← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 49

Sashe 33

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yaya Usman yana dariya ya bar wajen. Ni kuwa harara na bi bayansa da ita ina kiciniyar k’wace kaina da ga wajen Ustaz da ya manna ni da jikinsa kamar zai mayar da mu Abu guda. Idanunsa a lumshe suke sosai yana k’ok’arin aika sak’on da yake so ya aika ta hanyar manna min zazzafan kiss da na ji shi har tsakiyar kwanya ta. Cikin kunnena ya min magana. “Ki shiga ki musu sallama mu tafi gida K’alb, jikina na wani irin missing d’inki.” Na yi k’arfin halin tureshi daga jikina ina sakin tsaki na ce “Wallahi ba zan koma gidanka ba Ustaz ko me zai faru sai dai ya faru….” Murmushi ya saki ya ce “Ko? Ki ce Ashe Abba zai shirya samar mana d’aki a nan shikkenan Nima sai na dawo nan, kin ga ko aiki ba zaki dinga yi ba sai dai mu wuni muna raya sunna…” na zuba masa harara na ce “Ka d’auka wasa nake? To bari ka ji na maka ta yara billahillazee na gama aurenka… Allah ya kiyaye na zauna da mai mata, ka je can ka jagwalgwalata Nima kazo ka jagwalgwalani na bar maka Hameeda Amma ni wallahi a yanzu dai kam saurayi gal nake so…” Shiru ya yi yana kallo na. Kafin Naga idonsa ya ka’da ya yi jajur ya janyo ni jikinsa muka tsaya daf da juna da sauri na runtse idona don ba zan juri ha’da ido da shi ba, don idon nasa a rikice suke. Cikin dasashshiyar murya ya ce “Open your Eyes and look at me… ki fa’da min ba kya so na Mara kunya…” Ya fa’da yana zagaye fuskata da yatsun hannunsa “Oya talk mana, madam parrot.” Da sauri na runtse idona jin yarda ya zura harshensa a kunnena bayan ya saka hannunsa cikin rigata. Na ji ya saki wata ajiyar zuciya da ta saka ni Jin kamar na saki fitsari. Tsawon lokaci ina jikinsa na kasa Zare jikin nawa sai can na ji ya sake ni ya kwanta flat a saman gado idonsa a lumshe.. “Ke da kanki kin yi missing d’ina amma kafiya da taurin kai sun hana ki ki gane, sai yaushe zaki daina wahalar min da zuciya ne?” Ya fa’da yana zagaye ni da kasalallen idon sa da suka jirkita zuwa wani launi da duk Wanda ya ganshi zai gane. Na mik’e tsaye cike da tsiwa da masifa na ce “Sai sanda ka sakeni. Malam idan sonka zai kasheni sai fa ka sake ni, idan ma ina son naka kenan.” Daga haka na juya da sauri na fice daga d’akin haushina guda yanda k’amshin mayataccen turarensa ya mak’ale a kaya na. Gashi ba dama na canja Kayan da Zarar na canja kowa zai yiwa abin mummunar fahimta. Tilas na zauna da Kayan da duk inda na motsa sai naji k’amshin turaren da yake jefe ni a wani yanayi. Ina son Ustaz son da ya sabbaba min zafin kishinsa nake jin Sam ba zan iya ha’da shi da wata ba. Ga zafin mahaifiyarsa da nake ji a raina don haka dole zan hak’ura na bar mata d’anta.

Da daddare…..

Kamar kowane lokaci da aka Saba a lokutan baya UMMA ta shirya abinci. Abin haushi sai ga Ustaz ya zo don Naci a Daren ma. Kyan da ya yi yau har ya zarce misali. Sam bai ji kunya ba ya zauna a cikinmu duk inda na yi kuma idanunsa suna zube a kaina. Cin abincin ake ba mai magana sai dai ni da Ustaz da y’a taku rawa na lura shima ba abincin yake ci ba. Sai da aka gama sannan Abba ya yi godiya ga Allah ya yi addu’a mai tsawo sannan ya dubi UMMA ya ce “Ina tsammanin wani al’amari game da yarinyar nan mai kama da Aysha. Ina hasashen ko daga tsatsanmu take musamman masu kamar A’isha a dangin nan suna da yawa kasancewar da Mahaifiyar Alhaji suke kama don haka na ce lawyoyi su tsaurara bincike har sai an gano marik’iyarta da yarda aka yi ta tsinceta saboda kamannin Sun yi yawa. Banda a gaba na aka fito da ita lokacin da kika haifeta tabbas da na ce y’an biyu kika haifa.” Umma ta ja ajiyar zuciya ta ce “Ashe ba ni ka’dai abin nan ya tsayawa a rai ba, kamaninn ga sun b’aci kamar irin y’an biyun nan da ake kira Identical twins fa Wanda ba’a gane su sai da shaida. Amma kuma ai ba Wanda ya tab’a rasa y’arsa a dangin nan… Abba ya ja ajiyar numfashi ya ce “Gaskiya, ba Wanda ya tab’a rasa y’arsa a kaf danginmu daga na nan jihar har ba potiskum, Amma ina Jin lamarin yarinyar nan a zuciyata kamar jini na, kuma na tausaya mata da ita da y’an uwanta da aka raina cikin irin wannan bak’ar rayuwar, koda an bincike ba a dangi take ba, ni zan d’auketa da sauran y’an uwan nata da ba’a samu danginsu ba In sha Allah.” Umma ta ce “Gaskiya hakan ya kamata ka yi, Ubangiji Allah ya tayaka rik’o, Allah yasa ma tana d’aya daga cikin ahalin wannan zuri’a tamu.” Sam zancen su bai wani burgeni ba a zuciyata haushi ma na ji saboda me za’a d’au mutanen da suka yi silar afkawa ta cikin bala’i? Na dai bi su da ido kawai. A ranar kam k’emadagas na k’i na je wajen Ustaz duk da lallab’a ni da suka dinga yi na yi burus da su na shige d’aki, Abba ya ce a k’yale ni na huta.

