← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 49

Sashe 30

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around twelve sai ga Khadija k’anwarsa ta shigo gidan. Da murmushi na tareta itama ta mayar min da murmushin ta rungumeni kafin ta isa gaban Inna ta durk’usa ta gaisheta. Inna ta mik’e ta fita parlor. Khadija na kallona ta furta “Anty Eehsha, in bi ta bakin Mijinki ya ce lallai sai na dinga ce Miki Anty wai Eehsha, gaskiya kin sake kyau abin ki dole Yaya Ahmad ya dinga rikicewa meye sirrin?” Na d’an yi murmushi kawai ina girgiza kai na ce “Bakomai, ya gida Ya Mommy?” Khadija ta ce “Mommy na nan k’alau, duk da gaskiya bata San nan zan zo ba, sak’on motar ki Ya Ahmad ya ce na kawo miki gata can a k’ofar gida…” dole na k’ak’alo fara’ar dole da murnata na ce “Mota kuma? Kai Masha Allah Amma na gode sosai….” Khadija ta yi murmushi ta ce “Ki godewa Allah da ya baki Mijin da yake tsananin son ki, wallahi AYSHA ban tab’a ganin soyayya irinta Ustaz ba, sanda abin can ya faru fa Har Mommy ta ce ya sake ki Wallahi baki ga tashin hankalin da ya shiga ba, ko abinci baya ci ya rame ya yi bak’i sai idanuwa. Bana manta sanda ya same ni a d’akina yana k’walla ya ce “Khadija, wallahi na san Eehsha ba zata aikata ba, Amma ya zan yi na san Mommy ba zata yarda ba ki bani shawara… wallahi AYSHA kuka na saka bana komai ba sai na tausayinku da makomar zazzafar soyayyarku. Auren Hameeda kuwa ta dole ya amince don ya tubure ba zai aureta ba sai Mommyn ta masa dabaibayi da ke, ta ce idan Har bai aureta ba to wallahi ba zata yarda ya dawo da ke ba,….” hakan da yaji y’a saka a take a lokacin ya amince amma da shara’din sai ya fara dawo da ke, gidan da yake kusa da gidanku ke ya ginawa ba don komai ba sai don Abba ya cigaba da bibiyar lamarin ki Amma Mommy ta k’i yarda ta ce Hameeda ce zata shiga tunda ta nuna tafi son gidan… nan ma hankalinsa ya tashi sai da na dinga bashi baki tukun sannan ya yarda. Kullum zancen yaya Ahmad Eehsha, Allah ya bayyana gaskiya kowa ya san ba karuwa ba ce ke…” Duk suruntun da take jinta kawai nake, ba wai don na yarda ba ni na San daga jin wannan zancen Ustaz ne ya shiryo mata shi. Ta ja hannuna tana furta “Baki yarda ba ko? Ai shikkenan wata rana zaki shaida haka, yanzu muje kiga dalleliyar kyautarki ta mallaka masa budurcinki da kika yi…” Na bita muka fita har Inna da bakinta ya kasa rufuwa sai zunduma wa Ahmad albarka take. Motace mulmulalliya mai kyan gaske naga dai tambarin marcedez a jiki daga haka ba zan iya cewa ya sunanta ba don ni ban wani taso da son mota a raina ba, ban tab’a saka ran zan wani auri mutum mai ku’di kamar Ahmad ba. Daga nan Khadija ta ce ba zata koma ciki ba gida zata koma don Mommy bata son zata zo ba. Na rakata Har vakin gate inda drivern Ahmad zai kaita gida. Ina sake waiwayen motar na shiga gida. Ina shiga Inna ta ce “Amma yaron nan ya kyauta, yanzu kuwa zan yi waya na gaywa iyayenki ai ke auren yaron nan alheri ne a gareki, gashi yana masifar son ki.” Ban wani amsata ba sai y’ar dariya da na yi na shige bedroom. Ina shiga waya na k’ara na ‘daga Naga shine ina tunanin missed calls d’insa na ashirin kenan ba kuma zan d’aga ba sai ya gaji Ya daina kiran, Har a raina da gaske nake zan rabu da Ustaz ko ba yanzu ba. Na cilla wayar cikin drawer bayan na kasheta na Zare sim d’in gaba d’aya ma.

Kwana goma Inna ta yi aka yi waya maigidanta Alhaji Ba lafiya. Hakan yasa ta tattara komatsanta ta tafi gida y’a rage daga ni sai mai aikin da a ka kawo min su biyu dattijuwa da yarinya. Haka zan zauna mu yi hira da su….

