← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 49

Sashe 32

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Banda ba barci nake ba, da sai na ce mafarki na yi da mai kama da ni kwabo da kwabo. Exactly kamar ni ce a tsaye, sai dai banbancin yanayin gogewa da wayewar idonta. Don kana ganinta zaka san wayayyiya ce… na runtse ido na sake bu’dewa don na tabbatar da abinda na gani. Amma still idanuwa na suka sake sauka a kanta itama kallona take yi bata ko k’iftawa. D’an sandan da ke tsaye ne ya dawo da ni cikin hayyacina jin maganar da yake yiwa Alk’ali. “Hak’ik’a an yi kuskuren kama wannan baiwar Allahr, a aikin da wannan mai kama da itan ta aikata. Ba ita ba ce sai dai kamannin da suke da juna da akewa lak’abi da kwabo da kwabo yasa ake ganin kamar ita ta aikata. A yau Allah ya bayyana tsatsan ikonsa na kuma jinjina girma da k’udirar Allah mai yin halitta ya kuma sake maimaita irinta ba tare da kuskure ko guda ba. A yau muka yi dacen kama su a cameroun zasu hau jirgi su tafi south africa. Yallab’ai ita wannan itace Ainahin Aysha SHANY da ake nema ba wannan Ayshar ba.” Ba ni ka’dai abin ya bawa Al’ajabi ba, Har ma ya sanya zuciyata cikin ru’dani. Na lura hatta da mutanen wajen hakan ce a garesu ta yarda suka bu’de baki suna kallonmu. Ina kallon yarda Umma take Zare ido kamar yarda Mammy da Abba ma suka shiga shock. Ita kuwa Aysha sai nuna ni take da yatsa sai dai ta kasa furta komai. Fuskarta ce dai d’auke da tsananin mamakin da ya kasa b’uya a idonta. Sai k’ikkifta kyawawan idonta take.

Mai shari’a dai tsabar ru’dani ajiye biron ya yi, yana jijjiga kansa ya ce “Hukumullahi laaa ajaban.. wannan lamari to ya abin yake ne?” Bayan tsawon mintoci da samun hayaniya a parlorn. Alk’ali ya mayar da glass d’insa ya kuma dakatar da hayaniyar ta hanyar amfani da guduma ya buga table d’in da ke gabansa… nan take kowa ya nutsu aka kuma kasa kunne don cigaba da sauraran shari’ar. Kowa ba son jin yanke hukunci yake ba, so yake yaji ya aka yi aka samu wannan matsananciyar kamar da muke da juna. A idanunsu na gano hakan. Ni dai ina tsaye sai mayar da ajiyar zuciya nake ina sake ware idona ina kallon SHANY da take tsaye tana ta fisgar leb’enta da alama yanayin ya zame mata jiki. Idanunta kuwa kamar ma a buge take tsabar yarda suke lumshewa da kansu. Maganar da Alk’ali ya yi ne yasa na d’auke hankalina a kanta na gyara tsayuwata ina sauraran abinda ya ce. “Baiwar Allah ko bayin Allah, da gaske ne ku kuka yiwa Minuster D’an Audu sata bayan kun same shi a hotel kun shak’a masa abin Maye kuka yi amfani da wannan damar ku ka d’au hotonsa kuka ya’da a social media kuna nuna tsiraicinsa… ko da yake kafin nan zan so sanin sunayenku da na iyayenku garin da kuka fito da komai ma ina son sani…” Ya fa’da yana duban su. Gaba d’aya suka shiga kallon juna d’aya bayan d’ayansu suka shiga nuna mai kama da ni. Da alama itace shugabarsu ita kuma zata wakilcesu. Ba tare da shakkar komai ba ta gyara tsayuwarta tana cigaba da juya idonta exactly irin na y’an Maye ta ce “Sunana SHANY, haka na taso na ji ana kira na a gidan da na rayu. Na ji ana kirana da SHANY. Aisha shine cikakken sunana. Sunan Uba ko wakili kuwa ba ni da ko d’aya, ban kuma San su ba….”

Gaba d’aya naga y’an gidanmu Sun zaro ido. Musamman Umma da Abba. Mami kuwa k’asa Naga ta yi da kanta. Shi kuwa Ustaz Ware idonsa ya yi sosai sai ya kalleni sai ya kalleta. A raina na dinga nanata sunanta wato itace wacce aka zata ni ce a jikin wancan hoton na farko Har Ustaz y’a sake ni saboda shi…

Cikin fuskar mamaki Alk’ali y’a zuba mata ido kafin ya furta ban gane baki san iyayenki ba? Shi mahaifin naki mutuwa ya yi ko kuwa sallmaki ya yi kika shiga rayuwar bariki?” Muryar ta a shak’e ta furzar da huci ta ce “Na ce maka ban san su ba. Hakan yana nuni da amsar kai tsaye bani da su.” Alk’ali ya girgiza kai ya ce “Mahaifiya fa?” Sai naga ta saki malalacin murmushi tana juya kai ta furta “Babu! Ni y’ar tsintuwa ce, kamar yarda wad’annan da kake gani suma duk y’an tsintuwar ne, kai gaba d’aya k’ungiyarmu ma y’an tsintuwar ne mun tashi a k’ark’ashin kulawar wata mata…” Ido kawai naga an zuba mata nima
Kallonta nake cikin matsanancin mamaki. Alk’ali ya ce “Ikon Allah! Ita matar kuma bata San iyayenku ba take rainonku?” Ina kallo SHANY ta d’an yamutsa baki kafin ta girgiza kai da alama ta gaji da question d’in Alk’alin.

