Sashe 49
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jameema ce ta shigo, domin dawowarta kenan da wasu ƴan mata su biyu, tana shiga part ɗinta ta bar su a can sai ta fito ta nufi dainning aria, tana tune da Arab da ta barta a ɗaki a kulle ba'a bata abinci ba, kuma tayi ma masu aikin gargaɗi, "kar su sake shiga part ɗin, idan tana buƙatar su shiga ita da kanta zata neme su," shiyasa suka bi umarninta basu shiga ba, sai yanzu da ta dawo ta sa ɗaya ta haɗa abinci a kan faranti, bayan ta gama sai ta amsa ta wuce dashi sashin Arab. Tana buɗe ƙofan ta hange ta a kwance tamkar mai barci, itama a tunaninta barcin take yi shiyasa ta ajiye farantin a ƙasa, kana ta zauna a gefen gadon ta soma tashin ta
Arab tana ji amma tayi biris da ita, sai can daga baya sannan ta buɗe idanunta da suka gama canzawa sabida yunwa da damuwar da ta ɗaura wa kanta
"I'm sorry Baby, kiyi haƙuri na manta na bar ki da yunwa kin sha wahala. I'm so sorry." Tayi maganar cike da tausayinta tana shafa mata fuska har zuwa goshinta inda kwantaccen gashin kanta ya kwanta a wurin
Mayar da idanuwanta tayi ta rufe bata ce mata komai ba, kuma alamu ya nuna baza tayi maganar bane, amma kuma yadda fuskarta ta nuna tana cike da tsantsan tsana da kuma haushin Jameeman
Ita kuwa bata damu ba sai murmushi da tayi, tare da cire hannunta daga goshinta tana cewa, "ga abinci nan ki ci zan dawo yanzu." Bata jira cewarta ba ta miƙe ta fice bayan ta datse ƙofan
Kamar baza ta tashi ba tun bayan fitan nata, sai dai kuma ta miƙe ta sauka ƙasa ta soma cin abincin cikin sauri sabida azaban yunwar da take ji, zuciyarta na cinkushe da baƙin ciki da tunanin mafitan abun da yakamata tayi, bazai yiwu ta dauwama a haka ba dole tayi wani abu... Tana nan zaune bata motsa ba sabida tunanin da ya ɗauke mata hankali, sai ji tayi an buɗe ƙofan, ta bi wurin da kallo suka haɗa ido da Senator Ƙasim, da sauri ta miƙe har jikinta na rawa wajen nufan shi, tana zuwa ta rungume shi tare da fashewa da kuka
Hannunsa ya ɗaura a saman kanta alamun rarrashi tare da ɗago kanta yana kallonta yana mata murmushi
A lokacin Jameema ta shigo cikin ɗakin itama tana zuba nata murmushin tare da cewa, "Alhaji kaga yanda take ko? Ta ƙi kwantar da hankalinta bare ta bada haɗin kai, maybe idan kayi mata bayani zata fahimta."
Wannan kalaman na Jameema su ne suka sa Arab ta kasa furta komai, tayi shiru tana kallonta tare da tunanin ma'anar maganar nata
While shi kuma hannun Arab ɗin ya kama zuwa bakin gado ya zauna, itama ya zaunar da ita a gefe, kana ya kalli Jameema yace, "itama ta zauna."
Zama tayi a stool ɗin gadon tana kallon Arab
Haka itama ɗin kallon nata take yi tana tunanin irin makircin da zata lanƙaya mata, don da alamu ta soma gane me Jameeman take nufi, ko ma me zata faɗa sai ta tona mata asiri a yau ɗin nan, zata san ta taɓo ta
"A'isha." Senator ya kira sunanta yana kallonta
Sai itama ta mayar da hankalinta a kanshi batare da ta amsa ba tana shirin jin ta bakin shi
Yace, "a ganin ki mene ne dalilin da yasa na aure ki ko? Na san wannan tambayar yana nan a ranki duk da ba ki fito fili kin faɗa min ba, amma na san dole za ki yi tunanin nan; duba da yanda na ajiye ki a gidan bani da wani lokacin ki." Murmushi yayi before ya ci gaba da cewa, "auren ki da nayi yana da manufofi da dama a wurin mu; don bazan ce manufa kaɗai ba, amma dole za ki ji wasu a yanzu wasu kuma sun girmi tunanin ki. A cikin rayuwar siyasata dole zan buƙace ki domin kai ga ci, Mace irin ki muke buƙata sai aka yi Sa'a ke ce wacce tayi dai-dai da kwatancen da Malamina yayi min, na aure ki ne ba don komai ba sai don cikan burina na siyasa, tun lokacin da aka aura mana aure na sake ki domin ba ki zo gidan nan da igiyoyin aure na ba; sabida ba a buƙatar kasancewar mu a ma'aurata, don haka ko mai za ki gani ki kwantar da hankalinki idan har za ki yi mana biyayya, ko nawa ne zan iya biyanki ko mene ne kike so, buƙata kawai kiyi mana biyayya, na san Matata ta fara biyan buƙatarta a wurinki kuma kin gane manufarta, haka nima zan riƙa biyan buƙatata ta baya( Homosexual/Luwaɗi) a duk sanda nake so, don haka sai ki shirya don ko da amincewar ki ko babu zamu yi abun da muke so da ke; tunda na siye ki ne."