Da yammacin wata rana ina zaune a parlor kaina nake tsefewa don kitson ya fara damuna Aka yi nocking. YABI na kalla na ce “Maza bu’de k’ofar…” ta mik’e ta bu’de sai na ji ta ce “Lah Anty Fat….” “Shshss…” na ji ta ce hakan yasa na juya da sauri sai naga Mami ce ta shigo tana murmushi ta ce “Ma sha Allah, ah lallai AYSHA jiki ya yi kyau.” Na gyara zama na muryata cike da rauni na ce “Mami ina yini?” Bata amsa ba sai zama ta yi daf da ni ta min side hug ta furta “Sam AYSHA Baki da kirki, ko nema na ba kya yi, rabuwar kenan? Ai shikkenan ya maki kyau, dama jikin ki nazo dubawa kuma naga da sauk’i Allah ya k’ara afuwa bari na tafi.” Ta mik’e da niyyar tafiya kallonta kawai nake jikina a sanyaye na kasa magana. Ina kallo ta nufi hanyar fita sai sannan na samu damar cewa Mami ki tsaya mana please.” Ta juyo ta min wani kallo ta girgiza kai ta fice daga gidan. Sunkuyar da kaina kawai na yi sai nake jin abinda na yi kamar ban kyauta ba. Da sauri na d’ago ina kallon Yabi na ce “Ke a ina kika San Mami?” Ta d’an yi diri-diri kafin ta ce “Ai na yi aiki a gidansu last year to da na tafi gida ban koma ba.” Na tsura mata ido kawai ina ganin kallon ne ya mata yawa sai Naga ta shige kitchen da sauri. Haka kawai sai naji zuciyata tana wani irin bugu da ban san dalilinsa ba.

Kashegari again sai ga Mommyn su Ustaz. Cikin ginshira ta shigo tana min kallon ‘daid’aya da k’yar take amsa gaisuwata itama abin mamaki sai na ji ta kama sunan Asabe dattijuwar da take taya ni zama… Asaben ma a ladabce ta amsa mata. Hirar da suke ce ta bani mamaki don zahiri sun nuna sun san juna. Da zata tafi ta mik’e tana cewa Asabe mu je na ganki…” Asbaen kuwa ta bita cikin rawar jiki. A tsorace na bi Asabe da kallo har ta je ta dawo ban farka daga mamakin da nake ba. Asabe ta zauna tana dariya da sauri na kalleta na ce “Baba Asabe dama kin san Mommy?” Asabe ta d’aga min kai tana dariya ta ce “Sani kai Hajiya, ai daga can gidan aka kai ni gidanku shine aka kawo ni nan, ai nafi shekaru talatin ina yiwa Mommy aiki, banda ma baki da gane mutane zuwanki na farko ai ina gidan…” Ido kawai na zuba ina kallonta cike da mamaki. Ina kallo itama ta shige kitchen da alama taga ba zan ce komai ba ne. Haka kawai ranar sai naji na kasa samun nutsuwa ba ga Asaben ba, ba ga Yabi ba, dukkansu ba Wanda zan iya sake yarda da shi. Har na danna waya na kira Umma ganin bata d’aga ba sai na kashe wayar kawai. Na mayar da kaina na kwanta da niyyar kashegari zan kirata. Sai dai kuma wani abin al’ajabi sai na manta shaf.

Har bayan kwana biyu, muna zaune a cikin gida muka dinga jin jiniyar y’an sanda. Kamar ma a cikin gidan. Haka kawai sai naji gaba na ya yanke ya fa’di. Na yi saurin jan Hasbunallah a zuciyata, daidai lokacin da aka buga k’ofar parlorn da nake da k’arfin gaske. Zuciyata ta sake bugawa Wanda ban san dalili ba. Asabe ce ta bu’de k’ofar da sauri taja baya tana dafe k’irji ta ce “Mun shiga Uku Aunty y’an sanda…” kafin na yi magana Y’an sandan matan Sun shigo suka d’aga min handcuffs a hankali suka furta “You are under arrest….” Na ware ido ina kallonsu na ce “For what?” Y’ar sandar ta min wani kallon rainin hankali ta ce idan mun je station kya ji… ta wurga min wani hoto wacece wannan idan ba ke ba? Ana zarginki da kisan wannan bawan Allahn bayan kin kwashe masa dalolinsa da kuka je hotel…..” Wata irin ka’dawa jikina da cikina suke…. Na kasa furta komai ina kallon hoton da nake sanye da bak’ak’en kaya baka ganin komai a jikina sai fuskata hannuna d’auke da bindiga a tsakiyar d’akin hotel…..

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA…..46.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.
Chapter 30 · 0% Book details