← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 49

Sashe 35

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motsinta na ji a toilet sai gata ta fito tana sakin murmushi ta ce “Ayshatu kin shigo? To maza ki je ki shiga ki yi wanka na ha’da Miki ruwan wankan ki d’an rage kafin an jima ki je Saloon.” Cikin tausasawar murya take min maganar, sai na ji ta bani tausayi ganin yarda Har lokacin ta kasa sakin jiki ta ha’da ido da ni. Hakan yasa na fa’da jikinta na rungumeta sosai na sake kuka mai k’arfi sosai. Itama rungumenin ta yi tana sakin nata kukan da na tabbatar na abinda ta dinga min ne yake cin zuciyarta. Da k’yar na d’ago daga jikinta na zame na shige toilet. Wani irin wanka na yi da Har sai da na fara jin ra’dadi a fatar jikina sannan na hak’ura na bar dirzar kai na. Na yi sab’i ya kai ashirin gashin kaina kuwa ban san irin wankin da na masa ba har sai da Umma ta gaji ta fara buga min k’ofa tana kiran sunana. Hakan yasa na hak’ura na d’auro towel na fito daga toilet d’in. Umma na kallo na ta ce “Lallai kin dirzu AYSHA ji yarda fatar jikin ki Har wani ja take. Murmushi na yi na ce “Ba dole ba Umma, a sati fa sau d’aya suke bari mu yi wanka, wallahi ni kaina Har warin kaina na dinga ji.” Umma cikin tausaywa ta ce “Mun gode Allah dai da komai ya zama sai labari.” Zama na yi a gaban dressing mirror na shiga murtsike jikina da Neutrogena oil and body lotion. Ban yi wani makeup ba Umma ta kawo wata sabuwar riga light orange mai kyau sosai na zura a jikina. Da kanta ta min drying kai na ta gyara shi tsaf sai shinning yake. Gaba d’aya na ji jikina ya canja wata irin iska mai da’din gaske sai shigata take, kai Allah ya raba mu da k’addarar da zata kai mu gidan gyaran hali. D’ankwali na d’aura a kaina sannan na fita harabar gidan namu inda aka baza daddumai da tabarmi d’aya bayan d’aya na dinga gaisawa da jama’a kafin na zauna kusa da Anty Khadija da take fama da tsohon cikinta. Ya Usman ne ya yafito ni da hannu na mik’e na isa inda yake. A hankali ya ja hannuna ban san inda zai kai ni ba, na ga dai ya nufi d’akunansu da suke can daga gefe harabar gidan. Muna zuwa bakin k’ofar ya ce “Bana son musu AYSHA, ki shiga mijinki na nemanki.” Wani kallo na zuba masa na ce “Yaya Usman Miji kuma? Ai bani da Miji a halin yanzu…” kafin na rufe baki na ji an yi sama da ni ko ban yi magana ba na san Ustaz ne don naji mayataccen k’amshin turarensa…..

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 50…..

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Shiru na mata kafin na tab’e baki na ce oho musu, ban san me suke nufi ba Mami, na dai ji Abba yana cewa yarinyar zata iya zama daga ahalinsu saboda matsananciyar kamar da muke, kuma ai kin ga masu kama da ni suna da yawa a dangi ko?” Murmushi na ga ta saki a hankali irin murmushin nan na gefen baki, ta ce “Ai kuwa masu kama da ke suna da yawa a dangi, zai iya yiwuwa y’ar wani ce a family.” Na ce “To Mami yaushe zaki dawo, tun da gaskiya ta bayyana?” Girgiza kanta ta yi ta ce “Ba rana AYSHA, kada ma ki sake min maganar nan, na bar gidanku har abada, wane irin cin mutunci ne Abbanki bai yi min ba da shi da zuri’arku gaba d’aya, Usmanu ne kawai bai zargeni ba don har nan gidan yazo yana bani hak’uri haka Ummanku ba abinda zan ce mata don ban ga alamun jin haushina a tattare da ita ba. Sai dai da yake ban san zuciyarta ba.” Shiru na yi na kasa cewa Mami komai, don ni da kaina shaida ce na San an ci zarafin Mami na, akan laifin da na tabbata bata ji ba bata gani ba.”

Na da’de sosai don sai k’arfe uku na tafi, ina sake baiwa Mami hak’uri Amma ta nuna min sam ba zata hak’ura ba. Don ce wa ta sake yi AYSHA ni da gidanku Har abada.” Na mata sallama na tafi, ko ka’dan ban ga laifinta ba don ta k’i komawa gidan Abba don nima na sha alwashin ba zan koma gidan Ustaz ba, saboda irin maganganun da ya shak’a min masu kama da k’amshin mutuwa. Sanda na sauka har kusa da Mama na isa ina dariya na furta “Hajiya Mamanmu na tafi sai na dawo kuma? Ki dai daina cewa zaki zuba tsere da wannan gurguwar k’afar taki.” A fusace ta ce “Ubanki Imamu shine gurgu, jairar yarinya.” Na fice ina dariya abu na.

