← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 49

Sashe 39

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta d’an kalle ni tana furta “Ayshatun Mami ya aka yi ne? Akwai matsala?” Na d’aga kai kawai ina wasa da yatsu na na ce “Ina son magana da ke Umma.” Umma ta d’an dubeni tana duban d’akin kuma sai ta ce “Yi maganar ki mana, ai ba kowa ni da y’ar uwarki ne kawai kuma bai kamata ace kina b’oye mata abinda ke ranki ba, duk duniya baki da makwafinta.” Na d’ago ina kallon Humaira da itama take kallona tana sakin murmushi a hankali. Sai kuma Naga ta mik’e ta yi pecking d’ina a kumatu ta ce “Feel free Sis ki gayawa Umma matsalarki she is ur mother baki da misalinta, bari na baku guri.” Bata jira cewar Umma ba ta fice da sauri. Na saki ajiyar zuciya ina kallon Umma da ta kafa min ido. “Ina jin Ki Shatun Mami, me ya faru?”
Na yi k’asa da kaina cikin rawar murya na ce “Mhmn, Umma dama maganar Ustaz ne na amince zan koma gidan sa a bar maganar aurensa da Humaira.” Wani irin kallo na ga Umma tana min bakinta a sake da alama mamaki ne fal a zuciyarta ta ce “AYSHA wace irin magana nake ji, Mara da’din ji haka? Me yasa kike son mayar damu k’ananan mutane? Da kanki fa kika ce ba kya sonsa sai yanzu da Har ya kawo lefen y’ar uwarki da saka ranar aurensa sai kuma ki ce shi kike so. To wannan maganar ta tsaya tsakanin ni da ke kawai bana son ko a zuciyarki ki sake maimaita ta. Ahmad shi ya dace da auren y’ar uwarki ko ba kya son ya zama silar gyaruwar dukkan laifikanta. Kada ki zama mai son kanki mana Ayshatu.” Ta dafa hannuna ta ce “Ki yi hak’uri kina gama idda ke ma zaki samu mijinki ki tuna ita zata yi wuyar samun miji musamman irin rayuwar da tayi a baya, tunda yanzu kuwa Allah yasa babban Malami irin Ahmad zai aureta ai sai mu godewa Allah ke kuwa na San zaki iya samun kwatankwacinsa ko Wanda ya fi shi In sha Allah, tunda ke baki da wani aibu…” Zufa ce kawai take fita daga jikina. Na dinga kallon Umma ina mamakin kalamanta. Anya kuwa Umma na so na? Ko dai Har soyayyar uwa ta tattara ta barwa Mami ni. Idona suka ka’da suka yi jajur ina jin yarda jijiyar kaina take harbawa da k’arfin gaske na runtse ido na ina ji Umma ta d’an rungumeni ta hau bubbuga kaya na. A hankali ta ce “Ki zama mai son y’ar uwarki fiye da kanki AYSHA, ke kin taso da gatanki ita kuwa fa? Kinga dole yanzu tana buk’atar kulawar mu da dukkan soyayyarmu.” Ban amsa mata ba. Kukan ma kuwa ya k’i zuwa sai zugin zuciya da tsananin b’acin rai. Na janye jikina na mik’e kawai ina harha’da hanya na bar d’akin. Kashe wayata na yi gaba d’aya na daina kula kowa a gidan kullum cikin shiru nake hakan kuma bai saka Sun fasa shirye shiryen biki ba. Wanda zai zama daidai lokacin da na gama Idda.

Ranar da naga period d’ina na k’arshe hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba. Don na San ni da Ustaz kuma sai gani sai hange daga nesa. Hakan ya tashi hankalina sai dai na tattara na mik’a lamari na ga Allah. Na tabbata tawa k’addarar ce haka. Mami na ma ban sake nemanta da zancen ba. A ranar da zan yi wankan tsarki na gama period kasa yin wankan na yi saboda matsananciyar fargaba da b’acin rai. Na yi wata irin rama da ko lokacin da abubuwan can suka faru ban yi ta ba. Fuskata baka ganin komai sai idanuwa. Na kasa samun nutsuwa Har sai da na danna kiran Mami na. Bugu guda kuwa ta d’auka tana furta “A’in Mami ya aka yi?” Na fashe ina gaya mata na gama idda yau. Shiru ta yi kafin ta saki ajiyar zuciya ta ce “Ustaz ya san kin gama ko zaki gama a yau?” Cikin kasala da mutuwar jiki na ce “Na san ya sani don kwanakin period d’ina a kansa suke kamar yarda duk zan fara period shi yake gaya min yau Madam fa sai a hankali bak’o zai zo.” Mami ta yi shiru kafin ta ce “AYSHA, yanzu ba abinda ya rage mana sai ki fito musu ta yarda suke so, da zarar sun Miki maganar fito da miji ki ce kawai kin bawa Abbanki wuk’a da nama na San zai gane kina son komawa auren Mijinki ne, shikkenan sai ki a mayar da aurenku.” Na saki ajiyar zuciya ina jin shawarar Mami accepted har cikin rai na.

