← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da hawaye na na shiga gidanmu ina tunanin Ashe za mu ga wannan rana? Ashe Mami za ta daina amsa sunan Juya a wajen dangin Miji? Tabbas bayan wuya sai da’di.

A zaune na samu Mamina na isa wajen na zauna a gefenta cikin murmushi na furta “Alhamdulillah Sannu Mami.” Ta Shafa min Kai na ta ce sannu Ayshatu… Allah ya rabaku lafiya Allah yasa kada ki sha wuyar da na sha.” Ameen na furta jiki na a sanyaye kafin na Kai hannu na d’auko babies d’in masu tsananin kyau kamar ni ina jaririya Sun sha fararen kaya masu kyau gaske. Da sauri na kalli hoto na da yake gefen gadon Mami hotona ne ina jaririya na ce “Wallahi Babie d’in nan da ni suke kama.” Abba d a yake tsaye ya saki murumushi ya ce “Ba sai kin rantse ba Aysha, ai tun d’azu Nima na fa’da kama suke da ku sosai.” Na rungume su a jikina da k’yar Abba ya ce na bada su a kaiwa Ustaz.

Kafin ka ce meye wannan gidan mu y’a cika dank’am da mutane. Y’ay’a da surikai da jikokinsu haka aka cika gidan taf ana taya Mami murna, tabbas haihuwa rahma ce kuma ina tausayawa Wanda bai yi ta ba, sai dai kuma akwai ladansa mai girma a wajen Ubangiji ba mamaki y’a zama sanadiyyar shigarsa Aljanna.

Sanda Ustaz yazo don mu tafi dagawa na yi anan zan kwana. Abba ne ya ce tilas sai na fita na bi Mijina kwanan me kuma zan yi? Haka na tafi duka raina a b’ace. A mota Ustaz yake sanar da ni Visar mu ta fito. Na jefe shi da hararar wasa na ce “Kai ma ka San ko birnin lantsandan ne ba zani ba, har sai an yi suna.” Ustaz ya ce “Kada mu yi haka da ke K’alb, tunda dai t haihu lafiya ai shikkenan.” Na turo baki na ce “Kada ma ka fara, Am serious I won’t go anywhere…” shiru ya yi na lura ransa ne ya b’aci shi yasa bai sake min magana ba, ni kuwa ba zan sauka daga kan nawa ra’ayi nn ba. Haka muka kwanta yana Jin haushina dai dai bai fasa yi min duk abinda yake min ba. Ya bani abinci da drugs d’ina ya ha’da min ruwan wanka.

Tsakar dare…..

Cikin hukunci Ubangiji na ji baya na ya yi wata irin amsawa. Ba shiri na mik’e jin Mara ta ta amsa itama. Ban san sanda na d’aka wa Ustaz duka ba a gigice ina furta “Ka tashi mutuwata ta zo Ustaz, wayyo ka yafe min.” A Gigicen shima ya tashi. Yana kunna side lamp ya ce “Lafiya me ya faru?” Azabar ciwon da na sake ji ne yasa na damk’i hannunsa da k’arfi ina salati na ce “Mu tafi Asibiti Ustaz mutuwa zan yi..” da azama y’a zura min Hijab ya kinkime ni zuwa cikin mota don bana jin zan iya tafiyar ma. Ciwo kam na sha shi kafin mu isa asibiti, sai dai cikin k’udirar Ubangiji muna isa asibitin na haihu yaro namiji kyakykyawa jajir da shi kamar d’an larabawa. Farin ciki ne ya ratsa ni sanda na bu’de idona a kan fuskar yaron mai kama da Babansa kwabo da kwabo. Na furta “Alhamdulillah” cikin muryar da ta riga ta galabaita.

Ahmad ne ya fara shigowa cikin d’akin. Idanunsa a kaina ba ya ta Babyn da ake mik’a masa cewa kawai yake “K’alb, hope dai k’alau kike?” Na gya’da masa kai ina murmushi sai da ya saka hannu ya kwantar min da gashin kaina da ya yi Buzu Buzu sannan ya amshi jaririn da likitan take mik’a masa. Manna shi ya yi a k’irjinsa yana sakin ajiyar zuciya kafin na ga ya manna masa sumba a lab’b’an sa a hankali ya furta “What a wonderful gift! Alhamdulilah ya rabb…” ya lumshe idonsa sai ga hawaye suna zubo masa. Na saki murmushi nima ina jin k’wallar na son zubo min. Ya bu’de idonsa yana sakin murmushi ya furta “Kyauta mafi girma, daga halittar da nafi so fiye da kaina a duniya….” Sai da aka gama shirya mu sannan Ustaz ya dinga gayawa Mutane na haihu. Na San kowa sai ya yi mamaki don na rage edd na da kusan sati uku.

Kafin me, tuni asibitin ya cika da mutane, sam ba su wani duba tsakiyar dare ba ne. Yayyena duka sun zo haka Humaira Umma da Mami na, da ba yadda ba’a yi ta zauna ba Amma sai da ta zo. Humair sai ta tambayata take wai haihuwar da wahala? Murmushi na saki ina kallon turtsetsen cikinta na saki dariya na ce “Wallahi ki shirya ma, don ba na jin a duniya akwai ciwon da ya kai na haihuwar azaba..•” Humaira ta waro ido…

Asubar fari aka sallame ni. Mami kuwa tana gefena bata la’akari da sabon jegonta sai kulawa take ba ni. Da nuna tausayawa.

