← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 52

Sashe 15

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harshenta ta sanya ta lashi kumatun sa tana dariya, sai kuma ta kafa mishi fingers ɗinta da suke zaro-zaro kamar na cin kare, sun sha jan lalle sun yi wani kyau na ɗaukar hankali a kan zara-zaran fararen yatsunta, hakan ne yasa ta hana shi ƙoƙarin kissing ɗinta da yake faman yi kamar wani maye, har ya soma yawo da hannunsa ɗaya a jikinta, sai tayi saurin cewa, "idan fa kana taɓa Ni farashin ka yana ƙara yawa ne. Wait until we trade."

"So how much do you need? What do you want me to give you? I can give you wlh." Yafaɗa cikin rawan murya wanda tuni ya fice a cikin hayyacin sa sabida jin albarkatun jikinta manne da shi

Janye jikinta tayi tana yatsina fuska, sai kuma ta ɗauki wayanta tace, "For my account number, send me the money before we talk."

"Ok." Ya furta da sauri yana ciro nashi wayan tare da kwashe Numban nata da ta karanto mishi, bai yi wata-wata ba ya tura mata 50k a account ɗin

Tana gani ta ƙyalƙyale da dariya, sai kuma ta dube shi cikin tsananin nuna soyayya tace, "But please be patient Malam, now I don't have your time, don haka idan kana so muyi wata harƙalla ka bari sai na dawo daga tafiya, sai abun da kace zan yi." Ta ƙare maganar tana cije leɓen ƙasan bakinta cikin wani irin salo me jan hankali

Shi kuma jajayen idanuwansa ya zuba mata, tare da matsowa sosai wajenta, hannu yasa zuwa saman cinyanta yana shirin kware mata skirt din da ke jikinta, cikin marairaice fuska yace, "Please help me I can't stand it for a while, Princess I love you I need you in my life."

Ɓata fuska tayi tana ɗaura dogon farin hannunta a saman nashi, tare da cewa, "kuɗin ka bazai yi min maganin komai ba Malam, idan ba ka amince da abun da nace ba zan dawo maka da kuɗin ka, ba na son takura." Ta ƙare maganar tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka

Hakan yasa yace, "shikenan is ok, na amince Princess, but ko ɗan kaɗan ne ki bani dama in ɗan rage wani abu."

Murmusawa tayi tace, "You don't agree with what I'm telling you?"

"Na yarda but please, just 10mint."

"Ok." Ta furta tana ɗan janye hannunta daga saman nashi hannun

Hakan ne ya ba shi damar ci gaba da abun da yayi ninya cikin sauri da nuna zalamansa, they immediately clung to each other, at one point they began to romance tamkar zasu haɗiye kansu, kowannen su cike da ƙwarewa yake aikawa ɗan uwansa message

Sai da ta ga abun yana son wuce gona da iri sannan ta janye jikinta, duk da dai sosai taji daɗin kasancewar su tare don ba kaɗan ba alamu ya nuna mata Tariq ɗan Love ne ya iya sarrafa Mace, ta san cewa duk sanda suka kasance tare zata ji daɗi ba kaɗan ba, sai dai kuma bata yi ninyar ba shi kanta ba a yanzu don ba shi ne a gabanta ba, shiyasa ta lallaɓa shi sannan ta samu ta fito ta wuce gida

Shima ya tafi zuciyarsa na ƙara tsananin bege da ƙaunarta, bai san ya zai yi da mahaukaciyar ƙaunarta da sha'awar ta da yake fama da su ba, duk da dai ya san ita wace ce amma a zahiri da zai samu damar mallakar ta a matsayin Mata wlh sai ya aure ta, amma zai jure duk wani wulaƙanci domin ya mallake ta, shi dai ya san ya more idan ya samu zuƙeƙiyar yarinyar nan, bata da makusa ko ta'ina tayi mishi ɗari bisa ɗari, ya san idan ta zama mallakin sa dole zai hana ta mu'amala da duk wani namiji, ita ba irin matan nan da za'a iya yasar da su bane, sun san kan rayuwa kuma sun san yanda zasu bi domin su mallake zuciyar ɗa namiji, don haka shi babu ruwan shi don ita karuwa ce, shi dai ya same ta domun farin cikin zuciyarsa, ita kaɗai ce zata iya dashi.

             Arab kuwa koda ta shiga gida ta tarar da ƴan uwanta a gindin bishiya ne zaune. Inna kuma tana ɗaki a lokacin, but tunda ta ji muryan Arab sai ta fito tana cewa, "Oh Auta wai ina kika je ne yanzu aka zo neman ki? Kinga baƙo a waje?"

"Eh na ganshi Inna, mun je kasuwa ne Ni da Besty mun yi siyayyar tafiyana."

"Tafiya kuma?" Cewar Innar tana isowa wajen itama ta zauna, yayinda ta bi kayan da Ummu take fitowa da su suna gani

Zahra tace, "wanne tafiya kuma kika samu za ki yi?"

Dariya tayi tana ɗaukar wayanta tare da latsawa tace, "Abuja zan je."

"Abuja Autana? Ke kuwa me ya haɗa ki da Abuja da za ki je? Me za ki yo a can?"

"Uhm ai Inna wani Alhaji na samu wlh me kuɗin gaske, ina faɗa miki idan har na samu shiga a wajen shi to kakar mu ta yanke saƙa, wlh ina tunanin ma sai dai in Yi wuff dashi don ina ji a jikina kin kusa zuwa Makka Inna."