Tunda yake maganar; bakinsa kaɗai take kallo har ya dire zancen nasa ta kasa furta wani word; sabida gani take yi kamar a mafarki ne tsaban yanda maganar tayi mata wani irin duka, ta hautsina mata duk wata natsuwa nata, ta sanya mata firgici gami da kaɗuwa; wadda ko a fuskarta kaɗai zaka tabbatar da halin da take ciki.
[16/08, 10:05 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA ASHIRIN DA TARA*
_______________Har suka ƙarike maganganun su suka tashi zasu tafi bata furta komai ba. Sai da ta tabbatar zasu bar ɗakin sai tayi wuff ta miƙe kamar wata mahaukaciya, hawaye ke zuba a idanunta jikinta na rawa ta zube a gaban su, cikin muryan kuka tace, "don Allah kuyi hakuri ku bar Ni in tafi bazan iya wannan rayuwar ba, ku nemi wacce zata iya Ni bazan iya ba."
Dariya suka yi su dukka
While Senator yace, "bayan duk sonki da kuɗi ace wani abin ya gagare ki? Na sanki fa sosai kuma na san yanda kike matuƙar ƙaunar kuɗi, ɗan wannan abun shi ne baza ki iya ba? Kar ki manta zamanki billonia a ɗan ƙanƙanin lokacin nan mafarkin ki zai cika, mai kike tsoro ne? Kuma batun mu sauya wani bazai taɓa yiwuwa ba, kin san sirrinmu baza ki taɓa fita a gidan nan ba, zan yi magana da masu tsaron gidan babu ke babu fita, don haka kiyi shawara rayuwarki ko kuma kuɗi. Mu je Hajiya." Yayi maganar yana kallon Jameema. Kana suka fice a ɗakin suka barta a nan
Sai ta kwatsa ihu tana faɗin, "na shiga uku Ni A'isha! na kawo kaina inda zan kashe kaina da kaina." Sai kuma ta tashi cikin rawan jiki sabida ganin ƙofan a buɗe, bata yi wata-wata ba ta fice da gudunta, tana taɓa ƙofan falon nan ma a buɗe ta ji, sai ta fice da gudu jikinta na rawa sosai, har zata sauka kan benen sai ta hango su a ƙasan falo suna magana, sai kuma ta ga shi ya nufi ƙofan waje riƙe da waya, ita kuma Jameema ta bi hanyar part ɗinta, da sauri ta gangara ta sauka itama ta bi bayansa, tana ganin ya nufi haraban gidan yana waya, ita kuma sai ta lallaɓa ta jikin flowers tana ta tafiya a duƙe a hankali yanda baza a ganta ba, duk da akwai duhun dare amma gidan tarwai yake da fitilu masu haske, still jikinta sai rawa yake yi duk a tsorace take, burinta kawai ta samu kuɓuta daga gidan nan. Tana jin sanda ya gama wayan ya soma kiran securityn gidan har mai gadi, dole ta dakata sabida ganin sun nufo wurin, kuma idan tace zata yi ƙoƙarin fita dole zasu ganta sabida ta kai ƙarshen flowers ɗin. Daga inda take tana jin maganganun da yake faɗa musu
Yana basu umarnin, "kar su bari ta bar gidan, idan suka bari ta bar gidan daga yau kashin su ya bushe." Sai da ya ja ma mai gadin kunne domin shi ne a bakin ƙofa
Mai gadi yace, "an gama ranka ya daɗe! Yanzu ma zan soma aiki na, babu mai shiga da fita sai da iznina domin kwaɗo zan sa a ƙofan."
Jin hakan shiyasa ta lumshe idanunta tana sake buɗewa tana kallon tazaran inda take da Gate ɗin gidan, tabbas idan ta bari ya sallame su bata bar gidan nan ba shikenan kuma bata da damar fita, gwara tayi shahada idan Allah yasa zata iya tsallakewa. Shiyasa ta fito a guje ta nufi ƙofan fita, zuciyarta na wani irin tsalle da bugawar da take tunanin ƙiris ya rage ta fito daga ƙirjinta, tamkar zata ci kai sabida irin gudun da ta kwasa a wurin
Tuni sun hange ta. Nan da nan Senator ya basu umarnin, "su kama ta kar su bari ta fita." Hankalinsa a matuƙar tashe don ba ya fatan ta bar gidan basu kama ta ba
Tuni sun bi umarninsa daga su har karnukan gidan suka bi bayanta
Sai da ta kai bakin ƙofan Gate ɗin tayi wani irin zamewa fuskarta ta bugi jikin Gate ɗin. Bata tsaya tunanin wani abu ba bare buguwan da tayi, burinta kawai ace ta fice daga gidan, tuni ta saka hannu ta buɗe ƙofan tayi wuff ta fice. Gudu take yi kamar zata tashi sama, gudun ceton rai. Ko waiwayan bayanta ba tayi duk da tana jin gurnanin karnuka a kusa da ita, amma inaa ta ƙi tsayawa da iya ƙarfin ta take gudun
Ga layin masu kuɗi ne babu kowa, sai haushin karnukan da suke biye da ita da kuma na cikin gidan mutane, garin yayi duhu sosai duk da akwai hasken fitila na sauran gidaje da ya haska wurin