Da sassafe kuwa da kaina na shiryawa Abba favorit food d’insa Masa da miyar taushe. Duk ba na komai bane sai na cin hanci. Na dama masa kunun gya’da ha’dadden ba abinda yake sai k’anshin gya’dar gashi fari tas kamar yoghurt. Har a Sallahr walaha sai da na rok’i Allah yasa Abba ya amince da abinda zan je masa da shi. Ina kallo Su Humaira kallona kawai suke yi, sai dai ba su min magana ba don yanzu na zame musu horror komai suka yi masifa nake musu. Da kaina na kinkimi kwandon Abincin Abba na shiga da shi parlorn a raina ina furta “Yairinya kwalelenki, mijina yafi k’arfinki ko ta halin k’ak’a sai na k’wato abu na.”

Har k’asa na kai na gaida Abba da yake ta kallo na yana furta “Yau A’in Mami ta tuna da Abbanta kenan, Har gashi an min delicious.”
Na yi k’asa da kaina ina murmushi ganin fuskar Abban fal nisha’di da alama hak’ata zata cimma ruwa. Abba ya ce “Ko an samo min surikin ne? K’in ga shikkenan sai a ha’da da na y’an uwanki don na San yanzu dai k’in gama idda.” Na girgiza kai na ina murmushi na ce “dama akan maganar na zo Abba.” Ya gyara zama yana furta “Alhamdulilah, addu’a ta ta amsu kenan, yaushe suka ce zasu turo?”
Idona ya kawo ruwa sosai kafin na d’an girgiza kaina cikin k’arfin hali na ce “Abba, na baka zab’i ka zab’a min duk Wanda ya maka ni kuma zan aure shi.” Abba ya saki murmushin jin da’di ya ce “Kin tabbata AYSHA? Ko wa na baki zaki amince ki aure shi?” Na d’aga kai da sauri. Sai na ji ya ce “Alhamdulillah da y’a ta gari, ina alfahari da zamowar ayshatu cikin zuri’ata, Allah ya Miki albarka ki shirya yau da daddare zaki yi bak’o.” Duka k’irji na yake yi sosai na mik’e a kasalance na mik’e na fita. Sam ba haka na so na ji Abba ya ce ba, so na yi ya ce shikkenan AYSHA za’a mayar Miki da aurenki da mijinki. Duk da haka nan cire rai ba, ban sani ba ko akwai wani suprise da Abba yake min, may be da daddaren Ustazu na zan gani a zuwan Wanda ya zab’a min. Don haka har dare na kasa samun nutsuwa duk da haka na fece kwalliya sai zabga k’amshi nake sabuwar atamfa na saka mai masifar kyau na yafa babban mayafi da niyyar ina shiga wajen Ahmad zan cire mayafin tunda Naga yanzu hankalinsa na kan wayayyun mata. Kaina dama ko d’ankwali babu gashi na ne na gyara shi sosai ya kwanta abaya na.

Ai kuwa Maryam na zuwa ta ce min ina da bak’o na mik’e. Kitchen na shiga na d’au tray d’in da na ha’da masa delicious a ciki. Na saka kai na a parlorn. Zuciyata ta yi wani irin bugawa ganin Wanda yake zaune ban san sanda na saki tray d’in ba, kayan ciki suka tarwatse a k’asa gaba d’aya…..

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….60.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Don haka bana so na sake Jin kin furta kina son Ahmad, balle wani ya ji a yi da mu. Ki rungumi Mijinki ki so shi, sai ki ga watarana kin yi alfahari da aurensa balle yana son ki kuma shima yana da rufin asiri fiye da Ahmad ma.” Wasu hawaye kawai na ji Sun ziraro min na kasa furta kalmar komai sai ajiyar zuciya nake saki. Umma ta ce “Ke ai gaba ta kai ki, irin wa’dannan mutanen da suke ninka ka a shekaru Sun fi iya lallab’a mace da nuna mata tattali, don Allah Ausha ki so Abin ki ki bashi dukkan kulawa…” zaro ido nake kawai, ina tunanin ta ina zan fara son wannan abin? Ta ina zan bashi kulawar? Da wani rungumemen cikin za’a sha soyayyar. Ni AYSHA mai mafarkin auren Miji d’an gayu sai na b’ige a Mamuda mai tumbin ku’di. Na San su Asma zasu sha dariya don na sha alwashin ba zan auri mummunan mutum ba ko mai ku’dinsa kuwa gara na auri kyakykyawan da bashi da ko sisi. Umma bata sake bi ta kaina ba ta dai dafa kaina ta d’an shafa alamar rarrashi ta fice daga d’akin. Ni kuwa bin bayanta na yi da kallo ina tunanin yarda Umma ta zamo uwa a gareni Amma bata damu da ni ba, bata son farin ciki na. Ban sani ba ko sanda ta bawa Mami ne Har duk wani so da tausayi irin na uwa da take min ta tattara ta barwa Mami. Za’a sha drama don ba zan yarda da auren Mamuda ba.

Haka aka shiga gudanar da shagulgulan biki, ni dai nawa ido don bani da wata mafita kuma banda Allah. Har Anty Khadija da take fama da jeho bata zauna ba a bikin nan sai kai da komowa take tun tana bani hak’uri Har itama ta gaji ta tattara ta zuba min ido. Gyaran jiki kuwa haka na hak’ura ina ji ina gani aka gurji jiki na. Bana fita ko ina abinci ya zama bak’ona ruwan shayi kawai nake sha shima sai na runtse ido. Yaya Usman tun yana bani hak’uri har ya tattara ni y’a watsar. Y’an matan Umma kam an sha kyau na ban mamaki ina kallo aka kawo lefen Humaira daga gidan su Ustaz akwati na sha biyu.
Chapter 39 · 0% Book details