KASHGARI…..

Tun da na tashi da safe, na ji zuciyata ba abinda take so irin na ga Mami na. Hakan yasa na shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar Abaya ta peach color mai masifar kyau. Ina fita parlor na zube a gaban UMMA ina rok’onta ta bar ni na je na ga Mami na. Shiru Umman ta yi kafin ta ja ajiyar zuciya ta ce “Ayshatu y’ar gidan Mami, ni ba zan hana ki zuwa ganin Maminki ba Amma na San ko kin je ma bai zama lallai ta saurareki ba.” Na marairaice fuska ina cewa “Ni dai UMMA ki bar ni na je.” Ta d’aga Kai “Ki je Aysha Amma kada ki da’de tun da mutane suna zuwa Miki murna.” Har na mik’e na ji UMMA ta tsayar da ni ta ce “Au, tsaya Aysha kin tambayi Ahmad ne ai ya zama dole ki gaya masa kafin ki fita, tunda da igiyar aurenki a Kansa.” Gaba d’aya na b’ata fuska ta na ce “Umma wane irin na tambayeshi kuma? Ni fa wallahi UMMA ba zan koma gidansa ba, don har yanzu ban manta abinda ya min ba, k’arshe shine har da aure ban sani ba, ni wallahi bana son zama da kishiya na je ina wani raba miji da ita…” Baki Umma ta saki tana kallo na kafin ta ce “Cab’di, ba shakka, kanki d’aya kuwa Aysha? Ba zaki raba miji da wata ba, to kin ci gidanku shin mu nawa kika bu’di ido kika gani a wajen Uban ki? Gwara ma ki sahhalaewa kanki tunda kika zo A Nigeria dama a wata k’asar ne sai na ce mafarkin ki zai zama zahiri… shin menene ma laifin Ahmad da zaki ce ba zaki koma gidansa ba?” Rau rau na yi da idona na ce “Umma baki ji fa irin maganganun da yake gaya min ba, duk Akan laifin da ba nawa ba, sai da yaga ba haka bane sannan yake son kare kansa, ga mahaifiyarsa ba irin tsanar da bata nuna min ba. Allah ya kiyaye na koma wani gidan Ustaz…” Umma kallona kawai take cikin matsanancin mamaki ta ce “Duk na ji, ai mu ma iyayenki mun miki laifin me yasa kika yafe mana?” Na girgiza Kai na ina fincikar leb’ena na ce “Ku daban, shi daban, bari na yi sauri na tafi.” Ban jira UMMA ba na fice da sauri ko driver ban tsaya jira ba na tafi Titi da kaina Neman adaidaita sahu.

Tunda na shiga gidan Mama take jifana da kallon banza, ko amsa gaisuwata ba tayi ba, ta hau ni da fa’da cikin b’acin rai. “Aysha Fateema ba uwarki ba ce, ku barta ta huta tunda gaskiya ta riga ta bayyana bana son na sake ganin sillan k’afafunki a cikin gidan nan kin ji na gaya Miki.” Turo mata baki na yi na ce “Da’dinta ba wajenki na zo ba, wajen Uwata na zo, kuma wallahi sai na ganta babu Wanda kuma y’a isa ya ce Mami ba uwata ba ce, don haka ki bar wani balok’ok’o kafin ki tada hawan jininki a banza…” na haye sama ina dariya ganin yarda ta zaburo a guje. Sai da na tabbatar na kai inda ba zata iya Cafka ta ba sannan na juya na mata gwalo na ce “Ki biyo ni mana, idan kina da k’afa gurguwar tsohuwa kawai.” Ina ji ta ce “Ba shakka! Za ki sakko ki same ni ne.”
Chapter 33 · 0% Book details