Sashe 18
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da safe sai sha biyu na bu’de idona tun bayan sallahr asuba nauyayyen barci ya d’aukeni. Duk da naji zuwan Ustaz da nocking da yake bai saka ni tashi ba sai a wannan lokacin. Wanka na yi na tsantsara kwalliya cikin wani army green brocade d’ina da d’inkin ya yi bala’in fito da duk wata sura ta jikina Pitet ce sosai Kuma yawanci d’inkunan da aka min kenan. Gashi na da yasha gyara na kwantar a saman kafa’duna kafin na kafa d’aurin ture kaga tsiya. Bakina har da jambaki da ya k’arawa bakin kyau. Hakan yana daga cikin target d’ina na son tadawa Ustaz hankali.
Sarkin naci! Na fa’da a zuciyata ganin still yana kwance akan kujerar da take babban parlor na idonsa a lumshe parlorn duk ya ba’de da k’amshinsa. Karatun Alk’ur’ani yake saurara. Jikinsa wasu irin k’ananan kaya ne masu masifar kyau ni sai abin ma ya min wani banbarakwai ko don ban saba ganinsa da su ba ne. Juya jikina na dinga yi sosai musamman da naga ya bu’de idon sa a kaina yana lumshe su a hankali kamar mai jin barci. Dangwaliliya sosai nake masa kuma a jikina na ji kallon da yake min har na shige k’ofar da zata kai ni kitchen. Ina shiga na saki dariya na ce D’aya kenan!
A kitchen aikina nake na fere Irish ina yi ina bin sautin wak’ar da yake kunnena don ya kashe karatun. Juya jikina nake a lokacin ni kaina mamakin abubuwan da nake yi nake. Saboda ba zaka tab’a cewa waccan AYSHAn mai tsananin kunya ba ce. Jin sa na yi ya jani jikinsa ta baya ya rungume sosai gaba d’aya yabi ya baibaye hancina da mayataccen k’amshinsa “Ba gaisuwa?” Ya ra’da min a kunne cikin wata irin Husky Voice da sauri na runtse ido ina ji ya sake shinshinar wuya na ya ce “Uhmn Aysha? Na ce ba gaisuwa…” Ture shi na fara yi amma ya k’i bani damar hakan. “Ki bari Aysha you are my halal, me yasa kike hana ni? Ki gaishe ni na ce..” “Ba zan gaisheka ba Ahmad.” Madadin ya damu sai naga ya ja karan hancina kafin ya kai bakinsa saman wuyana ya sake shinshina wuyana ya ce “Your perfume makes me….” Sai kawai ya yi shiru yana lumshe ido. Yana k’ok’arin sake ja na jikinsa na yi saurin ture shi ina kallon yanayin da yake bin k’irjina da kallo. “Mugu kawai kada ka sake tab’a ni…” “Ai kuwa kin yi ka’dan dama ace budurwa ce ke dal zan iya d’aga miki k’afa amma ke ai kin zama y’ar hannu wani abin ma sai dai ki koya min….” “AHMAD! ya isheka, na ce maka Is enough ba zan sake tolerating ba, na ji ni karuwa ce Uban wa ya ce ka dawo da ni gidanka, ka cigaba da barina na yi gantalin mana… to ya isheka ba zan sake yafe maka ba ka sake kira na da banzan suna…” Tab’e baki ya yi naga ya fita daga kitchen d’in yana fad’in “Bari na wuce kafin ta kai ki fara duka na, ashe bayan wancan harkar har da rashin kunya kika koyo, koda yake duk wanda zai iya abinda kika yi Ai ba batun kunya a tare da shi…” “Ashe ka sani, ai rashin kunya ma yanzu ka fara gani.”
Sai da na gama ha’da break fast sannan na fice da abincin na jere a kan Dinning iya cikina ka’dai na dafa. Gidan ya ba’de da wani irin k’amshi. Na zuba a plate na koma daidai saitinsa na zauna ina cin abincin cike da gwasalo da yanga, ina kuma bin wak’ata cikin muryata mai zak’i.
Dubana yake k’asa-k’asa wani irin kallo mai cike da raini da rashin ganin girman wanda akewa shi. Hakan yasa naji tamkar na ha’diye zuciya na mutu duk da ban nuna masa akan fuskata ba. Bak’in cikin ganinsa nake balle na kirashi mijina. Ina kallo ya shiga d’aki ya canja kaya zuwa jallabiya mai shegen kyau ya fito yana zanga k’amshin turare waya a kunnensa yana amsawa k’asa-k’asa kamar baya so. Yana kallona bai fasa wayar ba ya ce “Ki shirya zamu asibiti…dole ne a binciki lafiyar ki don ina cikin ru’dani…” a k’ufule na ‘dago na masa kallon baka isa ba ka yi ka’dan, sannan na ce “Ba zan je ba, ai ba dole aka maka ka zauna da ni ba, idan kaga kana kokwanton lafiyata kawai ka sake ni mana.” Dariya ya yi sosai irin dariyar da ake wa mutumin da ya fa’di magana mara amfani…. “Dole fa ki je asibitin nan idan ba kina son na kira Abba na gaya masa ba.”
