← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 49

Sashe 16

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da na yi kukan sosai har naji kaina na sarawa, sannan na ji shigowar Ustaz cikin d’akin. Da sauri na lumshe idona kamar mai barci duk da wani zazzab’i ne naji yana ratsa k’asusuwan jikina. Zama ya yi a gefen gadon shirun da na ji ne ya saka ni bu’de idona sai naga nasa idon a lumshe ya jingina da gefen gadon. Muryarsa da yake bayyana damuwa ya ce “Ki tashi ki yi alwala zamu yi sallah.” Na mik’e da sauri na ce “Idan na k’i fa?” Ya zuba min ido yana furta “Dole ma zaki yi, don sunnah ce ga duk ma’aurata kafin su kusanci juna, duk da dai ni ba kusantarki zan yi ba, amma tabbas zan yi romacing jikinki har na samu nutsuwa don na gaji da tara abinda ke jikina, shi yasa ma na dawo da ke.” Ya fa’da yana narkar da idonsa a cikin nawa, kallonsa kawai nake da mamakin furucinsa a zuciye na ce “Sha’awata kake shi yasa ka dawo da ni gidanka kenan?” Ya ‘d’aga min kai. “Lefi ne don na yi sha’awarki? Wasu banza ma suka yi sha’awarki, abinda zai hana ni gurzar ki son raina yau naci alk’awarin kema ba zaki fara sani na d’a namiji ba sai na miki kishiya ba don komai ba sai don kiji abinda na ji ba zaki b’areni a leda ba kamar yarda ban b’areki ba, kuma dole gobe akwai Doctorn da zata zo ta miki test…” wani kalan zabura na yi, ina jifansa da wani kallo. Ya sake d’aga kansa yana murmushi ya d’agan gira. “Oya tashi ki yi alwala Madam, and after the prayer you must remove all your clothes yau zahirin ki nake son gani na more…..

Mu ha’du da daddare may be a Arewabooks 😜

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 38…

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Baki na saki kawai ina kallonta ta cigaba da fa’din. “Hmn, ai ni wallahi Ustaz bai kyauta min ba, na zata ke fa zai kawo kusa da mu ya tamfatsa wani Uban gini mai masifar kyau, ga amaryar daga ganinta tana da wayayyan kai kuma ta girme mu sosai a shekaru sai kin dage AYSHA don y’an r gayu ce wallahi, abinda ma ya kawo ni kenan na fa’da miki ki tashi tsaye sosai kada ta k’wace miki Miji….” murmushi kawai nake ina kallonta har ta gaji ta zabga min harara. “Wai ba zaki ce komai ba ne? Ni ya naga kamar ba ki san da kishiyar ba fuskarki looking so exhausted…..” na dafa ta ina jan hannunta muka shiga cikin parlor muka zauna sannan na ce mata “Asma’u ban san Ustaz ya yi aure ba, amma ba zan ce komai ba sai Allah ya bada zaman lafiya ….” Cikin mamaki Asma take kallo na ta ce “Baki sani ba As in how? Ta yaya zai yi aure without you knowing?” Na tab’e baki ina ware hannu alamun ban damu ba sai na ga ta yi turus ta ce “AYSHA you looked not worried? Kan ki d’aya kuwa?” Na ce “Da biyu ne Asma? Baya gabana ne kawai, ya je ya yi ta aurensa bakomai tawa k’addararce haka, ina addu’ar Allah ya bani ikon amsar ta a yarda tazo min.” Jikinta a sanyaye take kallo na. Ta ce “Ba ki damu ba AYSHA?” Na girgiza kai Ina furta “Ban damu ba Asma, me ke gareta? Da zan sawa kai na damuwa? A zatona abinda kake so shi kake kishi… na tsani Ustaz irin tsanar da ba zan ma iya kwatanta miki ba, I hate him wholeheartedly kuma bana jin akwai abinda zai saka nan gaba na so shi, wallahi ko mata d’ari zai aura a yanzu dai ba zai dame ni ba, ba kuma ya gaba na, daga shi har matar tasa ba su isheni kallo ba, ni yanzu kawai ibada na saka a gaba da fatan cikawa da Imani. Rayuwar nan da duk abubuwan nan da suke cikinta wallahi tsoro suke ba ni.” Asma jinjina kai kawai yake kafin ta ce “Wai kina nufin har yanzu baku koma daidai da Ustaz ba?” Na sakar mata murmushi kawai ina mik’ewa na shiga kitchen na samo mata drinks da wasu snacks ragowar na safe da na yi na ci. Bata wani jima ba ta tafi bayan ta gama bani hak’uri sosai ta na sake gaya min AYSHA sai kin dage sosai akan Mijin ki fa…Ina gaya maki waccan matar idonta tar yake kuma billah da shekarunta don idan aka ce zata yi sa’ar sa ma I won’t surprised, so sai kin yi ta kan ki.” Na yi dariya kawai na rakata har gate ta tafi bayan na ha’da mata kayan cosmetics da yawa a leda.

