← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A razanen ta cigaba da nuna ni muryarta na rawa ta furta “Sharrin da za ki min kenan Aysha, wallahi k’arya take Sam ba ni ba ce a jikin hoton nan kuma ba ni da alak’a da duk wani abu da ya shafi hoton…” Bori na hau yi Anty Khadija na rirrik’eni na hau nuna su ina fa’din wallahi su ne, na gaji na gaji don me za’a dinga jingina min laifin da ba nawa ba ne,Hakn ya isa! Ya isa!! Ya isheni!!! Runguma sosai Anty Khadija ta kai min ta saka hannunta ta toshe min baki. Ki yi shiru Aysha Allah yana bayan mai gaskiya kuma tabbas shi zai saka miki. K’ananan maganganu ne suka cigaba da tashi a d’akin kowa yana fa’dar duk kalmar da yaga dama a kaina. Umma dai na tsaye tana bin kowa da ido. Zannira ta turo baki. “Ah to yarinya kada ki sake kama suna na, abin kunya ne dai kin janyowa familyn mu, kuma kina nema ki lik’a mana, nan kika dinga kwanaine kina hura hanci wai ke za ki auri mai ku’di ke da ake gani kamilar mace ake murnar ta samu Miji d’aya tamkar da dubu sai ga shi kin ba’dawa iyayenki k’asa a ido an tashi ba wan ba k’anin abinda Bature ke kira 2-0…” Kowa na ‘d’akin cike da mamaki ake kallon su Zannira jin irin kalaman da suke fita daga bakin su. Umma dai tana tsaye idanunta sun ka’da sun yi wani irin jaa. Anty Khadija ce ta kalli Zannira da Zaituna a zafafe ta ce “Ah to lallai ta bakin AYSHA akwai lauje cikin na’di a cikin wannan habaicin da kuke zubar wa, ashe dai tabbas hassada da bak’in ciki kuke mata, idan kuwa ya tabbata hakan ne ba abinda ba zaku iya aikatawa ba wajen son ruguza maganar auren, don haka dole an bincike ku ku fa’di gaskiya don ba k’ira ba abinda zai kawo gawayi….” A zafafe Umma Sa’a ta ci burki a gaban Anty Khadija ta nuna ta da yatsa.. “Kada ki fara Khadija, kada ki sake ki jawo mana waruwar kai a cikin dangi, mu kan mu a ha’de yake abinda bahaushe ke kira tsintsiya mad’aurinki d’aya don haka ki cire hasashenki akan su Zinatu me ye ribarsu idan suka yi silar waruwar auren AYSHA?” Bu’de baki Anty Khadija ta yi zata yi magana Umma da ke tsaye ta furta “Khadija ya isa! Kada ki sake magana, idan ma abinda kika fa’da d’in gaskiya ne Allah zai bayyana cikin girma da d’aukakarsa…” Shiru Anty Khadija tayi tana mayar da numfashi hawaye na zuba daga idonta, sai dai bata sake maganar ba duk da irin maganganun da suka cigaba da tashi na mita da habaici. Ta yi shiru kawai her face looking so worried. Jan ajiyar zuciya kawai take tana buga baya na. Tsit da d’akin ya yi ne ya sata mik’ewa tana kallo na, ta furta “Ki yi hak’uri AYSHA Allah yana bayan mai gaskiya, zan yi shiru da wannan maganar amma anan kawai ba don komai ba sai don bana son yin jayayya da umarnin Umma, amma zan gayawa Yayanki zaku ma mu cigaba da bincike ta k’ark’ashin k’asa amma tabbas zato na akan yaran nan yake..” Na girgiza mata kai. Ta fice daga d’akin bayan na tabbatar ba zani wajen kai lefen ba. K’una zuciyata kawai take da wani d’aci da nake ji a mak’ogaro na.

Ina ji duk aka fice kai lefe. Ya zama gidan ya yi wani irin shiru. Ina kwance idona a lumshe na ji maganar Umma a kaina. “Ke ki zo in ji Abban Sadik.” Ido na na bu’de ka’dan ina kallonta cikin dishi-dishin hawaye na. Itama kallon nawa take sai naga ta juya ta fita daga d’akin. Da k’yar na mik’e saboda matsanancin ciwo da kaina yake. Na yafa mayafi na fita kiran da Abba yake min.

A zaune yake fuskarsa sam ba walwala, ba mamaki Umma ta gaya masa duk abinda ya faru. Gefe ya nuna min bayan ya amsa gaisuwata murya a hankali ya kalleni ya ce…. “Me yasa kike zargin su Zinatu da duk abinda ya faru?” A hankali na yi k’asa da ido na ina wasa da hannu na..”Magana nake miki.” Ya fa’da wannan karan muryarsa a sama ka’dan.. shashshek’ar kuka na fara yi ina furta “Nima ban sani ba Abba, kawai ina tunanin zasu iya aikata min hakan daga yanayin kalamansu a kai na.” Ido ya k’ura min kafin ya ce “Wasu maganganu suka gaya miki?” Tsaf na kwashe na gaya masa, sai naga ya yi shiru, idanunsa sun yi wani irin jaa fiye da na Umma. Murza hannunsa kawai yake kafin ya ce “Akwai inda kika je da su ne a satin bikin ki?” Da sauri na d’aga kai na. na ce Eeh Abba akwai, na je gidansu har ma na yi barci a can, mun je kuma gidan Anty Falmata da wasu gidajen na cikin dangi.” Shirun ya sake yi tsawon mintuna biyar kafin ya furta “Tashi ki tafi ki ba ni wuri, Allah ya bayyana gaskiya.” Tunda abin ya faru yau ne kawai Abba ya min magana cikin kwanciyar murya. Sai na ji wani abu ka’dan ya gushe daga b’acin ran da yake cunkushe a zuciyata.

