← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 52

Sashe 28

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni Alhajin ya sake ruɗewa saboda kallon ido ciki ido da suke yiwa juna, narkakkun idanuwanta ba ƙaramin sake tafiya da shi suka yi ba, tare da sake nutso a tafkin ƙaunarta da sha'awar ta, jiki na rawa ya zaro wayansa yana cewa, "I look like you're in a hurry, but if you don't mind, give me your phone number; We'll talk later."

Bata ɓata lokaci ba ta karanta mishi Numban

Sai yace, "ban yi tunanin kina da sauƙin kai haka ba, kin haɗu sosai, Allah yasa zan samu karɓuwa duk sanda na kira ki?"

"Don't worry Alhaji, whatever you want you will find in my place." Tayi maganar tana cije leɓe cikin salo irin na gogaggun ƴan hannu, waɗanda lokaci ɗaya da salon su suke janye Mutum, har wani gantsaro ƙirji take yi tana karkaɗa mishi fararen manyan idanuwanta masu shegen kyau da ɗaukar hankali

Shi kuwa tuni ya washe baki yana cewa, "yauwa na gode, ki sanar min da sunan ki bazan so in bar nan ba sai naji sunan ki duk da nima ina sauri ne, but Ni suna na Alhaji Sammani, what about You?"

Before ta ba shi amsa ne Tariq ya fito daga ɗakin don ganin shiru bata shigo ba bayan tace mishi, "ga ta nan." Ya kasa haƙura shiyasa ya leƙo don ya duba ta, karaf idanuwansa suka faɗa a kansu, da sauri ya fito daga ɗakin daga shi sai gajeren wando da Singlet yana kiran sunanta

Hakan yasa ta juya ta ganshi don bata ji buɗewar ƙofan nashi ba tunda ta juyawa ƙofan baya

"Me kike yi a nan kuma? Waye wannan?" Yayi maganar da damuwa a kan fuskarsa yana sake kai duban sa kan Alhajin da ke tsaye wanda a ƙalla zai kai shekaru 50 a duniya, duk da hutu da jin dadi ya ɓoye shekarun nasa sai zallan ƙuruciya da ya bayyana a kan fuskarsa, baza ka taɓa cewa babba bane kuma ba shi da jikin girma sosai ɗan dai-dai ne

Murmushi ne ya suɓuce a kan fuskarta, tana riƙe masa hannu ta saƙala nata cikin nashi, cikin salo da yaudara irin nata nan da nan ta kalallame murya tana narke mishi da cewa, "haba Sweetie mene ne kuma na kishi? Kaga fuskarka kuwa?" Sai ta shafa fuskar tana ɗan zizira mishi tsinin ƙumban ta cikin jan hankali tace, "wannan ɗan uwan Mamana ne ai, na zo shiga ciki ne muka haɗu muna gaisawa." Sai ta kalli Mutumin da cewa, "Kawu Sammani wannan shi ne wanda muka zo nan ɗin tare ai, kuma shi ne wanda zan aura."

Da sauri Alhaji Sammani ya washe baki yana cewa, "Ah ah ashe shi ne surukin namu? To Masha Allah! Allah yasa za'a yi damu."

Tuni Tariq kunya ya kama shi har yana sunne kai ƙasa, kana ya gaishe shi cikin girmamawa yana cewa, "Kawu ina wuni."

"Lafiya lau Yaro, ban san tare kuke ba shine nake tambyar ta me ya kawo ta nan? Amma babu damuwa tunda ta gaya min akwai abun da ku ka zo yi." Sai ya kalli Arab ɗin ta kashe mishi ido; sai yayi murmushi yana cewa, "to bari in je nima sauri nake yi, ki gaishe da Maman naki kinji ko?"

"To Kawu." Ta furta tana murmusawa

A haka ya wuce ya bar su a wurin, sai suka shige cikin ɗakin su

Suna shiga Tariq ya janyo ta kan jikinsa yana cewa, "wai da gaske Baby za ki aure ni? Ni ne wanda za ki aura ɗin?"

Yaudararren murmushinta ta sakar mishi tana shafa fuskarsa idanunta cikin nasa, cike da kissa tace, "me zai hana Yallaɓoi? Idan muna tare ai zan iya auren ka, ka haɗa komai fa da Mace take burin mallakar ɗa namiji, baka da makusa ko kaɗan, don haka bani da dalilin ƙin amincewa da kai."

Wannan kalaman nata ba ƙaramin faranta ranshi suka yi ba, nan ya matse ta a jikinsa yana cewa, "ban taɓa tunanin ina burge ki har haka ba Baby, naji dadin kalaman ki matuƙa, i love You Baby, har a cikin zuciyata ina jinki can ciki, i will never be happy every day idan na rasa ki, i love you so much and so much!"

Dariya tayi; sai ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya soma tsotsa tamkar zai cinye ta, lokaci ɗaya suka soma cuɗa junansu cikin ƙwarewa da tsantsan sha'awar da ke addabar su. Sai da suka gama gamsar da junan su a falon sannan suka shiga wanka, a can ma sai da suka yi taɓe-taɓen su tamkar baza su rabu ba, ko kaɗan ba sa gajiya musamman ma Arab da abun ya zame mata jiki yanzu, mintuna kaɗan ba ta iya jurewa idan babu namiji a tare da ita