K’emadagas na masa na mik’e na shige d’akin ina jin a raina ko me za’ayi ba zan je asibitin ba. Tsawon mintuna biyar sai ga shi ya biyoni d’akin waya kawai ya sa min a kunne yana furta “Abba..” ina sallama Abba ya rufe ni da fa’dan da yasa na runtse idona. Ina ji Ustaz ya zira min wani babban Hijab mai kama da julbab brown color kalar jallabiyarsa ya ja hannuna muka fice. Kasa musa masa na yi saboda yarda fa’dan Abba yake nuk’urk’usar zuciyata, har hakan ya bayyana a gabbaina na samu kasalar jiki. Ina ji ya ce “Koda yake ba fa amfanin Hijab d’in tunda dama na yaudara ne duniya ta Riga ta san jikin ki…” runtse idona kawai na yi ina ji ya saka ni a gaban motarsa na furzar da wani huci ina jin Anya zuciyata zata d’auki wannan tozarcin har zuwa ranar bayyanar gaskiya abinda kamar wuya. Duk kalmar b’atancin da na yi niyyar fa’da sai naga ta yiwa wannan mugun azzalimin ka’dan. Muna shiga asibitin muka isa reception sai na ji yana tambayar nurse akwai female Doctor on duty? Mata shigar budurwar ta ‘d’aga kai ta fito da file d’in da inaga tuni ya bu’de don shi ya bata numberr file d’in, muka nufi office d’in Doctor. Kallona matar take tana murmushi ta furta “Congratulations Ahmad for having a beautiful wife…” Naga ya yi murmushi kawai sannan ya sanar mata Test za’a min na H.I.V likitan ta d’an waro ido ka’dan ta ce “But why?” Ya cije leb’ensa kawai idanunsa sun yi jajur ya ce “Nima zaki min, mun manta ba mu yi ba ne.” Sai naga ta saki murmushi ta ce “Alright, hakan yana da kyau.” Ta rubuta mana sannan ta ce Mu je laboratory nasu. Har muka isa Lab d’in zabga masa harara nake cikin jin haushinsa aka d’au jininmu sannan aka ce mu jira a waje. Allah ne kawai yake dannar zuciyata tsawon zaman da muka yi ban rufe Ustaz da duka ba, duk da dai ya ceci kansa da ya ce a yi test d’in har da shi. Ba abinda ya d’aga hankalina don na san bana d’auke da kowace shegiyar cuta. Tsawon lokaci kafin a fito da result d’in. Sannan muka koma wajen likitan. Sai da ta mana nasiha sannan ta bu’de result d’in tana murmushi ta ce “Negative, sam baku d’auke da wannan cutar Allah ya sake kiyayewa.” Mainakon naga farin ciki a fuskarsa sai naga ya saki wani fake smiling haka ya mik’e yana yiwa likitan godiya.
Muna shiga mota ya ce “Allah ya ceceki, amma fa ki daina murna dole sai mun sake zuwa wani hospital d’in an sake duba ki, don I don’t trust you anymore.” Na ha’diye wani kalar yawu kafin na ce “And so what? Idan kai baka yarda da ni ba, in dai Allah ya yarda da ni Alhamdulilah!” “Kada ki min rashin kunya, wallahi zan zaneki a banza, baki san yarda zuciyata ke hurting ba ko? Zan huce a kan ki wallahi, ki bar ni na ji ma da abinda ke damuna shashasha” Ya fa’da fuskarsa sam ba alamar wasa.. tsaki na ja na ce “Wallahi ba zan zauna ka dokeni ba, sai dai mu doki juna, shashasha kuwa da ka fa’da sunan mu d’aya…” Waro idonsa ya yi ya ce “Really?” Na ce “Offcourse” ya saki fake smile d’insa ya ce “Bari mu je gida naga ko zaki iya duka na mara kunya, yau kam zan k’ure miki abinda ke saki rashin kunya, zaki san ni ba mate d’in wa’dancan tarkacen samarin naki ba ne….” “Allah ya kai mu.” Na furta ina d’auke kai. K’wafa ya yi kafin ya ja motar a mugun speed ya bar cikin hospital d’in.
Daga ranar ban sake ganinsa ba, ko na gansa ma ba ya shiga sabgata sai dai ya harareni ya d’auke kai. Ni ma bana k’asa a gwiwa nake ramawa sai kawai ya tab’e baki ya wuce.
Yau ni ka’dai ce a gidan don kwana na biyu ma ban saka Ustaz a gidan ba. Kwance nake akan tattausan carpet d’in da yake tsakiyar parlorn na dinga jin ana nocking a hankali. Bu’de idona na yi a hankali na mik’e na isa bakin k’ofar a hankali na ce “Waye?” Wata murya mai kama da ta Mami na ta amsa da “Ni ce Aysha bu’de…” Da azama na bu’de k’ofar cikin mamaki na ware idona ganin da gaske Mami na ce a tsaye a bakin k’ofar, tana sanye cikin dogon Hijab idanunta a kai na tana sakar min murmushi…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA… 37.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.