← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 49

Sashe 40

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da ya kama za’a kai amare. A ranar na ji labari wajen Anty Khadija wai nima zan bi Mijina Abu Dhabi a ranar da daddare. Wani irin k’ululu ne y’a tsaya min a mak’ogaro na kasa furta komai sai binta nake da ido. Har sai da ta gaji da kallon ta bushe min ido tana furta “AYSHA lafiya? Kika shiga irin wannan shock haka?” Na saki ajiyar zuciya mai k’arfin gaske kafin na fashe da kuka na ce “Abu dhabi fa kika ce Anty Khadi? Wallahi bana son mutumin nan kuma duk da haka ba zai barni cikin y’an uwana ba sai ya cilla ni wata uwa duniya.” Anty Khadi ta dafa cinyata ta ce “Ki saka a ranki wannan k’addarar ki ce, shi a can yake kasuwancin sa, baya ga haka kuma ya amince za ki karatun da kike so a can, ba shikkenan ba burinki da na Maminki ya cika kun samu Wanda zia barki ki yi karatu.” Kuka nake sosai a jikinta na ce “Ni na hak’ura da karatun har abada in dai don haka aka d’aura min aure da shi.” Aunty Khadi ta ce “Aa fa AYSHA, yanzu ai lokaci ai ya k’ure ko so kike a fara k’irga Miki aure? Dukkan wasu shirye shirye sun kankama yau za ki bi mijinki.” Daga haka ta mik’e rik’e da d’an jaririnta sunan Abba muna ce masa Jawad ta fice. Kifewa na yi akan gado. Kukan ma da nake yi y’a d’auke d’if ba abinda nake ji a zuciyata sai wani irin matsanancin b’acin rai da tashin hankali Mara misali. Ban san wainar da ake toyawa a cikin gidan ba, don ban tashi ba sai daf da magriba, cikin matsanancin b’acin rai da na k’uncin zuciya. Na ma manta da zancen wai yau Mijina zai tafi da ni Abu Dhabi. Wanka kawai na shiga ko na ji sanyi a raina. Ina fitowa d’aure da towel a jikina na ga gari ya yi duhu. Sai ji na yi an turo k’ofa an shigo ina d’aga kai na ga Anty Khadija rik’e da wani k’aramin akwati a hannunta tana kallo na da alamun rashin wasa a fuskarta ta ajiye Box d’in ta ce “Ashe ma kin yi wanka, don har ya fara waya jirginku k’arfe goma zai tashi kada a yi delay. Ki samu ki shirya ga can k’anne ki suna jira ku yi sallama kafin a kai su d’akin mazajensu.” Wani irin rawa jikina yake ina kallon Anty Khadija da sam abinda take fa’da baya damunta naga itama yau har da kishiya za’a kai mata amma sam bata damu ba, mace ce mai wata irin zuciya Mara misali. Ta fita sai gata ta sake dawowa wannan karan kaskon turaren wuta ne a hannunta sai zabga k’amshi yake ta ajiye daf da ni. Sannan ta mik’a min Humar da kwalacca tana danna wayarta ta k’ara min a kunne “Maminki zata Miki magana, saura ki mata kuka ki d’aga mata hankali.” Ai kuwa ban ji kashedin Anty Khadija ba ina karb’a na fasa mata kukan sosai. Kamar ba zata yi magana ba, sai can ta saki ajiyar zuciya ta ce “Yi shiru Babyn Mami, ki kwantar da hankalinki zan Miki wani alk’awari muddin kika yarda kika yi zaman aure da kyau cikin soyayya da kulawa ni kuma zan share Miki hawayenki zan kuma dawo gidanku.” Na bu’de ido na da sauri Har ban san sanda murmushi ya sub’uce min ba na furta “Da gaske Mami?” Sautin murmushi ta na ji tana furta “Am serious Baby, buri na kawai ki bawa Mara d’a kunya.” Haka ta min nasiha sosai sannan ta ce “A cikin akwatin da na aiko Miki da kayan da zaki saka yau, akwai magunguna a ciki kada ki yi wasa da su masu kyau ne na gaske na saka matar ta rubuta Miki duk bayanin yarda zaki amfani da su. Allah ya miki albarka ya yiwa rayuwar aurenku albarka ki dage da biyayya AYSHA ko kya rabauta duniya da lahira.” Daga haka ta yanke kiran ina ta fa’din Hello Hello Mami na, amma ban ji ta ba. Hakan yasa na sauke wayar daga kunnena cikin mutuwar jiki da ta zuciya wasu hawaye masu zafin gaske suka shiga zubo min. Wa zan yiwa soyayyar? Wa zan nunawa kulawar? Wa zan wa biyayyar? Wata zuciyar ta amsa min da MAMUDA MAI KATON CIKI. Sai kawai na lumshe ido na ina sake hasasho shi a cikin duhun idona hankalina y’a sake tashi, gani nake ko da wasa ma ba zan iya d’aukar nauyin wannan mutumin ba. Anty Khadi na tsaye tana kallona Har ta gaji ta mik’a min kwalaccar haka kawai sai naji k’arfin zuciya yazo min don zuciyar ce ta bani shawarar na je gidan Mamudan Amma zallar rashin kirki da zan dinga nuna masa sai ya gaji ya sake ni, kuma ba zan tab’a yarda ya kusanceni ba, sai me don an k’irga min aure ai ba kaina farau ba.