Da daddare sai ga Umma Yaya Usman ne ya kawo ta. Kadaran kadahan na nuna mata na yi farin cikin ganinta. Na kawo mata drinks da snacks da bana rabo da su, after na yi warming d’insu a microwave. Ta d’an zagaye idonta da kallo tana furta “Alhamdulillah, dama na san ba zaki bani kunya ba indai ta b’angaren tsaftar jiki da muhalli ce.” Na ‘dan yi murmushi kawai. Ta ce “Sai kika ji labarin Ustaz ya yi aure? To bana son ki saka damuwa a ranki, kishiya dai baa kanki aka fara ba, a gidanku ma mutum biyu kika bu’de ido kika gani, kuma Abbanki ma da kansa ya sake bashi support na k’ara auren, Allah ya bada zaman lafiya ki sake kula sosai banda bin zugar k’awaye, a kuma dinga danne kishi, namiji baya son mace mai zafin kishi da yawa….” Haka dai ta yi ta min nasiha kafin su tafi, ni dai jinta kawai nake ba wai don zan iya kwatanta abinda ta gaya min ko ka’dan na yiwa Ustaz biyayya ba. Ta turo min wasu pack, maza kwashe Kazar sababi ce ta Surayya Dee da garurrukan magani ki sake dagewa da kula da jikinki don shine kima da martabar mace, Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da dukkan fitina.” Na amsa da ameen, ina kallo suka tafi bayan Yaya Usman ya jani da tsokana ya kuma yi alk’awarin kawo min matarsa jibi. Ina ta son na gayawa Umma Mami na ta zo sai dai wata zuciyar tawa tana kwab’ata, dole na yi shiru ina kallo Yaya Usman ya ja mota suka tafi.

Na dawo cikin gidan ina kallon Kazar da Umma ta kawo min, na d’an tab’e baki ban k’i ci ba na zauna na ci a bata don daga d’and’ana romon na ji ta yi da’di sosai kamar ba kazar magani ba. Na sha tsumin Maman Fareeda sai ga wata gyatsa na yi. Ban yi shirin d’ora abinci ba don na san ba zan ji yunwa ba idan ma naji yunwar zan sha cereals, kawai na kunna t.v ina kallo, zuciyata na ta tunanin me Zan yiwa Ustaz na nuna masa ban damu da aurensa ba.

Dabara ce ta fa’do min, don haka na mik’e na isa harabar gidan na kira d’aya daga cikin masu hidimar gidan. Ku’di na bashi da takardar da zai siyo min abubuwan da Zan buk’ata. Ina kallo ya yi d’an turus nima kallonsa nake na ce “Ya ne ko ba zaka je ba?” Ya girgiza kai da sauri ya furta “Idan na dawo zan ajiye a k’ofar kitchen ta baya don Alhaji ya ce koda wasa kada mu sake mu yi wa matarsa magana…” ji na yi kamar na k’unduma zagi, sai dai na dake zuciyata na yi tsaki na ce “Idan ka dawo ka ajiye ‘din, ka danna door bell don na san ka dawo.” Na shige ciki zuciyata a zafafe ina ta mitar “mutum sai shegen kishin tsiya.”

Ai kuwa bayan three hours sai ga shi ya danna door bell d’in. Na mik’e na isa k’ofar kitchen d’in ta baya. Duk abinda na rubuta ya siyo min. Na kalli kayan ina murmushi greeting cards ne masu shegen kyau an rubuta Happy married life da wasu frames. Sai da na d’auko biro n zauna akan kujera da niyyar na rubuta sunayensu sai na tuna ban san sunan matar tasa ba. Tsaki na ja na rubuta Happy Married Life You and your new bride…” na warwatsasu ko ina har a bakin k’ofa ta yarda duk tsiyar sa idan ya shigo sai ya gani.
Chapter 16 · 0% Book details