Shi kuma tsantsan iya soyayyarta da ƙwarewanta na iya tafiyar da namiji hakan ne yasa Tariq ba ya iya gajiya da ita, bai taɓa cin mace sau ɗaya sau biyu ya sake na uku ba, hasali ma shi ba kasafai yake wannan harkan ba sai idan ta motsa mishi, amma kuma yanda yake jin Arab a zuciyarsa bazai taɓa iya haƙura da ita ba, kullum da zai samu damar su kasance tare yana so, ba ya gajiya da ita ko kaɗan, tana da daɗin da duk yawan mata zai yi wuya a samu kalanta da yawa, bare tana gyara jikinta sosai, duk wani abun da zai kawo mata ni'ima tana yin shi da hannunta, bata yarda da abubuwan siya barkatai ba, da kanta take haɗa kayanta ta sha iya shanta, shiyasa idan har kana tare da ita zai yi wuya baka manta kanka ka mutu a gogin ƙaunarta ba, duk wanda yayi tarayya da ita yana jinta daban ne matuƙa, bare ƴan bariki sun fi shiga rai fiye da matan gida, su kaɗai suka iya tafiyar da kowanne irin namiji babu ƙyama bare kunya, duk da ya san wace ce ita amma burin sa ace ta ba shi damar da zai mallake ta ya killace ta a cikin gidan sa, tana da kyan da ba kowanne namiji bane zai iya haƙura da ita duk da ya san wace ce ita, sai dai yayi fatan ta zama tashi shi kaɗai a nan gaba.

       Abinci suka ci sannan suka kwanta manne da juna babu kaya a jikinsu. Washe gari kuma suka tashi suka shirya tsab, inda Tariq ya sanya ƙananun kaya da suka yi mishi kyau matuƙa, don dama shi mutum ne mai son gayu, ga shi kyakykyawa farin sa mai kyau mai ɗaukar hankali

Ita kuma sai ta sanya bak'ar material da ya ɗauki beauty white skin ɗinta, doguwar riga ce tunda yawanci shi ta fi ƙauna, musamman idan an yi mata aljihu zaka ga ta saka wayanta duk karikitanta a ciki, babu ruwanta da jaka don bata cika using dashi ba. Ɗankwalin kayan ta ɗaura tayi ture kaga tsiya fuskarta da light make-up, sai ta jefa chewing gum a baki kamar yanda ya zame mata ɗabi'a, ga shi ta iya taunan chewing gum ɗin don nata salon na daban ne, da wannan taunan nata kaɗai take iya janyo hankalin namiji, duk wanda ya kalle ta sai ya sake. Takalma ta saka mai tsini sannan suka wuce zuwa mota

A haka suka isa anguwan da ango yake. Yana yin parking sai ya kira Angon yace mishi, "ga su a waje."

Babu jimawa ya fito kuwa, ganin su tare sai yace, "Ah ah Mutumina Ina ka samo wannan mai zafin haka? Daga zuwa garin mu har kayi kamu?"

"No da abata na zo ai, tana masauki ne shi ne dalilin da yasa nace maka bazan kwana a nan ba ai."

"Haba dai? But meyasa baka sanar min ba? Masha Allah amma kun dace matuƙa, kayi dacen kyakykyawa, sannu ko." Ya ƙare maganar yana kafawa Arab ɗin idanu

Wacce ta ɗauke kai tunda tayi mishi duba ɗaya, tana taunan chewing gum cikin yanga tana latsa wayanta. Jin yayi magana sai ta ɗago itama ta kafa mishi idanuwanta da babu alamar kunya a cikin su, a buɗe suke kyar na zubin ƴan duniya; masu shiga jikin duk wanda ta zuba mishi su sabida kyawunsu. Murmushi tayi masa tace, "sannun mu, ya kake?"

"Lafiya lau, kin zo lafiya?" Ya furta cikin washe baki

"Alhamdulillah." Kaɗai ta furta ta sake ɗauke nata idanun tana shan ƙamshi irin nata na big girl wayayyu

Tariq yace, "yauwa abun da yasa na kira ka ban shiga ciki ba; don ba na son kowa ya ganin min ita ne, ka san yanzu zamani ya sauya."

Dariya yayi Angon yana cewa, "shege baaba, kuma haka ne fa, gwara kayi tattalin abun ka don wannan Allah ne ya kashe ya baka." Ya ƙare zancen yana sake kallon Arab don ba ƙaramin kyau tayi masa ba, ba hassada ba ya san abokin nasu ya kere ma sa'ar su idan ya mallaki wannan, ko shi ace za'a musanya mishi da ita wlh da gudu zai amshe ta, ta tafi da duk wani imanin sa, ko jirgawa da idanuwansa ba ya yi a kanta tsaban yanda ta haɗu ta ba shi sha'awa, ga ta yarinya sharaf ko a ido aka kalle ta za'a gane hakan

Tariq ya katse mishi zancen zucin shi yana cewa, "ina son ka haɗa ta da Amaryan ka ne sai ta zauna a can wajen ta, hakan zai fi tunda bazai yiwu muna yawo tare ba mu ba zama zamu yi ba sabida harkan biki."

"Eh wannan ba matsala bane ai, bari in shiga gida sai in kira Ƙanwata ta raka ta zuwa gidan, zan kira Lailan in sanar mata."

"Yauwa nawan." Tariq yace hakan yana ba shi hannu suka kashe

Shi kuma sai yayi dariya yana cewa, "bari in zo ina dawowa yanzu." Sai ya juya ya shiga gidan su. Babu jimawa ya dawo da wata ƙaramar yarinya da baza ta wuce 10years ba. "yauwa to ga ta nan zata kaita."

Tariq yace, "Gidan da nisa ne ko mu je kawai a mota?"

"Eh babu wani nisa, amma ku je a motan zan jira ka a nan, idan ka dawo sai mu shiga ciki."

"Ok."
Chapter 28 · 0% Book details