← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 52

Sashe 42

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Baba kuma babu sauƙi dole sai dai ya haƙura tunda yana jin jiki, idan yayi kamar zai warke sai kuma jikin ya tashi, dole aka hana sa zuwa tunda baza su bar shi ya tafin musu a haka ba

A ranan da Inna ta tafi washe gari jikin Baban ya sake tsanani sosai, shiyasa Arab ta ƙi tafiya sai ma canza mishi asibiti aka yi don gani suke yi kamar ba ya samun kulawa a asibitin gwamnati, sai aka mayar da shi na kuɗi, haka yake shan jiki tunda ciwon already ya ci jikinsa kafin ya kwantar da shi, duk damuwa ne ta haifar mishi da ciwukan nan har da hawan jini, baƙin ciki da damuwan da yake saka wa ransa a kan abubuwan da Inna Harira take mishi, ga damuwar halin da yaransa suke ciki ya kasa sanya su a kan hanya, ciwo ya ci ya ci jikinsa har ya taɓa mishi zuciya

Kwana uku da kai shi asibitin ma Allah ya amshi abun sa

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Tabbas mutuwa wata aba ce mai girma wanda komin taurin zuciyarka idan har mutuwar ta shafe ka dole ne sai ta taɓa ka, duk yanda su Arab suka kai da rashin biyayya ga mahaifin su; da kuma rashin ɗaukar sa da muhimmanci a rayuwar su, sai da suka yi kuka, sun sha kuka sosai domin a zuciyarsu babu wacce ba ta ƙaunarsa, bare tafiyar da yayi ya tafi ne baza su sake ganin sa ba, mutuwar ta shige su sosai kuma tasa jikinsu yayi sanyi matuƙa, ko magana ba sa iya yi, duk wanda ya gansu sai ya tausaya musu tamkar ba su ba

Barin ma Firdausi wacce ta fi su shiga wani hali, a daren da ya rasu washe gari ta zo gidan, ta sha kuka ba kaɗan ba duk ta fita a hayyacin ta, haka suka haɗe kai suna ta kuka kamar zasu bi shi

Baba ya ga jama'a gaskiya ba kaɗan ba, shi kansa Senator Ƙasim mutane da yawa ya zo dasu jana'izar

Haka Matar shi Jameema itama a ranan ta zo, tana tare da su Arab tana faman rarrashin su, gaskiya ta tausaya musu domin mutuwar mahaifi babban illa ne ga rayuwar kowanne Mutum, tamkar ka rasa wani ɓangare na jikinka ne, rashi ne babba.

          Inna tana can Saudiyya mutuwar ya riske ta, duk yanda ta kai ga musguna wa Baba itama mutuwar ya matuƙar girgiza ta har sai da ta zubar da hawaye, shiyasa gaba ɗaya aikin hajjin tana yin shi ne cikin rashin walwala, nan take hankalin ta sai ya tashi burinta kawai ta koma gida, hankalinta duk yayi gida duk da ta san ko ta koma baza ta same shi ba, amma yanda mutuwar ta shige ta ne duk ta ruɗe a can; ba ta iya yin wani abun kirki

Kwana uku da rasuwar shi sannan Jameema ta koma gida, while Senator shi tun a ranan ya tafi bayan ya danƙa ma Arab kuɗi mai yawa wanda zasu kula da jama'a ƴan gaisuwa

Yawanci duk a ranan mutane suka watse, dama ba wasu mutane bane illa su Firdausi, itama a ranan uku ta wuce, sai Jameema da ta tafi itama a ranan, sannan sai Gwaggo Samira, duk a ranan suka wuce

Arab ce kaɗai tare da su Ummu a gidan, sai ranan bakwai sannan suka tattara su duka suka taho Kano; kasancewar Arab tace, "su biyo ta kawai idan Inna ta kusa dawowa sai su dawo." Haka kuwa suka bi ta babu musu

Kuma a can ma babu wanda yace don me? Domin Jameema ma murnan ganin su tayi, sai haba-haba take yi dasu tamkar zata goya su, duk da akwai ƴan aiki amma komai ita take musu, musamman zata ce, "su shirya su fita yawo." Wani lokacin ma har gidan su take kai su, wato gidan sarauta kasancewar ita ƴar can ne, mahaifinta ƙani ne wajen Sarki. Duk sun saba da jama'ar gidan su babu wanda bai sansu ba. A cikin ƴan uwa ma har su Zahra sun samu samari don har biyo su suke yi gidan su Arab su sha soyayyar su

But sai dai su ɗin babu wacce take son su don Allah sai dai don a rage zafi, domin already kowacce cikin su tana da wanda take fatan aura. Zahra ta tsayar da Haidar a wanda take burin aure da zaran Inna ta dawo za'a yi magana. Haka itama Ummu sabida akwai wani saurayi da yake son ta

Shima kyakykyawa ne duk da ba wani kuɗi sosai da sosai yake da shi ba, irin ƴan ƙaryan nan ne duk abun da take so yana mata, ga shi ya iya wanka na jan hankali da iya tsara kalaman soyayya, lokaci ɗaya ya samu zuciyarta sabida gaba ɗaya ta susuce a kansa, duk abun da ya faɗa mata ita yarda take yi dashi don yace mata, "ba a nan yake aiki ba, yana ƙasar England ne yana aiki, suna yin aure can zasu wuce."

