Sashe 10
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A yammacin ranar still ina kwance, Umma ta lek’o ta ce “Ke ki zo in ji Abbanki da y’an uwansa…” wani irin tsawa na ji kaina ya yi don ban san da me suka zo ba… Kai NI AYSHA NA GA RAYUWA INA KAN GANI MA….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔫𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: https://chat.whatsapp.com/EuW3Jn8UkDrJudA1ThiH23
Kina buqatar kayan kitchen Masu kyau da rahusa?
Kina buqatar inda zaki dinga samun kaya Masu quality?
Uwar gda Amarya Duk ku tawo 💃🏽
Quality shine takenmu 😻 Muna maraba da masu sayan daya ko sari 👯♂️ Muna tura kaya ko ina da yardar Allah cikin Aminci😻 muna zauna a garin Kano cikin kwaryar birni👯♂️ masu sayan kayanmu Mina godia👯♂️
NA GA RAYUWA…31.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033648387.
★★★
Ina ji Alhaji ya ce “Amma daga yau maganar Miftahu ta kau?” Inna ta ce “Ta kau mana, ba dole ta kau ba tinda kakarsa ta nuna bata so, sai a yi addu’ar Allah ya bata mafiyinsa, ita kuma tata jarrabawar kenan..”
Tsawon sati na yi a asibiti kafin a sallameni, saboda likitan ya CE dole a bani kulawa ta musamman don jini na ya hau ka’dan. Ranar da aka sallameni muka koma gida Inna ta dinga kula da ni sosai tana k’ok’arin Kawar min da b’acin ran da nake ciki. Hakan yasa na samu nutsuwa na yi wani fresh tas da ni ba abinda ke damuna sai d’an abinda baa rasa ba.
Sai dai wani abu da yasa na tsani zaman garin, sai aka fara yama’di’di da ni har da masu cewa cikin shege na yi a Kano shine aka dawo da ni nan. Abinka da k’aramin gari tuni labari ya kewaye lungu da sak’o aka fara shigowa kallo na. Inna kuwa ba dama ta fita sai a yi ta nunata wannan shi ya tashi hankalin mu da na Inna ta gayawa Alhaji Kano zata mayar da ni, don anan kam duk wanda yazo neman aurena ma gulmar da mutane zasu kai masa ba zai bar shi ya aure ni ba. Alhaji ya jinjina kai ya furta “Sharrin k’aramin gari kenan, mayar da ita d’in shine mafi alheri gaskiya, can birni ba lallai wani ya samu labari ba ma, nan kuwa madadin ta samu nutsuwa sai ta sake firgicewa, amma ki jawa Uwarta kunne ta san irin abinda zata saka ta, don wahalar da take bata ta yi yawa abu sai ka ce a gidan gyaran hali.” Sanda Inna ta gaya min zata mayar da ni Kano ban wani damu ba, don ni kai na zaman garin ya fara isata ba don komai ba sai don kallon da mutane suke min na matsayin Karuwa! Na ha’da y’an kayana na bawa mai aikin Innan don dama ba wasu kaya ne masu yawa ba. Kwana biyu tsakani kuwa muka taho Kano.
Inna ta saka Umma a gaba da nasiha akan ta sassauta min, wannan k’uncin da gallazawar ba shi zai gyara ni ba sai ma ya k’ara tab’arb’ara ni, ki nutsu Kubra ki ja y’arki a jiki ki san matsalolinta tun farko ke kika yi saken da kika nesanta kan ki da ita har ta fa’da wannan halin garin kawaicinki na banza da wofi…” Umma ta jijjiga kai murya can k’asa ta furta “In sha Allah Inna.” Shikkenan na samu sassauci har ma na dawo sashen Umman da kwana cikin d’aya d’akinta da bata amfani da shi sai sauke bak’i. Da farin ciki na gyara d’akin na kuma dawo da duk wasu tarkacena da suke sashen Mammy na. Sai ga shi ya fito tas. Daga ranar kuma Umman ta rage hantarata ko saka ni aikin mai wuya. Na so na koma Islamiyya sai dai ban san da wani ido zan kalli Malaman ba. Hakan yasa na hak’ura Umma take biya min karatu tunda ita tayi ilimin addini sosai. Fita ce dai ban isa na fita ko nan da waje ba, hakan yasa na sake wani shegen kyau fata ta tayi fresh sosai.
