Sashe 20
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana ƙoƙarin amsa ne sai ya faɗi ƙasa, shiyasa ta duƙa don ɗauka. Dai-dai kan wasu fararen ƙafafu da suke cikin Black flat shoes suka sauka, inda shi kuma ya take ba tare da sanin sa ba sabida already ya ɗaga ƙafan sa ɗaya zai ajiye; ATM ɗin ya shige ya taka, ƙafafuwan ta bi da kallo sabida tsananin kyawun da suka yi mata, har ta so shagaltuwa a kai tare da tunanin ya mamallakin ƙafafun zai kasance? gaskiya Allah yayi halitta. Ɗagowa tayi da zummar tayi mishi magana ya ɗaga mata domin da alamu bai san ya taka ba ma. Sai karaf idanuwanta suka haɗe dana Doctor Aliyu, kallon kallo suka yiwa juna sabida dukkan su sun gane fuskokin juna, da sauri ta janye idanuwanta saboda irin kallon da yake sakar mata, sam ba ta ƙaunar haɗa ido dashi musamman yanda idanuwan nasa suka kasance wani iri ga su kalan Brown, sai ta ɗan yatsina fuska tana ci je baki da cewa, "excuse me! ka ɗaga ƙafarka zan ɗauki ATM."
Bai ce komai ba ya matsar da ƙafar yana bin ƙasan da kallo
Ita kuma tuni ta sake duƙawa ta ɗauka ta ba wa mutumin. Sai ta kawar da kai bata sake kallon inda Aliyu yake ba
Shi kuwa yana tsaye shima riƙe da kwandon da yayi siyayya a ciki. Fuskarsa babu walwala shima bai sake bi ta kanta ba, sai dai a ranshi mamakin ganinta a nan ɗin yake yi, but mamakin sa ya ƙare a sanda Alhaji Bashir ya zo wajen ta yana kiran ta da Baby yana tambayar ta, "ta gama ne su tafi?" Yana jin amsar da take ba shi, sai ya taɓe baki a ransa yace, "No wonder, ai ba abun mamaki bane don naga Karuwa a nan." Sai ya ja dogon tsaki yana ɗaura kwandon kayan shi ganin sun matsa daga inda suke
Arab tana jinsa, har sai da ta juyo ta dube shi, hakan yasa suka haɗa idanu ya balla mata harara fuskarsa babu ko ɗigon fara'a, kasa ramawa tayi don abun ma mamaki ya bata, "lallai wannan mutumin." Ta furta a laɓɓanta ba tare da ta san zai fito fili ba
Alhaji Bashir da ya ji kamar tayi magana, sai yace, "Baby are you talking to me?"
"No ba da kai nake yi ba." Ta furta tana sakar mishi murmushi
Cewa yayi, "su tafi."
Sannan ta bi bayan shi suka fice ma'aikata na kwashe musu kayan
Aliyu kuwa da harara ya raka su yana sake haɗe rai, ji yake yi ya sake tsanar yarinyar a ransa, ga ta dai ƴar ƙarama amma ta ɓata rayuwar ta, har mamaki yake yi wasu irin iyaye ne dasu da har suka bar ƙaramar yarinyar nan tana yawon karuwanci? Anya kuwa Nafi'u ya san ƴar gidan wa ya aura? Da alamu har ƴan uwan nata duk halin su ɗaya don basu yi kama da mutanen ƙwarai ba, tsaki kawai ya kuma ja cike da takaici a ransa, shi dai har ga Allah bazai iya auren ƴar gidan karuwai ba, Nafi'u ba shi da wata hujjar da zai iya auren Firdausi koda ita ba karuwa bace, but ai gidan su ɓata-gari ne, kuma kowa zai riƙa mata irin wannan kallon, yana ga kawai kyawu ne ya ribace shi har ya aure ta... Kayan sa ya ɗauka ya fice bayan ya biya kuɗin, yana fita kuwa ya hange su a cikin mota sai dariya suke yi, a gaban shi motan ta wuce Arab bata ma ganshi ba, the more yana kallon fuskarta the more yana sake jin tsanarta na sake shigan sa. Motan sa shima ya shiga ya ja ya tafi, yana kallon nasu motan a gaban shi a haka har suka yi nisa, sai ya ga sun shiga wani Hotel yayinda shi kuma yayi gaba abun sa, zuciyarsa abubuwa da dama take raya mishi a kan Arab, yayinda yake sake turr da ita a ranshi; tare da jin ƙyamar rayuwarta da halayyarta.
Ita kuwa Arab sam ba ya gabanta, tunda suka fito ta manta da shafin sa, ta mayar da hankalinta a kan Alhajin ta sai nishaɗi suke yi. Suna tare a ranan har dare kamar chewing gum sabida ban kwana da suke yi zata tafi, shiyasa yake fanshe duk wasu kwanaki wai da zata yi ba tare da shi ba
Ita kuwa sai dariya take mishi saboda yanda ya susuce a kanta ya ƙi haƙura, tace, "Alhaji kar ka damu in dai Ni ce sai ka gaji da kasancewa da Ni."