Sanda muka isa gida na Hajiyan Potiskum ce ta tilastawa Mami sai da ta tafi gida fa’di take “Tafi maza y’ar albarka ke ma ai d’anyen jego ne kike haihuwa kwana guda, sai sanyi ya kama yaran.” Haka Mami ta hak’ura ta tafi ba don ta so ba har a ranta.

Haka aka cigaba da kulawa da ni. Gefe guda kuma ana ta shirin ha’da suna na da na Mami inda za’a yi shi a wani Babban wajen biki.

Ranar suna da safe Ahmad ya sanar da sunan yaro Sulaiman sai muke ce masa AKBAR.

An tari sosai a shagalin sunan. Inda twins d’in Mami suka ci suna NILFA DA NAUFA. Abba na bai ji kunya ba sunan Matansa Mami na da Umma na ya mayar.

An sha suna an gaji jikina ya yi Lakwas. Hakan yasa muka yi wanka kawai muka kwanta.

Cikin daren na ji Ustaz a jikina da sauri na bu’de ido ina kallonsa ina nuna masa Hajiyar potiskum da take zube a k’asa tana barci. Ya saki ajiyar zuciya ya ce “To tashi mu je, wata mahimmiyar magana za mu yi.” Ban yi musu ba na mik’e don ban hango wasa a idonsa ba.

Ina shiga d’akin na gan shi yana parate a tsakar d’akin fuskarsa a ha’de sosai hakan da ya razana min zuciya. Na dinga kallonsa hankalina a tashe. Idonsa a kai na ya mik’o min wata farar enveloped na kalleshi na kalli takardar zuciyata na wani irin bugu. “Karb’i mana…” na ji ya furta muryarsa a sama. Hannuna na rawa na amshi takardar na bu’de ina addu’a ido na a runtse kafin na Ware ido akan takardar. Abinda na gani ne yasa Ban san sanda na daka tsalle na rungume shi ba takardun wata babbar plaza ce da yake ginawa shine ya mallaka min. Kiss na masa sosai kafin na ce “Na gode Jannaty, ka yi min komai…” muryarsa na rawa ya rungumeni yana furta “Ni ne da godiya K’alb, kin shayar da ni duk wani abu da nake so a rayuwar nan kin bani farin cikin da Ban tab’a zaton akwai shi ba. Ke mace ta gari ce Mumina mai halin k’warai duk Wanda Allah ya bashi mata irinki a duniya to fa ba shi da wani sauran buri a duniya sai dai ya yi fatan dacewa da lahira… Allah ya yi
Miki albarka K’alb…..” Ya fa’da yana manna min kyakykyawar sumbata a bakina. A hankali ya janye daga jikina yana furta “Madalla da Mace ta gari, Alhamdulillah.” Nima na ce “Madalla da Miji na gari Alhamdulillah!” A tare wasu hawaye suka zubo mana. Tabbas rayuwar mu ta yi kyau Allah yasa mu dace.

Jikar Nashe ma anan take cewa Alhamdulilah sai mun ha’du a sabon littafina HADARIN GABAS….

Ga wanda yanzu suka fara bin littafina akwai wasu a k’asa. Masu tambaya…

Takaicin Uba….. labarin yarinyar da ta rasa dukkan farin cikin ta sanadiyyar mahaifinta. Ayra Gaya an sha gumurzu kafin ta amince ba duka maza ba ne suke amsa sunan Butulu…. Tabbas mijinta ya sha fama kafin ta amince ta amshe shi a matsayin miji saboda tsanar da ta yiwa Ubanta. Idan baki karanta ba 1k ne Amma ina promo zan ba ki shi akan 500 kacal.

Ya Abin Yake? Labarin yarinyar da Uwar ta ta tsaneta sanadiyyar wani b’oyayyen sirri da ita ka’dai ta sani sai Hammad da ya zamo d’a ga Mijinta ashe akwai k’ura a lokacin da Hammad ya bayyana kansa a matsayin Mijin Hamda da suke Uba d’aya. Anan allura ta tono galma…

Me Zan Yi da ita? Littafin da ya kara’de duniyar rubutu.

Gaskiyar Lamari…

K’udirar Allah…. Mhmmn wata miyar sai a mak’ota.

D’AND’ANO DAGA KUDIRAR ALLAH.

LITTAFIN NAZEEFAH SABO NASHE.

PAID BOOK IDAN KIN SHIRYA
SIYA
TURA KUDIN KAI TSAYE A
ACCOUNT
NUMBERR NAN. 2118666253 UBA

KI TURA
SHAIDAR BIYA TA 08033748387.

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

Ya zama complete biya 1k kacal don ki karanta.

SARAUTA TA DANNO. SHAHARARRIYA MARUBUCIYA NIMCYLUV ZATA ZO MUKU DA SABON LITTAFINTA MUTALLAB 1.10.2024. SAURA KWANA BIYU💃🏿 HANZARTA SHIGA GROUP DON KARANTA LITTAFIN DA BA NA BIYUNSA A WANNAN SHEKARAR….

Domin a fara tafiyar littafin *💋MUTALLAB💋* da kai join our Conversation group. Musamman iyaye mata wanda yaransu ke age ɗin Adolescence

https://chat.whatsapp.com/GjfdfXJ0Pg0HGgCT0UkCt5

Na yi gaba sai kun zo 💃🏿💃🏿
Chapter 49 · 0% Book details