A harabar gidanmu na tarar da dalleliyar motar tasa, sai walwali take. Tsaki na ja a zuciyata don na San shine saboda mayataccen k’amshin turarensa da na ji. A can gefe na hango su shi da Yaya Farouk. Tun daga nesan na ji kaifafan idanuwansa a kaina. Tsaki na zabga ina sake tsuke fuskata na shige su daga shi Har Yaya Farouk d’in ba wanda ya isheni kallo a cikinsu. Dalili suma su Yaya Farouk d’in Har yau ban daina jin haushinsu ba. Har na wuce Ya Farouk ya taso da sauri ya biyo baya na yana kiran sunana. Banda bana son na nuna masa raini a gaban Ustaz da ba zan tsaya ba. Sai da ya k’araso sannan ya ce “AYSHA kina kallon Mijinki kika share shi kika wuce baki tsaya kun gaisa ba, wannan fa ba tarbiyyar gidan nan ba ce..” wani kallo na watsa masa ina gani ya waro ido da alama mamakin kallon yake na kuwa tsuke fuska na ce ya je ya nemi matarsa, don ni ba matarsa ba ce na wuce tunaninsa.” Da haka na juya zan shiga gida. Ji na yi an ja hannuna an rik’e gam ko ba’a fa’d’a ba na San Ustaz ne daga jin yarda yanayin jikina ya sauya. Ga bala’in k’amshin sa da ya cika min ciki. Hannun na so na fisge sai dai ya k’i bani dama. Na juya a fusace ina masa wulak’antaccen kallo na ce “For the last time, malam na sake gaya maka kada ka sake rik’e min hannu…” Shima fuskarsa a d’aure ya ce “Da izinin wa kika fita? Da wannan gantalallen mayafin? Ko kina nufin don kin saka abaya shi zai baki damar fita ba mayafi da aure na a kan ki?” Tsaki na yi na ce “Na fita d’in, jikina ko naka? Sau nawa zan gaya maka kada ka sake kira na da sunan matarka, How I wish zaka iya ganin zuciyata kaga tarin tsanarka da take ciki…” Runtse idonsa Naga ya yi. Ya k’i sakar min hannun kuma a hankali ya bu’de idonsa da suka juya zuwa wani launi murya cike da kasala ya ce “You hated me but I love you AYSHA, na gode je ki gida.” Daga haka ya sab’ule hannunsa ya juya ya tafi. D’an tab’e baki na nayi duk da wani sashen na zuciyata yana son tausaya masa sai dai na k’i barin hakan ya yi tasiri.

————ZAMAN KOTU————-

Ranar da za’a koma kotu da wuri muka tafi. Da kam na ce ba zan je ba, amma Ya Usman ya ce dole na ne na je. Ina kallo Umma jikinta a sanyaye take shiryawa har muka je kotun kuma yanayin walwalarta bai dawo ba. Mu ne a sahun farko a kujerun kotun. Fuskata sanye da bak’in glass kuma don na bawa Ustaz haushi yau ma ban saka Hijab ba, rolling na yi da mayafin abaya ta, na sha kwalliya a bina. Bakina har da chewingum ina tauna shi kamar da gayya haka nake satar kallon Ustaz yana ta zuban harara.

Kotun ta d’inke da jama’a, kowa na son jin k’arshen shari’ar da zan kira mai sark’ak’iya. Ina ta hango Ahmad yana ta sakar min harara ni rabon ma dana gansa tun ranar da na gasa masa magana a harabar gidanmu. Ko waya ya daina yi min.

Tsawon mintuna Ashirin muka d’auka kafin Alk’ali ya shigo aka buga gudumar kotu hakan ya bawa Kotun damar yin shiru. Aka kasa kunne saurarar Alk’ali. Su SHANY aka shigo da su kowacce sanye cikin dogon Hijab sai dai fuskokinsu a bu’de suke. Sai dai a fuskarsu zaka hango Sun rame ka’dan da alama a duk inda aka aje su basa jin da’di.

Alk’ali ya kallesu d’aya bayan d’aya kafin naga ya gyara glass d’insa yana kallon lawyoyin da suke zaune kowa da takardu a gabansa. Alk’ali ya kalle su gaba d’aya kafin ya ce “A fito da Atine…” kowa ya zuba idon son ganin wacece Mama Atine. Kanta a k’asa ta fito tana yatsina fuska kana kallonta kaga cikakkiyar y’ar duniya mai ji da iskanci. Kowa zuba mata ido ya yi Kotu ta fara k’ananan surutai daga bakunan jama’a Wanda majority nasu tsinewa Atine ake. Ni kaina tsanar matar ce ta shiga zuciyata Farat d’aya na dinga Allah wadarai da ita. Allah dai ya shirya musulmi. Shi na ji Umma ta ce cikin raunanninyar muryar da ta saka ni kallonta da sauri. Alk’ali ya dubeta ya ce “Ke ce Atine Harka?” Ba tare da b’ata lokaci ba ta d’aga kai tana cije bak’in leb’enta. “Ni ce Atine.” Alk’ali ya jinjina kai ya ce “Ko zaki gaya min alak’ar ki da wa’dannan yaran? Kin san su?” Cike da confidence ta kalli Alk’ali ta ce “K’warai na san su…” “Menene ha’dinki da su?” Ta d’an tab’e baki ta ce “matsayin Uwa nake garesu tun daga jarirantaka Har kawo yanzu.” Alk’ali cike da mamaki ya ce “Matsayin Uwa? Kamar yaya? Kina nufin yaranki ne ko na y’anuwanki kike rik’o?” Anan kam tsit Atine ta yi, ta yi k’asa da kanta tana murza hannayenta alamar rashin gaskiya k’uru k’uru a fuskarta a zuciyata na ce Munafuka.
Chapter 35 · 0% Book details