Sashe 14
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kwana biyar tsakani Umma ta ce na tattara kaya na na koma gidan Ya.Muhd kada na dawo har sai an gama biki. Idona cike da hawaye na ce “Umma ba zan yi attending bikin ba?” Ba zaki yi ba Aysha, akan me za ki yi attending biki? Idan yaso duka idanun y’an biki ya dawo kan ki da wanda ya san labari da wanda bai sani ba kowa ya ji ko?” Na girgiza kai na. Tsam na mik’e na fara tattara kaya na zuciyata a mugun k’untace. Ina gamawa Umma ta ce na fita driver na jira na. Da sauri na fita idona na zubar da k’walla. Umma ta d’an yi tsaki kawai. Ina ji tana furta “Sai na zauna ina kallo mutane suna nuna ki ana yama’didi da abinda ya faru saboda ba ni da kai, bakin duniya ya je ya sake tagayyara ki.” A mota ba abinda nake sai tsinewa mutumin da ya yi silar shigata cikin wannan matsalar da ban ji ba ban gani ba.
A gidan Yaya Muhammad kuwa da wani irin murna da farin ciki su Anty Khadija suka tare ni. Ga k’annenta har biyu da ta kawo su taya ni zama. Ayra y’ar su y’ar shekara biyu itama ta ‘dafe ni tana dariya. Sai na ji duk wani k’uncin zuciyata ya fara Yayewa na rungume Ayra ina dariya.
Wanka na shiga na fara yi, don yinin yau kaf ban yi wanka ba. Kai na da yake cunkushe Anty Khadija ta kalla ta yi tsaki tana furta “Sannu Aysha, so kike ki lallata gashin ki ko? Maza Samira shirya ki kai ta saloon d’in da muka je jiya a gyara mata kai, a mata predicure da manicure, kada ku dawo gidan nan sai na ganta tsaf kamar amarya.” Na turo baki na ina furta “Ki bari sai gobe Anty Khadija daga zuwa na, ni fa duk wa’dannna abubuwan yanzu bana son su..” Khadija ta tab’e baki ta ce “Yanzu kuwa zaku tafi, kuma har lalle sai an miki duk da dai ba ke za’a bikin.” Girgiza kai na yi na ce “Gaskiya zan yi komai amma banda lalle.” Anty Khadija bata kula ni ba ta bawa Samira Atm ta ce “Idan kun dawo a d’aura girki ni zan je wajen Umma.” Na fita ina jan hannun Ayra da ta bi ta mak’ale min.
Samira k’anwar Anty Khadija tunda muka fita take aikin yi min nasiha, da nuna min illolin bin ru’din samarin Zamani. Kallonta kawai nake ina mamakin kalamanta ban ce mata komai ba illa murmushin takaicin da nake saki, don na san ba laifinta ba ne, kowa kallon da yake min kenan. Tsaf aka wanke ni aka gurji fatar jikina duk wani datti da ya mak’ale min sai da ya fita tas jikina ya zama kamar mudubi tsabar santsi da sulb’i. Gashi na ya yi tsaho na ban mamaki. Ni kaina da na kalli kai na a mudubi sai da na sake kallon kai na na saki murmushi. Mai gyaran kuwa sai cewa take “Ma sha Allah! Wannan in dai amaryace yau na san zautarwar da zaki yiwa mai gidan Allah ne ka’dai zai k’wace ku, irin ku ko fatar jikinku ba zata bari a yi kishi da ku ba, jiki kamar tarwa’da.” Murmushi kawai na saki. Ina jin yarda jikina yake wani tashin k’amshin turaren da aka min na jiki. Muka biyata ku’dinta muka fita Samira ma sai zuzuta kyan da na yi take.