"Don Allah da gaske kike yi?" Innar tafaɗa cike da washe baki

"Wlh kuwa Inna, shiyasa nake son in je saboda ya gayyace Ni, but ba wani daɗewa zan yi ba yakamata dai in je inga masaukin sa ne."

"Kai wannan ganganci ne wlh, taya ya za ki bi mutum har wani uwa duniya don kawai yana son ki? Har yaushe farashin naki ya sauka haka haba Arab? To makarantar naki fa ko kin manta kuna da Exams ne?"

Arab kallon Ummu da ke maganar tayi tana waro mata idanu da cewa, "lallai Aunty Ummu ba ki san waye Alhaji Bashir ba shiyasa kike wannan zancen, wlh ko ke ne kika samu damar nan sai kin je, to meye a ciki don na je can mun fahimci juna? Ba ki san irin kuɗin da ya tura min bane lokacin muna gidan Aunty Firdausi, wlh bazan zauna ba don na san arziƙi ke kirana."

Baba da ya fito daga ɗakinsa domin duk yana jin abubuwan da suke tattaunawa a kai, sai ya tsaya daga bakin ƙofan yana cewa, "akul ɗinki A'isha da wannan banzar shirmen, wato abun naku ya kai har ki bi namiji wani garin tsaban gantali ko? To babu inda za ki je, baza ku mayar da Ni mutumin banza ba duk kun hana Ni saƙat a gari, ko ina zancen ku ake yi na gagari baku tarbiyya, wannan abun da me yayi kama? To zan ɗauki mummunan mataki a kan ku wlh idan har baku gyara ba, kowaccen ku ta samu Miji tayi aure don bazan iya wannan shirmen naku ba, na gaji wlh."

Inna kamar jira take yi ya ajiye numfashi sai ta hayayyaƙo mishi tana cewa, "wlh bazai saɓu ba, ai zancen ka zancen banza ne tunda ba kai kaɗai kake da yaran ba, baka isa kayi musu aure a wannan marran sabida kana min baƙin ciki ba, na gode Allah ya bani ƴaƴa mata masu share min hawaye amma kai baƙin ciki yayi maka katutu kullum so kake yi kaga bayana, to wlh na rantse da Allah ba ka isa ba Iro, tun wuri ma ka canza tunani idan zugin ƴan gari zaka bi can ta matse maka, mu kuwa ba yau muka saba da su ba kuma maganganun su bazai mana komai ba, yara dai nawa ne sai abun da suka yi ninya zasu yi babu takura a rayuwar su, su ba Bayi bane balle ace za'a hana su ƴancin kansu, duk abun da suke so shi zasu yi tunda dai basu tarewa uban kowa hantsin gaba ba."

"Yanzu Ni kike faɗawa haka Harira? Ni Mijin ki?" Yayi maganar yana nuna kansa

"Yo yau ka soma ji dama? Ai idan har baka fita a harkan yarana ka dena takura musu a kan mutanen gari ba; wlh daga kai har su sai dai aniyar ku ta ƙare muku, yarana nan gari nan bari kurwan su kurr, kuma insha Allahu da su zan yi kuɗi, sai zaman anguwan nan ya gagare mu don mun fi ƙarfin zama a kwata."

Kanshi kawai ya gyaɗa yana juyawa ya shige cikin ɗakin sa zuciyarsa kamar zata yi bindiga ta fashe, sai dai bazai iya amayar da abubuwan da ke ransa ba, Harira ta rigada ta fi ƙarfin sa bai san ya zai yi ba, bai san ta wanne hanya zai bi domin ya ceto rayuwar ƴaƴan shi ba, haƙiƙa yana kaicho da wannan rayuwar, yana tur da Allah wadai da samun Harira a matsayin Matar sa, ga shi yanzu ba shi da wani ikon da zai iya tsawatar musu a matsayin waɗanda suke ƙarƙashin ikon shi, bai da wannan fawan. Har hawaye yake sharewa sabida yanda ya ji sun ci gaba da shewa da maganganu wanda ko alamu bai nuna sun ɗauki zancen shi da wani muhimmanci ba, inda yana jin Inna tana sake zuga Arab ɗin sosai

"Duk yanda za'a yi ta damƙo mutumin ta ɗaura shi a tafin hannunta, akwai ma maganin da zata bata zuwa gobe sai ta sake yin farin jini fiye da ko yaushe, kuma duk abun da ta buƙata ya bata sai ya bata a nan take, bari dai ta je ta ga yanda zai susuce a kanta."

Ƙarshe dai rediyo ya sa a kunnen sa ya dena sauraron baƙin cikin da suke ƙunsa mishi.

             Zuwa washe gari kuwa Arab tayi sammako ta gama shiryawanta tsab. Ibrahim ya zo da motan abokin sa zai kaita tasha ta samu abun hawa, tare da Ummu suka je tayi musu rakiya. Zahra kuma na gida suna aiki da Inna

Bayan sun kaita tashan har ta hau Mota sannan suka juyo.
[15/07, 9:25 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________

*BABI NA TARA*
_______________  *ABUJA STATE*
            Tun shigowar Nawwara cikin falon Mummy ta washe baki tana cewa, "iyee ƴan matan Yayanta, wannan cancaɗi haka! Kwalliya yayi kyau."

Dariya tayi tana isowa wajen, yayinda ta samu wuri kusa da Ikhlas ta zauna tana cewa, "Mummy good morning?"
Chapter 15 · 0% Book details