A cikin wannan yanayin aka fara shirye shiryen bikin su Ya.Usman shi da Ya.Umar. Bikin ya rage saura sati guda don haka gaba d’aya hankalin Umma ya koma kan bikin. Nima ina ta shiri na na bayar da d’inkuna na. Umma dai ba wani sake min fuska take ba duk da dai bata gallaza min. Kullum su Yaya Muhammad da matansu sai sun zo gidan jin tsare tsaren biki. Yau ma tun bayan magriba suka zo. in daga cikin d’aki na ji Muryar Anty Khadija tana cewa “Wai Umma AYSHA bata nan ne? Naga kullum idan muka zo ba ma ganinta. Na kuma lek’a d’akin tsakargidan nan ma bata nan.” Ina ji Umma ta yi shiru sai kuma na ji ta ce “Tana cikin d’aki, ni na hanata fitowa cikin mutane tunda dangi suna yawan zuwa bana son ta jawo raina ya b’aci.” Na lumshe ido kawai ina daga cikin d’aki ina sakin murmushi. A.Khadija ta ban ka’da labulai ta shigo, idonta a kaina ina aikin taje gashin da ya bi ya dameni Saboda tsabar yawansa da tsaho. Ga shi na da’de ban yi saloon ba. Baki ta bu’de tana kallona tana dariya “Ah! Lallai AYSHA kin samu kan ki dole ki manta da ni, irin wannan kyau da kika yi haka?” Turo baki na na yi ina furta “Wani kyau kuma? Ni da ko man arziki Umma ta hana ni shafawa ta hanani saka ko kwalli.” A.Khadija ta saki ajiyar zuciya tana karb’ar comb d’in hannuna ta ce “Wallahi kin yi kyau AYSHA fiye da zatonki, ko don dama can ke mai kyau ce..” Ta taje min kan tsaf ta kama ta tufke, sannan ta jawo babbar ledar hannunta “Tashi kiga Kayan bikin da na siya miki.” Ido bu’de nake kallon ha’daddun kayan di’nkuna masu kyau na zamani. Ban san sanda rungumeta da k’arfin gaske ba. Itama dariya ta yi ta rungume ni. Na kwashi kayan na fita da su parlor wajen Umma. Kayan Umma ta Kalla Kafin ta kalli Anty Khadija ta ce “An gode k’warai Khadija, amma da baki wahalar da kanki ba, don Aysha Ba Zata zauna a gidan nan lokacin biki ba… can gidanki ma zan turata su zauna da mai aikin ki da k’anwarki…” Cikin wani irin yanayi nake kallon Umma sai dai bata ba ni fuskar ma da zan mata musu ba, hakan yasa na ja k’afata na koma cikin d’aki, zuciyata ta min rauni na zauna kawai bakin gado na zuba uban tagumi, duk d’okin bikin nan da na ci ashe ma Umma ba zata bar ni na je ba. Anty Khadija ce ta shigo ta zauna kusa da ni. A hankali ta ce “Ki yi hak’uri AYSHA, na san Umma tana dalilin hakan, kada ki ce zaki yi fushi da ita ba Uwar da zata guji d’an ta fa hakan da take miki soyayya ce…” d’aga mata kai kawai na yi ina murmushin da sam bai kai zuciyata ba… Anty Khadija ta min sallama da cewa sai na taho. Na d’aga mata kai.
Kashegari jikina a sanyaye na mik’e Umma ta shigo tana kallona “Ki ha’da kayanki, za’a kai ki can gidan Yayanku da yamma.” Na d’aga mata kai kawai.
Da yamma kuwa ina zaune a harabar gidan Abba ya saka ni shara don dama haka kawai idan ya bushi iska sai ya ce na fito na share harabar gidanmu. Duk girmanta kuwa haka nake shareta tas, yau ma sharar nake, na ji k’arar shigowar mota, gaba na ya yi wani irin fa’duwa. Tsabar kyan motar ban san sanda na d’aga ido ina kallonta ba, Mai motar bai fito ba kamar yarda nima ban fasa shara ta ba, sai dai ina ji a jikina kallona yake yi. Don haka na ji na bi duk na daburce. Fitowar Yaya Muhammad ne yasa ni ajiye tsintsiyar na zauna a saman wani dakali ina kallon yarda Yaya Muhammad ya nufi inda motar take. Tsawon minti guda na ga an bu’de motar mai Motar ya ziro wasu takalmansa masu kyan gaske, ina d’aga kai na idanuwa na suka fa’da cikin na USTAZU yana tsaye idonsa a kai na… Da sauri na ajiye tsintsiyar ina sakin tsaki na juya na bar wajen… cikin wani irin k’unar zuciya da b’acin rai….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 33…
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.