Girki muka d’ora don Anty Khadija ta ce mu ‘dora girkin Ya.Muhammad yana azimi kasancewar alhamis ce. A gurguje muke aikin don lokaci ya Riga ya k’ure. Kunun kwakwa da madara muka masa sai plantain da chips da liver sauce. Muka ha’da masa tamarind juice da aka ha’da da apples. Ganin mun gama na tattara ba barwa Sameera gyaran kitchen d’in. Na ja hannun Ayra don na mata wanka don duk ta b’ata jikinta da cornflakes d’in da ta sha. Duk toilets d’in bedrooms d’in ba ruwan zafi ya k’are haka yasa na janyo hannunta zuwa na sitroom da Samira ta ce min akwai ruwan wankan. Anan na mata wankan ban san da mutane a parlorn ba hakan yasa na ajiye hijab d’ina na fito gashi na kwance a saman baya na jikina kuwa wata Riga ce k’arama na fito rungume da Ayra a hannuna. K’iris ya rage na saki Ayra a k’asa ganin wa’danda suke zaune a sitroom d’in. Ya.Muhammad ne da Ustaz da wani da ban san sunansa ba. Kuma mutumin ya kafa min ido kamar zai ce babu. Ta k’asan ido nake kallon yarda fuskar Ustaz ta yi kicin kicin da b’acin rai. Na rasa yarda zan yi tabbas idan na fita a haka ba abinda ba zasu gani ba a jikina, don Rigar irin tsukakkiyar nan ce da ta fitar da duk wata sura a jikina idan na ce har Shatin pant d’ina ana gani ban yi k’arya ba. Idan har na juya zuwa toilet d’auko Hijab d’ina nan ma za su ga baya na. Ya Muhammad ya mik’e don da alama bai lura da ni ba. Sai na ga Ustaz ya mik’e ya nufo inda nake fuskarsa a mugun ha’de ya wani irin zabga min kallo ya yi bake-bake a gaba na ta yarda na zaunen ba zai iya gani na ba murya a cunkushe ya ce “Koma cikin toilet Malama!” Da wani irin sauri na shige cikin toilet d’in don dama irin taimakon da nake so kenan. Na d’au Hijabi na da yazo min har k’asa na fice a toilet d’in kai na a k’asa. Ina ji Bak’on ya furta “Ahmad wacece wannan d’in.” Murya can k’asa na ji Ustaz ya furta “My Ex-Wife…akwai wani abu ne?” Ni dai na shige ciki da sauri duk jikina b’ari yake na dinga ja musu Allah ya isa kamar laifina ne ba nasu ba. Tunda na shiga kuma ban fito ba. Sai da Sameera ta lek’o d’akin tana kallona ta ce “AYSHA ki je in ji Abban Ayra kina da bak’o.” Baki sake nake kallonta kafin na furta “Bala’i, ki je kice ba zan zo ba, nazo na masa Uban me?” “Ki masa Ubanki, mara kunya fitsararriya…” na samu muryar Ya Muhammad yana furtawa a sama. “Ba zaki tashi ba..” Da wani irin k’arfin hali na ce “Wallahi na zani ba…” Sai naga Yaya Muhammad ya bu’de ido ni kuwa na cigaba da cewa “Ai wallahi ko kashe ni zaka yi ba zani ba…” Ban yi aune ba naji saukar mari a saman fuskata a zafafe Ya.Muhammad yake furta “Ni kike gayawa haka, da kika samu har yazo yana son ganinki banda shima baida zuciya ban ga Uban da yasa zai sake neman aurenki ba a karo na biyu.” Duk da zafin marin da na ji bai hana ni sakin wani murmushi ba na ce “Na rantse da rabbu ba zan je ba Yaya Muhammad sai dai kai gutsi gutsi da nama na, da na koma gidan wancan mutumin gwara na mutu ba aure…” Zai sake kai min duka sai naga Sameerah ta hana hakan yasa ya fice a hassale yana fa’din Samira fito bari na saka shi ya shigo cikin d’akin tunda ita bata da mutunci. Ina kallo Samira ta fita na wani irin dariya ina wawurar wani sandan labulai da yake gefe na na tsaya a tsaye kamar y’ar Caburos so nake kawai Ustaz ya shigo na tafka masa. Zuciyata tana wani irin zafi na ji an turo k’ofar yana sallama cikin kwantacciyar murya. Ko rufe bakinsa bai yi ba na cilla masa sandar ina huci na nuna shi da yatsa…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 35….
NAZEEFAH SABO NASHE.★✍️
08033748387.