← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 49

Sashe 4

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sha d’aya na kwanta, bayan na idar da sallahr walaha. Barci awa guda na yi Umma ta shigo wannan karan hauri na tayi da k’afa na bu’de idona da k’yar ina kallonta. “Uban wa zai d’aura abincin ranar?” K’asa na yi da kaina kawai, ina jin wani irin k’una da zuciyata ke yi. Sai naga ta fita kawai tana furta na baki 30 minutes ki fito ki d’aura abincin. Tsabar yarda zuciyata ke suya ma bai saka na yi hawayen ba, idona kawai na lumshe ina jin wani irin tsanar Ustaz na zagaye jiki da zuciyata, duk shine Sila da bai shigo rayuwata ba da duk haka bata faru ba, tabbas ha’duwata da shi ba abinda ya jawo min sai tashin hankali ya wargaza farin cikina ya wargaza na ahalin gidan mu. Wannan masifa har ina? Me yasa idan na ma aikata Ustaz ba zai min uziri ba sai kawai yazo gidanmu ya tona min asiri? Na dinga ha’diyar zuciya ina jin kamar zuciyar tawa zata daina aiki. Haka na mik’e ganin mintuna talatin da Umma ta bani sun cika, sauk’in abin ma girkin ranar na iya gida ne kawai kuma akan gas ake yin sa. Amma ina fitowa sai Umma ta kalleni ta ce Sakwara za ki yi. Da sauri na ce “Sakwara kuma?” Ta zuba min harara ta ce “Eeh pounded Yam, ita Abbanku yake so kuma dakan turmi ba engine ba…” Jingina na yi kawai da bango ina bin bayanta da kallo ina sake tambayar kai na Anya kuwa Umma ita ta kawo ni duniya?”

Tun daga ranar ban huta ba, Umma jibga min aiyuka take masu yawa da suka fi k’arfina. Tun ina jin ciwon jiki idan na yi har na saba ganin bata da ranar dai nawa kamar ma k’ara ingiza ta ake. Na yi bak’i na rame na yi wani irin lalacewa, idanuna suka shige lungu kamar ba AYSHA y’ar gayun Mami ba.

Sam Umma bata barina na yi wanka sai bayan kwana biyu abinda yafi damuna kenan daga izayar da take min, don ni kam ina da son wanka a lokutan baya kafin abin ya faru na kan yi wanka Three times a day wallahi. Yanzu kuwa babu damar haka na zama kamar wata y’ar fursuna tsanar yarda jiki na ya lallace don ma fatata mai kyau ce.

Rabona da na saka Abba kuwa har na manta, balle su Yaya Muhammad. Ya.Usi ne sam baya fushi da ni, ya kan zagayo duk. Dare ya mik’o min d’an abu a leda ko nama ko yoghurt sai dai baya min magana, hakan kuma da yake ban damu ba don na san yana bin umarnin Umma ne.

Da safiyar wata juma’a, lokacin sati biyu cif da faruwar lamarin,
Ina zaune a tsakargida Jummai ce take gyara min kai, sai jin sallamar mutane na yi, ko ba’a fa’da ba na san wacece zuciyata ta buga da k’arfin gaske don na san wacece Muryar Kakata ce da ta haifi Abba, wacce muke kira Inna. K’asa na yi da kaina ina jin yarda zuciyata ke harbawa. Jummai ce ta amsa sallamar, ta amsa a ciki sai sannan na ‘dago na ce “Inna sannu da zuwa…” wani irin kallo ta watso min da yasa hantar cikina ta ka’da na santa sarai mace ce mai zafin gaske, don ko wasan jika da kaka ita ba yi take ba, kullum girarta a tsare ta ke da k’yar ta kan yi murmushi shima ba ya zarce gefen lab’b’anta.

Ta yi k’wafa ta shige parlorn Abba ba tare da ta amsa gaisuwata ba. Umma jikinta na rawa naga ta fito daga d’aki. Ta shiga parlorn Abban itama.

