← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki tashi mu tafi na ce miki Aysha!” Ya.Usman ya fa’da cikin muryar da ke bayyana fushinsa. Girgiza kaina nayi na ce “Ya Usman ka bar shi ba zasu fahimceka ba suma a potiskum d’in, ka bar shi na yarda da k’addara zan Jure, zan auri Tanimu.” “Ba zaki jure ba AYSHA, hauka ake za ki auri Tanimu, ki tashi mu tafi na ce.” Hawaye ne suka zubo min na ce “Ya.Usman, Umma fa? Baka ganin ranta zai b’aci kuma zata yi fa’da.” Fuskarsa a tsuke sosai ya finciki hannuna da kansa ya zura min Hijabin ya ja hannuna muka fice da sauri. Motar gidan mu da Driver yake ja ita Yaya Usman ya tura ni a ciki. Ya tayar da ita da sauri muka bar gidan cikin wani irin mugun speed. Ni dai lumshe idona kawai na yi saboda sam raina babu da’di.

Har muka isa garin kuma magana jefi-jefi muke yi, duk da tafiya ce muka yi ta bata wasa ba. A cikin gidan kuwa Inna da fara’a ta tare mu, ta saka aka kawo mana abinci da ruwan sha da zob’o masu sanyi. Kasancewar daga ni har Yaya Usman ba mu karya ba hakan yasa muka ci abincin sosai. Da alamu Inna ta fahimci rashin nutsuwa a tattare da mu, don haka bata mana magana ba har sai da muka ci abincin muka yi sallah kuma. Sannan ta ja ajiyar zuciya tana kallon Yaya Usman ta ce “D’an fodiyo tafiyar lafiya kuwa kuka yi na gan ku ficikai ficikai. Ba nutsuwa sam a tare da ku.” Yaya Usman, ya kalleta ransa a b’ace ya furta “Ba lafiya ba Inna, haka kawai k’alau kin san ba zan yi yo wannan doguwar tafiyar ba.” Ta girgiza kai ta ce “k’warai kuwa, da dai Muhammadu ne shine bawan Allah mai son zumunci, sai ka gaya min me yake tafe da kai?” Ya sake tsuke fuska ya ce “Yanzu Inna abinda ake wa AYSHA ya dace akan laifin da ba a tabbatar ta aikata ba, kada fa nan gaba a zo ana jin kunyar yarinyar nan..” Inna ta ‘dago kai tana kallonsa “Duk na yi wannan tunanin bayan dawowata Usmanu, kuma ina shirin na koma a wannan satin na ce a je can gidan su Fatiman. Rok’eta Allah da annabi a ji da gaske yarinyar nan ta san tana aikata ba’dala kamar yarda Kakanku ya ce min, sai kuma ga ku kun zo yanzu me ya faru kuma?” Usman ya ce “Wai aure Abba zai mata, auren ma na son k’ask’anta ta wai da Tanimu Driver…” Inna ta ce “Cabd’i jam! To lamarin Imamu kuma sai du’ai, ta ina wannan abin yazo masa fisabilillah kamar muna garin mahaukata, to ba da ni zaa yi haka ba tozarcin Ai ya yi yawa. Zata yi aure dai amma ba da Tanimu ba da kai na zan samar mata Mijin aure dama can abin yana raina, na ce ko da yaron nan, Alhaji da kansa ma ya yi sha’awar hakan da Miftahu za’a ha’data aure Jikan Mariya k’anwata yana da halinsa kuma zai iya rik’eta In sha Allah, na san zai rufa mana asiri..” Yaya Usman ya saki ajiyar zuciya yana furta “Wannan kuwa, In dai Muftahu ne ai sam ba shi da aibu, Allah ya tabbatar mana da alheri, amma don baki ga gallaza war da ake mata a gidna can ba kamar wacce ta yi kisan kai.” Inna ta tsuke fuska ta ce “Kayya, amma Kubra akwai ragowar Imani kuwa a tattare da ita? Sai ka ce ba ita ta haifi y’ar ba, ai shikkenan sai ta yi zamanta anan har lokacin aurenta ta yi aurenta su tafi can lagos da Miftahun.” Yaya Usman ya kalleni sai na sakar masa murmushi don har a zuciyata na amince da auren Miftahun, don ba laifi kyakykyawa ne Fulani Usuli kuma d’an gayu ne ya yi bokonsa daidai gwargwado. Shigowar Alhaji kakanmu ce tasa aka yi shiru a d’akin. Da mamaki yake kallo na ya ce “Tsohuwa ke ce yau a gidan?” Murmushi na saki ina gaishe shi ya yi dariya ya furta “Shikkenan amaryata ta zo bari a bu’de miki naki d’akin ki shiga..” Jan mu ya dinga yi da wasa har na mance kaso hamsin na b’acin raina sai b’abbaka dariya nake. Tsaf Inna ta gaya masa duk abinda yake tafe da mu. Sai naga ya yi dariya ya ce “Imamu kenan, wato masifaffiyar zuciyarsa tun ta yarinta har yanzu yana nan yana fama da ita, ban da abinsa wa yake tsallake k’addararsa idan ma ta aikata d’in ta dawo ta tuba Ai sai a yafe mata, Allah Ai gafururrahimu ne. Dama ko baku zo ba ni na yi niyyar kiran Imamun na gaya masa a k’arshen watan nan za’a d’aura mata aure da Miftahu jikan Mariya, tunda kuwa kun zo sai ka barta anan su fahimci juna da Miftahun kai koma.” Usman ya mik’e yana duban agogo ya ce “Ai yanzu ma zan juya, don baa san mun taho ba.” Suka yi sallama nima na raka shi har mota ina jin kamar na yi hawaye don tafiyar da zai yi. Ya girgiza min kai murya a hankali ya ce Be a good girl AYSHA, In sha Allah k’arshen matsalarki ne.” Na lumshe idona ina cije leb’ena ka’dan na d’aga masa kai ya saka hannu ya share min hawaye na sannan ya dank’a min ku’di masu d’an yawa a hannuna ya shiga mota yana d’aga min hannu. Jikina a salub’e na koma gidan. Sai dai yarda Alhaji ya tasa ni a gaba da hira da abubuwan ban dariya yasa na wartsake na shiga amsa masa.