Haka na shirya sai dai ban saka komai a fuskata ba. Laffayar ma da take ta zuba wani cool k’amshi Anty Khadija ce ta na’da min. Ta ja hannuna muka fita parlorn gidan inda sauran y’an matan Abba da za’a kai
Gidajensu suke. Kallonsu
Kawai nake d’aya bayan d’aya don zuciyata ma ta bushe na kasa kukan sai wani irin tafasa take hakan yasa nake fesar da huci a kai a kai. Hucin da yake bayyana Har a k’ofofin hanci na.

Dangin Ustaz ne suka fara zuwa suka tafi da Humaira. Ta zo rungumeni na janye jikina ina jin haushin ta da tsanarta sosai a raina. Ina kallo sauran ma duk aka fice da su. Gidan ya yi tsit daga ni sai Umma sai Aunty Khadii da take zaune a gefena tana sake kwantar min da hankali. Ni dai ido kawai na
Lumshe daidai lokacin Abba ya shigo shima ya k’araci nasiharsa ban bu’de idon ba. A k’arshe ya ce “Allah ya baki ikon sauke nauyin da Allah ya d’ora Miki.” A raina na ce “K’warai kuwa nauyi, ko da kanku kun san ni y’ar fucilata da ni wannan mutumin ya min nauyi, ba mamaki daga ranar da yazo karb’ar hakkinsa ya ragargaza ni na Mutu kowa ma ya huta. Na tuno first night d’in mu da Ustaz yarda na ci bak’ar azaba ina ga wannan mai randar cikin ga jajayen ido fici fici daga ganinsa ka ga jarababben mutum. Abba da kansa ya ja hannuna zuwa waje wajen Mamuda da aka ce ya zo. Haka na zama tamkar rak’umi da akala na kasa wani motsi zuciyata ta soye idanu na fes nake kallon mutane. Ban damu da barin gidan ba don su kansu mutanen gidan na saka musu alamar tambaya a kan su da k’yar idan sun damu da farin ciki na.

Suna gaban motar shi da wancan abokin nasa ni kuma ina bayan Mota ni da Yaya Usman da yake ta faman aikin lallashi na. Sai dai ko gezau kallonsa kawai nake. Mamuda mai tulun na ji ya ce “Ka rabu da ita Usman, nan da gobe zaka ganta warai, ai ba a lallab’a bazawara tunda ta riga ta San da’din aure ita kanta na San yanzu a matse take mu ka’dai ce….” Abu na ji ya sake tokare ni a k’irji. Jin yarda yake kalamai kamar yazo daga k’auyen k’awai na yi shiru ina tunanin izaya iri iri da zan masa har sia ya gwammace bai San wata Aisha ba wallahi. Yaya Usman ya ja hannuna ya rik’e sanda za mu yi sallama a airport cikin wata irin murya ya ce “I mish you lil sis ne a good girl please AYSHA!” Sai a lokacin kuka yazo min na fa’da jikinsa ina sakin wani irin wahaltaccen kuka. Shima kukan yake kafin ta janye ni daga jikinsa Naga ya juya da sassarfa ya bar wajen da sauri. Na lumshe ido na, na yi kuma saurin goge hawayen don bana son Mai tulun ya ga lagona.

Muna hawa jirgin na nemi mai tulun na rasa don ni ban sani ba ko ya shigo ko bai shigo ba. Haka kawai sai na dinga jin wani irin feeling a raina. Ga zuciyata ta na wani irin bugu kamar zata fito daga k’irjina. Na dai daure na zauna a kujerar da take daf da ni. Bayan tsawon mintuna guda sai ga wani mutum yazo yana nuna min boarding pass d’insa ya ce “Am sorry Madame, Seat d’ina ne.” Ban yi magana ba na mik’e na isa inda na ga kamar nan ne nawa. Wani mutum ne cikin wasu irin k’ananan kaya masu masifar kyau. Kansa sanye da p.cap ya rufe fuskarta sa bayansa jingine da kujerar jirgin kamar mai barci. Na d’an bi shi da kallo kafin na tab’e baki na zauna. Sai zabga k’amshi yake kunnensa kuwa headphone ne a mak’ale. Zama na ke da wuya aka fara sanar da tashin jirgin. Hakan yasa gaba na y’a dinga fa’duwa musamman ganin yarda jirgin yake kamar gargada. Ina kallo kowa ya fara fastening seat belt d’insa amma ni hannu na ma rawa yake don rabo na da jirgi tun ina k’arama. Ji na yi mutumin ya zura hannunsa kawai don saka min belt d’in a masife na ture hannun nasa cikin bala’i na ce “Mahaukaci ne kai ko na ce maka ina da buk’ata?” Hannu ya saka ya d’auke p.cap d’in fuskarsa wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin Wanda nake zaune a kusa da shi……

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….59

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.
Chapter 40 · 0% Book details