K’walla min kiran da ta yi ne yasa hantar cikina juyawa jikina kamar mazari na mik’e na shiga parlorn Abban. A gefe ba durk’ushe tun kafin ma ta ce min na durk’usa ‘din. Masifa ta cigaba da yi. “Dududu A’in nawa take da za’ace kun kasa bata tarbiyya, Mace guda d’aya jal da Allah ya baku a ce baku san hanyar da zaku tarbiyyantar da ita ba! To dama da nazo bai saki annamimiyar can ba da Allah ka’dai ya san abinda zan muku, haba ni tun a farkon fari ban so ya auri matar nan ba, kana ganinta kaga wayayyiyar da idonta ya Riga ya bu’de da duniya ga shi nan ta gurb’ata muku tarbiyyar y’a da son ranta, ai kuka jawo da kika d’au y’a guda mace da Allah ya baki kika bata, kika kuma ja gefe kika daina saka baki a tarbiyyarta wai ke alkunya, yanzu wa gari ya waya? Wa aka cuta idan ba ke ba? Ga Boko nan Ai kun gani da an yi magana Imamu ya ce wai Fateemah y’ar boko..” Ta yi k’wafa tana cije leb’enta ta ce “Wallahi bata ci bulus ba, yanzu zan je har gidan Uban da ya d’aure mata wani wuri na ci Ubanta la’ada waje har na ha’da da iyayenta iskancin banza da wofi…” Cikin rauni Umma ta ‘dago tana kallonta ta ce “Inna ba za’a yi haka ba, tunda dai ya saketa Ai bai kamata ki je ba…” “sai na je Kubra… ina ce Fateemah ba k’anwar Uwarki ba ce balle ta Ubanki kuma bamu da alak’ar komai da ita tunda bata haihu ba ko? To sai naje, sai ta gaya min dalilin da ta yasa ta saka yarinya a turbar rashin arziki… Ke kuma annamimiya tashi mu je maza ki nuna min gidan, kafin mu dawo ki gaya min abokin shai’danancin naki shima na je har gidan Ubansa na ci mutuncinsu….” Zufa ce ta dinga zubo min, ni kuwa me yasa Inna zata ja ni gidan su Mami ni sam ba zan iya kallo Mami ba, duk da abinda ta min har yau da tausayinta a raina, sai dai sam ban isa na yiwa wannan jarababbar matar musu ba. Jikina a salub’e na mik’e ba bi bayan Innan da take ta min masifa… “Allah dai ya wadaran boko, ba ga abinda nake gayawa Imamu ba kullum nazo sai nace ya aurar dake ya ce min wani Zamani ya canja, ai gashi nan yanzu yaga zamanin a gidansa…”

Ni dai shiru na yi mata. Ko a cikin motar masifar da take ta yi kenan. Idona lumshe har muka isa gidansu Mami. Ina ganin mu a k’ofar gidan gaba na ya yi wani masifaffen fa’duwa….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️

https://chat.whatsapp.com/EuW3Jn8UkDrJudA1ThiH23

Kina buqatar kayan kitchen Masu kyau da rahusa?
Kina buqatar inda zaki dinga samun kaya Masu quality?
Uwar gda Amarya Duk ku tawo 💃🏽

Quality shine takenmu 😻 Muna maraba da masu sayan daya ko sari 👯‍♂️ Muna tura kaya ko ina da yardar Allah cikin Aminci😻 muna zauna a garin Kano cikin kwaryar birni👯‍♂️ masu sayan kayanmu Mina godia👯‍♂️[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 26…

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.

★★✍️

Bayan na koma barcin still wani
Mafarkin na sake yi ana sake k’yakyata min dariya ba k’akkautawa. Ina gudun ana bina na durk’ushe a wajen ina wani irin kuka ba na komai ba sai na neman taimako, ina kuma addu’ar Allah ya raba ni da koma menene mai bi na d’in…
A kusa da ni aka yi maganar da ta kusa saka ni na zauce. “Ba ki da mafita Aysha, baki da mafitar da ta zarce addu’a, idan kowa ya k’i ki mu muna son ki….

daidai nan na mafarka sakamakon dukan da Umma ta kai min a gefen cikina. A firgice nake kallon Umman da itama ta k’ura min ido, kafin naga ta d’an janye idonta da kaina, idan ba idona ba ne ya gano min ba daidai ba, sai naga kamar k’walla ta share. “Ki tashi an yi sallah ki fita ki yi aikin ki…” ta fa’da cikin raunin muryar da ta sake sanyayar min da jiki. Na mik’e jikina a salub’e na fita na yi alwala. Ko da gari ya waye na gama duk Ayyuka na, sai na ji zuciyata ta yi sanyi bayan idar da sallahr walahar da ta zame min jiki. Na zauna ina sake tariyo mafarki na, na ji a raina tabbas na amince da cewa Aljannu ne suka aure ni, suka fito min ta wannan hanyar. Ina son na je na gayawa Umma amma zuciyata na kwab’ata don haka na k’udundune maganar na barta cikin raina, dafatan Allah yasa naga Ya.Usi na gaya masa mafarkin ko ya samar min mafita.
Chapter 4 · 0% Book details