“Shegu ne mu, haka uwar gijiyar mu Atine harka take gaya mana bamu da wasu dangi bayan ita, ita ta rainemu ta kula da mu har muka kawo yanzu bayan iyayenmu Sun cillar da mu….” Alk’ali ya yi rubutunsa kafin ya d’ago ya zuba mata ido ya ce “Ina son sanin tarihinki…”

Ta sake turo bakinta cikin yanayin tsiwa ta ce “Atine y’ar harka shine sunan wacce take kula da mu tun da muka tashi ita muke gani ita kuma muka sani. Tun muna yara tare muka taso da wa’dannan, su na sani a matsayin y’an uwana. Sune dama sa’annina a gidan Babu wani mai cikkaken asali a cikin
Mu. Takurawar da Uwar rik’onmu take mana yasa muka tashi da k’untutaccuyar zuciya mai zafin gaske da k’unci. Wahalar da mu take tamkar bayi. K’alilan daga cikinmu take warewa ta saka a makarantar boko Wanda kyansu ya kai kyau, hakan yasa ta saka ni a makarantar nima don ta sha fa’da ni jarinta ce, kuma wacce ta bata amanar kula da ni a kullum tana jik’ata da naira.

Na yi makarantar private school tun daga nursery Har Secondary school, yanzu ma Ina jami’a. Tana bani abinci mai kyau sutura mai kyau ba don komai ba sai don na yaudari k’usoshin gwamnati hakan yasa bata gajiya da siya mana sutturu masu alfarma da supplement na gyaran jiki.

Yaudarar maza muke ta hanyar nuna shigar banza don tun yarinya tana shekaru sha hu’du dama zata fara koya mata duk wata hanya da ta San zata mallaki namiji da dukiyarsa. A duk inda masu ku’di suke muna zuwa mu zak’ulosu mu kuma yaudaresu bayan sun saki jiki da mu sai mu saka musu abin Maye a abin sha mu yashe dukiyarsu mu d’auki hoton tsiraicinsu mu ce da zarar sun fa’da sai mun ya’da a social media. Har zuwa yanzu da muka yaudari Minister d’an Audu!” Daga haka ta ja d’an mitsilin bakinta ta tsuke tana cigaba da ka’da jikinta. Da alama sam ba abinda yake damunta balle ta shiga cikin fargaba sai far far take da idonta da ya sha eyeliner.

Alk’ali ya jinjina kai yana sake kallonta ya ce “Yanzu ina uwar d’akin taku take?” D’an rausayar da kanta ta yi kafin ta furta ta ce “Tana Abuja ta ce kada ma mu nuna min santa mu je mu yi ta kanmu, wannan ne dalilin da yasa na d’au alwashin sai na tona mata asiri… ta ce d’an Audu bai da mutunci da dai wani ne tana da hanyar fito da mu.” Alk’ali ya sake jinjina kai ya ce “Ikon Allah! To ina kuke kai ku’dad’en da kuke yin fashi? Ko damfara zan ce?” Alk’ali ya jinjina kai ya ce “Ku bada address d’in inda za’a sameta. Kafin nan zaku zauna a hannun hukuma Har zuwa lokacin da zata zo mu tabbatar da abinda kuka gaya mana gaskiya ne…. Da wannan nake cewa Kotu ta wanke Aisha daga zargin da ake mata… muna kuma rok’on ta yiwa jama’a afuwa akan kuskuren da aka samu… Za’a dawo shar’ai sha bakwai ga watan nan da muke ciki… daga haka ya buga gudumar kotu d’aukacin jama’ar da suke wajen suka furta “Kotuuuuuuu!” Wanda ya yi daidai da isowar duka zuri’ar gidanmu wajen har Ustaz da bakinsa ya kasa rufuwa. Na dinga kallonsu da wani irin yanayi da ni kaina na kasa tabbatar da abinda nake ji. Haushinsu da haushin rashin yarda da ni da suka yi ya nanna’de duk farin ciki na. Na dinga jin wani irin zafi a zuciyata. Idona ya sauka kan Mami da take zaune kanta a k’asa na lura tun d’azun bayan bayyanar SHANY a yanayin da take ciki kenan…..

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….49.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.
Chapter 32 · 0% Book details