"Ai ba haka bane Baby, Ni sam ba na so ki tafi ne, but idan kin yarda duk inda zan je zan riƙa tafiya da ke, zan sakar miki kuɗi har sai kin ce kin gaji, fatana dai ki kasance da Ni a duk inda zan je, zamu riƙa tafiya tare."
"Oh! Alhaji kar ka manta fa Ni ina gaban iyayena ne, bazai yiwu mu riƙa kasancewa koda yaushe ba, nima bazan so hakan ba domin ba na son ka gundura da Ni, but zan riƙa ƙoƙarin zuwa a duk sanda ka buƙace ni amma ba ko ina ba, ka san ba zaman kaina nake yi ba, bambanci na da Karuwan titi kenan."
"I know there is no problem that's why I said that baby, but shikenan tunda kin ce haka, amma idan zan riƙa yin nisa zamu tafi da ke don na fi son kasancewa da ke a kan kowacce Mace, wlh Baby bazan taɓa gajiya da ke ba don ke ta musamman ce, ko ba'a taɓa faɗa miki haka bane?" Ya ƙare maganar yana jan mata jelan kitson kanta da ke jiƙe sharkaf sakamakon wankan da tayi
Ita kuma sai ta sake kwantar da kan nata a faffaɗan ƙirjinsa tana cewa, "na san da haka Alhaji, kaima na musamman ne a gare Ni don ban taɓa samun abin da na samu a wurinka ba a wajen wani."
"Baby ai nace miki ba ki da matsalar kuɗi, zan kashe miki ko nawa ne kuma ko me kike so zan ba ki."
Murmushi tayi na farin ciki, nan ta sanja salon hiran nasu. A haka suka kasance a ranan cikin nunawa juna soyayya
Zuwa washe gari kuma ya sa aka tafi mata da motan, an zuba kayan tsaraban da yayi mata a ciki, kasancewar bata iya motan ba har yanzu shiyasa yasa aka kai mata. Tana cikin motan Driver a gaba, a haka suka isa Zaria Arab na farin ciki sabida farar tafiyan da ta yo, ta samu kuɗi wajen Alhajin gaskiya ba kaɗan ba, ko yanzu da zasu taho 200k ya tura mata.
[20/07, 8:39 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA GOMA SHA BIYU*
_______________ *ZARIA CITY*
Lokacin da Arab ta koma da motanta; duk sun ruɗe sabida ganin motan
Inna kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don daɗi, bakin ta ma ya ƙi rufuwa faɗi take yi, "Wayyo daɗi Wayyo! Daɗin haihuwa kenan, yanzu idan ban haihu ba taya zan samu wannan arzikin? Allah na gode maka da ka bani Yara waɗanda zasu share min hawaye, farin ciki sai gudana yake yi a gidana, waɗansu kuwa hassada da ƙyashi yayi musu yawa sai dai su mutu wlh, ƴaƴana sun yi gaba nan gani nan bari mahassada sai dai su haɗiye zuciya su mutu, Allah ya yiwa ƴaƴana goshin arziƙi, wannan kaya haka? Nan gaba sai zuwa Makka a duk sati-sati, Allah na gode maka." Sai ta ɗaga hannayenta cikin farin ciki tana nuna godiyar ta ga Allah
Yayinda Ummu da Zahra sai ɗaga kayayyakin da Arab ɗin ta yo musu tsaraba suke yi, suna murna su ma sabida ganin kayan masu shegen tsada, haƙiƙa ƴar uwansu ta kankaro musu girma. Sai tambayarta suke yi, "wannan wanne irin Mutum ne haka? Wanne irin kuɗi yake dashi? Sannan me suka yi a can da ina da ina suka je?"
Ai nan Arab ta zauna tana ta ba su labari, abubuwan da suka yi da duk yawon da suka yi da Alhaji, sai dai bata sanar musu da haƙiƙanin zaman da suka yi a Hotel ba, kawai tace musu, "bikin Abokinsa ake yi."
Duk da ƴan uwanta sun san cewa dole tana ba shi kanta ne don ita kaɗai ce a cikin su suka san tana wannan ɗabi'ar, su kawai iyakan irin soyayyar nan na shan minti ne ba sa wuce haka, daga nan sai su samu kuɗi abun su, but yanzu ne Zahra ta shiga sahun ta, don itama tana mutuwar son saurayin nata ne, ɗan gidan sarauta ne kuma shi take da burin aure, yayi mata alƙawarin aure but sai ta ba shi kanta, shiyasa ta ba shi kanta, sai dai tunda suka aikata wannan al'amarin ya bar ƙasar bai sake dawowa ba, kusan wata biyu kenan a na uku, suna waya har yanzu suna soyayyar su sai dai ba ya ƙasar ne yana can yana karatu, yayi mata alƙawarin duk sanda ya dawo zasu yi aure; don shima yana sonta sosai
Ita kanta Inna itama duk a ganinta tsaban farin jinin yaranta da yanda ta koyar da su cin kuɗin samari shi ne yake tasiri, da kuma yanda take nema musu magani na farin jini saurayi ya sakar musu kuɗi, bata san cewa yanzu duniyar bani gishiri in ba ka manja bane, shiyasa duk abun da zasu yi baza ta hana su ba tunda ta san cewa basu taɓa aikata wani kuskure ba, suna yin komai ne don su wanki garori.