Ina wajen Alhaji ya kira Abba ya fara yi masa fa’din kan hukuncin da yaso yankewa ba tare da neman shawara ba. Abba dai shiru ya yi sai da Alhajin ya gama fa’da sannan ya ce “ka yi hak’uri Alhaji, hankalina ne duk a tashe game da lamarin yarinyar nan ta kai har bana son shiga taro…” “To sai me shi d’an Adam Ai dama haka yake, ba ya raina abin fa’da don haka maganar wani Drivern ka na janyeta, na soketa daga yau yaron nan Miftahu zata aura…” wata ajiyar zuciya na ji Abba ya sauke wadda kana jin sautin fitarta har ta cikin wayar. Ya ce “Alhamdulillah, Allah yasa Midtahun ya amince..” Alhaji ya ce “MIFTAHU yaro ne mai biyayya na san ba zai ja da umarni na ba.” Suka yi sallama. Sai sannan na mik’e na fita tsakargida don taya Inna aiki.

Da daddare a kan gadon Kakata na kwanta, cikin matuk’ar kwanciyar hankali da samun sukunin zuciya. Murna ta cika ni ganin na fita daga k’angin bauta zuwa y’anci da nake fatan ya ‘dore har gaban abada. Kamar an ce na kai Sunnah T.V na danna remote na kai, abin mamaki kawai sai ga fuskar Ustaz ta cika allon television d’in, fuskarsa da ‘dan murmushi ka’dan yana kallon wanda yake karanto masa tambayoyi yana amsawa kamar yarda ya saba a duk sanda ya gabatar da karatun da yake gabatarwa duk juma’a da lahadi. Cak lumfashi na yaso d’aukewa sai dai na yi jarumta k’warai da gaske wajen ganin ban rasa nutsuwata ba. Hannu na saka zan kashe t.vn sai na ji mai tambayar ya ce “Ustaz Ahmad ita wannan tambayarta guda ce, wai me yasa ka saki matarka a daren da ta tare a gidanka?” Shiru Ustaz d’in ya yi yana murza goshinsa da d’an yatsan hannunsa kafin ya furta “K’addara.” Ya kuma lumshe idon bai sake magana ba. Da sauri na danna remote na kashe Tvn zuciyata na wani irin tunzira da wani irin b’acin rai. Na lumshe nawa idon ina jin kwararar hawaye a saman fuskata. Har cikin dare na kasa barci saboda k’unar da zuciyata take ciki ba zai bari na samu na yi barcin ba. Shi yasa da na Yi sallahr asuba Inna ta ce koma ki kwanta ki dai ina jin ki ba wani barcin kirki kika yi ba, wato ba zaki bar sakawa kanki damuwa ba ko?” Shiru na yi don bani da amsar da zan bata. Dole na koma barci don idona har yaji yake. Da safe na diga jiyo hayanyia daga parlorn Inna sama sama. Da sauri na mik’e don sai na ji kamar fa’da ake. Na d’an d’aga labulai d’akin sai na ga Gwaggo Mariya ce k’anwar Inna take ta masifa idonta a rufe. “Wallahi ba zai yiyu ba Yaya, ta yaya sai da yarinya ta gama watsewarta za’a ce Miftahu ya aureta me yasa sanda take da mutuncin ba a bashi aurenta ba sai yanzu to gaskiya da sake ba dai Miftahu ba… ina shi ina auren Karuwa fisabilillah Miftahun da kowa ya shaida da nagartar halayensa…” D’if parlorn ya yi ana saurarar tijarar gwaggo Mariya da ko kunyar furta wasu maganganun bata ji. Ni dai ji na yi kai na yana wani irin sarawa ga duhu ina gani ga wata irin hajijiya ni dai daga nan ban sake sanin me ya faru ba sai gani na yi a kwance a gadon asibiti. Inna a zaune kusa da ni sai Alhaji shi kuma yana zaune kan kujera duka fuskokinsu ba sukuni don Inna ma kamar kuka take.. ido na na sake lumshewa don bana son su fahimci na farka ina ji Alhaji ya ce “Yanzu ba zaki shiru da kukan nan ba…” cikin shashshek’a ta fara magana “Bar ni Alhaji, bari na yi kukan nan ko zan samu zuciyata ta yi sanyi, Mariya fa! Mariya tawa ita take gudun ha’da jini da ni saboda wata k’addara ta samu jinina ashe Mariya ba mai iya rufa min asiri ba ce? Jikanta take cewa ba zai auri Jikata ba wani irin Zamani muke ciki?” “Irin wanda Manzon Allah ya bamu labarin zai zo, don haka ki saka a ranki ba lallai yarda zuciyar ki take ba ta kowa ta zama haka fak’at! A yi addu’ar Allah ya kawo mata Miji na gari kawai.” Zuciyata ce take wani matsanancin bugu wai ni yau Ayshah ni ake talla da ni ana k’in aure na? Wace irin k’addara ce wannan tabbas jarrabawar nan zata min wuyar answer don ina jin karaya tun daga zuciyata har gab’ban jikina….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 29.
Chapter 7 · 0% Book details