zata iya faɗan abun da ya fi haka tunda ba kunya ta cika ba, sai dai ranta babu daɗi sabida ganin Arab ɗin tare da saurayin ta wai sun zo biki, har yanzu baza su canza halin su ba, abun ya kai har Inna tana barin su zuwa wani waje da saurayi, "Allah Sarki Baba! Na san kana nan kana kwana da baƙin cikin Inna, Allah ya kawo maka mafita..."

"Wai Aunty lafiyan ki ina magana kin yi shiru?" Arab ta katse mata zancen nata ganin hankalin ta ya ɗauke tana magana bata ji ta ba

Da sauri ta dawo hayyacinta tana kallonta tace, "me kika ce ne?"

"To ina kuwa za ki ji kin zauna kina saka tunani a ranki? Ga ciki a gaba amma baza ki bar zuciyarki ta huta ba, shiyasa ciwo ke kwantar da ke, Allah dai ya raba lafiya mu kam zamu tafi."
Chapter 30 · 0% Book details