Ita abun da take hangowa kenan, shiyasa duk ta amince dashi, yanzu sun yanke shawaran duk tare zasu yi aure bayan Inna ta dawo za'a tsayar da rana

A can Kano su Zahran suka yi babban Sallan su. Bayan kwana biyu da yin sallah suka koma gida sabida gyare-gyare da zasu yi na dawowar Inna, tunda ba wani daɗewa za'a yi ba zata dawo.
[08/08, 9:34 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️

_________________________

*BABI NA ASHIRIN DA BIYAR*
_______________Jameema ce tsaye a dainning area tana ba wa masu aikin su umarnin yanda zasu shirya kan dainning ɗin, mutane biyu ne masu shirya wurin while biyu kuma suna kwaso coololin da suka shirya komai a ciki suna kawo wa

Arab ta fito daga ɗaki wanda barci ne ya sure ta har rana tayi bata farka ba, fitowan ta sai ta iso wajen tana cewa, "Aunty Barka da aiki."

Jameema wacce sai a yanzu ta ganta ma sai tayi murmushi tace, "yauwa Ƙanwata barkan ki, kin tashi ashe?"

Murmushin itama tayi tana cewa, "eh, I don't know when I fell asleep but now I wake up, until time is up."

"Ƙwarai kuwa, na shigo na ganki kina ta sharan barci nace bari in bar ki kar in tashe ki, dama na shigo sanar miki ne akwai baƙi da zan yi, ɗan Aunty na ya zo shi ne zasu shigo gaishe Ni da Matarsa."

"Ayya ashe baƙi zamu yi? To bari in je in shirya before su zo."

Jameema tace, "sai kin dawo, nima yanzu zan shiga in watsa ruwan."

Daga haka Arab wuce wa tayi ta koma part ɗinta. Wayanta ta tarar tana ƙara shiyasa ta ɗauka ganin Besty ɗinta ne, sun jima suna waya before ta kira Zahra suka gaisa tana musu ya hanya kasancewar tun tafiyar su jiya basu yi waya ba, sun jima suna wayan har da Ummu before ta shiga wankan.

               A lokacin ne motan Malik ta shigo gidan, bayan yayi parking suka fito shi da Nawwara, sun yi kyau matuƙa cikin shaddar da suka yi anko kalan maroon, ko da gani ka san kuɗi da hutu ya zauna musu don har wani ƙiba suka yi

Tun tafiyar su yawon Honeymoon suka ƙi dawowa a can suka yi azumi da ƙaramar sallah

Sai da Abban Malik ya nuna musu ɓacin ransa yace, "maza su dawo kafin ya taho inda suke ya saɓa musu." Sannan ne suka dawo

Yanzu kwanan su biyu da zuwa Kano, shi ne suka zo gaishe da Jameema tunda a matsayin ƙanwar Mummyn su Malik take

Itama sai da tayi musu mita tace, "wlh idan basu zo ba zasu ga fushin ta tunda sun manta da ita."

Suna shiga falon Jameema ta tarbe su don tana zaune a Falo tana jiran shigowar su. Rungume juna suka yi da Nawwara tana cewa, "sai yau Allah yayi zan ga idanun ki Nawwara, kika biye wa Abdul kwata-kwata ba kwa ƙaunar zuwa wuri na, ko me nayi muku oho? Tun auren ku fa baku zo nan ba."

Dariya Nawwara tayi da cewa, "kiyi haƙuri Aunty, wlh muna ta sa ranan zuwa Allah bai yi bane, bayan mun dawo kuma ayyuka sun yi yawa, Abba ya tsare mu yace babu inda zamu matsa sai mun gama aikin Office, to sai da wannan sallan ya zo ne muka ɗan samu damar fita muna zagaya dangi."

"Ai yayi min dai-dai tunda alamu ya nuna babu mai hankali a cikin ku, daga zuwa hutu kun je kun shantake a can, ke kuma kwata-kwata kika biye masa kika ƙi dawowa." Tayi maganar tana jawo kunnen Malik da ya zauna a gefen ta

Shagwaɓe fuska yayi kamar zai yi mata kuka yace, "kai Aunty don Allah kar ki katse min kunne, please ki sakar min."

"Bazan saki ba har sai ka faɗa min dalilin da yasa ba ka son zuwa gidana, wato kuna ma garin ba don mun yi waya da Mummyn ka ba bazan sani ba? So ku kayi ku tafi ban san da zuwan ku ba."

"Wlh Aunty a'a, ya za'a yi mu zo bamu zo nan mun ganki ba? Allah zamu zo."

Nawwara na dariya tace, "ai Aunty kar ki yarda da daɗin bakin shi, tun farko sai da nace mishi mu zo mu gaishe ki First; but yace a'a, kuma Ni na san dole zai ce ya manta mu tafi bamu zo ba, shiyasa tun farko nace mu fara zuwa."

"Hohho! Ka ga gaskiya ta bayyana, ai kuwa zan yi punishment ɗin ka, a nan zaku ƙarisa kwanakin ku har ku koma Abuja, zan kira Mai martaban in faɗa masa."

Murmushi Malik ɗin yayi tare da faɗin, "da girman kujeran ki Aunty, tuba nake, amma..." Sai ya kalli Nawwara ya harare ta zai yi magana
Chapter 42 · 0% Book details