Tara na dare na jiyo Yaya Usman ya shigo gidan da sauri na mik’e na nufi har sashensu don tun yamma nake jiransa am eager na ga ha’du da shi.

A parlorn dukkansu suke zaune, Ya Usi Ya Umar da Ya Ali. Na gaishesu suka amsa fuskar ba yabo ba fallasa. Ya Usi kam da fara’a sosai ya tare ni. Ya ja hannuna ya zaunar da ni gefensa yana furta “Ya aka yi AYSHA gayu? Koda yake yanzu wannan sunan tsaf ya tashi daga kan ki, duk kin bi kin sukurkuce kamar ba Ayshan Mameey ba…” murmushi kawai na yi ina tuna Mamee a raina. Na ce “Dama murna na zo maka Yaya Usi, duk da dai baka sani a cikin lamarin ba, congrats to you and am happy for you….” Na fa’da wata y’ar k’walla na son zubo min. Kama hannuna ya yi yana furta “Okay Okay na gane, mu je d’aki mu yi maganar har ma na nuna miki hotonta.” Ina mik’ewa muka ha’da ido da Ya.Umar sai na ji bakina kawai ya furta “Congratulations Ya Umar..” Hannu kawai ya ‘d’aga min ina ji Ya.Ali ya zabga tsaki.

Muna shiga na zauna gefen kujera ina kallon hoton da yake mik’o min. Yarinya ce k’arama ba zata zarce sa’ata ba. “Ma sha Allah, gaskiya ta yi ina tayaka murna once again, duk da dai baka saka da ni ba.” Hannuna ya matsa yana furta “Am sorry Aysha kwana biyu kin ga bana damuwa nazo inda kike, wallahi zuciyata bata iya wa tausayi kike ba ni, ina so ki tsaya ki nutsu ki ajiye zuciyarki waje guda ki yi aure, da zarar na yi aure zan mayar da ke can waje na, don naga duk gidan nan ba mai tausaya miki na yi magana da Abba akan ya barki ma ki cigaba da karatu ya nuna min sam ba zai yiyu ba, Miji ma yake nemar miki ya miki aure tun kafin mutane su farga da abinda kika aikata, although dai maganar duniya bata b’uya..Wallahi AYSHA da tunanin matsalarki nake kwana nake tashi, ga shi shi kuma shegen an ce har yanzu bai dawo garin ba, bari mu tuntub’eshi mu ji ko biyansa aka yi don ya b’ata miki suna.”

Murmushi na saki, irin murmushin da na da’de ban yi irinsa ba, jin abinda Ya.Usi ya ce da gaske shi ka’dai ne mutumin da zan bugi k’irji na ce ya yarda ban aikata ba. Ya saka hannu ya share min hawayen da suke zuba a idona duk da ni ban san zubar su ba saboda har ga Allah murmushi nake. Murmushin na sake yi ina kallon cikin idonsa na ce “Ya.Usi na gode sosai da kulawarka gare ni ya sunan amaryar tamu?” “Sadiya” ya furta yana lumshe ido. “And I love her very deeply….” Murmushi na saki ina ajiyar zuciya a hankali na tuna Ustaz da dukkan kalamansa ashe akwai abinda zai saka Ustaz ya rabu da ni, ko wai wayata bai sake yi ba tun bayan afkuwar lamarin nan, ashe duka soyayyar Ustaz a baki take.” Na girgiza kaina kawai kafin na mik’e na bar cikin d’akin saboda kukan da ya taho min….

Da safiyar wata laraba ina zaune a d’akina sai ga sallamar Asma k’awata. Da wata irin murna na tareta. Ita kuwa hawaye naga ya fara zuba daga idonta. Ta saka hannu ta ja hannuna muka fita harabar gidanmu. “Zo mu je AYSHA, zo mu je kada Umma ta fito ta gan ni ita ta hana ni zuwa duk sanda nazo sai ta ce na tafi kawai..” Na bita muka fita harabar gidan mu. Hawayen kawai take ta kasa ce min komai. Sai da na girgiza ta na ce “Wai Asma’u meye haka zuwa kika yi ki sake d’aga min hankali?” Girgiza kai ta yi tana rungume ni a jikinta ta ce “AYSHA Ustaz ya ci amanar soyayya wallahi, abinda ya miki bai kyauta miki ba, ni fa ban san me ya faru ba sai jiya Umma na take gaya min wai an fara zagaya unguwa da cewa da wani k’ato Ustaz ya kama ki ranar auren ki.” Waro ido na yi zuciyata na bugu na ce “Waye ya fa’da Asma?” Ta sake runtse idonta hawaye na zuba a idonta ta ce “Ba wanda bai ji ba AYSHA zancen nan har Islamiyya wallahi….” Tunda abin ya faru sai yau hankalina ya sake masifar tashi jin ashe zancen ya isa har Islamiyya wajen Malaman da suke ganin mutunci na. “Ki gaya min Aysha ya aka yi kika canja daga Ayshan da na sani?” Runtse idona kawai na yi ba tare da na mata magana ba, don bana jin zan iya furta ko kalmar ‘a’ saboda rawa da dukkan jikina yake yi…” na mik’e dai na shige cikin gida a cikin wani irin yanayi da ni kai na ba zan iya cewa ga yarda na kai kaina d’aki ba.
Chapter 9 · 0% Book details