Sashe 34
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali na tura k’ofar d’akin Mami na. Wannan karan a zaune na sameta tsaf da ita cikin kwalliya sosai sai zabga k’amshi take…. Ta d’ago tana kallo na da mamaki ta ce “A’isha ke ce da safen nan? Ho ho ho! Aysha Sam ba kya girma, idan banda haka daga fitowarki jiya shine kika zabaro k’afa kika fito.” Zama na yi a jikinta na rungumeta sosai na ce “Mami na ina missing d’inki shi yasa wallahi gidan ba da’di shi yasa, don Allah ki koma gidan mu Mami…” wani irin kallo ta hurgeni da shi kafin ta jijjiga kai ta ce “Ni da gidanku Aysha har abada! Babu sunan da nake kiran gidanku a yanzu haka sai BAKIN GIDA…. Idan ma abinda ya kawo ki kenan gwara ki tashi ki tafi.” Idona ya cika da k’walla ganin yarda b’acin ran Mami ya bayyana ainun.. na gyara zama na a jikinta ina sakin kuka. A hankali ta saka hannunta tana bubbuga baya na ta ce “Ki yi shiru ba abinda zai raba ni da ke. Am still your caring mother… ya labarin wannan yarinyar kin ji ana zancenta a gidanku?” Sam na manta wace yarinya ce don haka na ce mata “Wacce Mami?” Ta d’an cije leb’enta ta ce “Your carbon copy, me kika ji Imamu ya ce a kanta ko shi ko Ummanki?” Na gyara zama na ina kallonta na ce “Me yasa kike son sani?” Ta girgiza kanta ta ce “Komai ma, kawai gaya min….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢✍️★
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA…..48.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Na yi saurin zame hannuna da Naga Ya Usman da ya rik’e ni. Na isa wajen Mami a hankali na fa’da jikinta ina sakin kuka na furta “Mami na!” Tsam na ga ta yi tana kallona da hawayen da suka jik’a mata idanu, sai naga ta janye ni daga jikinta da sauri ta mik’a a hanzarce ta bar wajen. Jikina a sanyaye na bi bayanta da kallo. Anty Khadija ce ta zo ta kama ni tana furta “Tashi AYSHA mu je gida ki huta.” Na kalleta da idona da suke zubar da k’walla sai ta girgiza min kai ta saka hannu tana share min k’wallar a hankali ta furta “Yau ranar farin ciki ce AYSHA ba ranar kuka ba.” Ban fasa kukan ba don ji nayi kamar yanzu abubuwan suka dinga faruwa. Na bi bayanta ina kallon yarda kowa na gidan mu yake yi min kamar ya lashe ni. Na tuna wa’dancan idanun nasu na wancan lokacin da suka dinga yin kamar su kashe ni don haushi. Fuskata na tsuke musamman hango Ustaz da na yi fararen hak’oransa Sun k’i su rufu, haka kawai sai naji haushinsa y’a tokare min a k’irji. Ido na zubawa Umma na da take ta kuka kamar me? Na d’auke kaina kawai bayan na yi k’asa da idona ina wasa yatsun hannuna. Dukkansu haushinsu nake ji kamar yarda zuciyata ta kasa musu uziri. Ya Usman kawai na rab’u da jikinsa ya dinga buga min baya a hankali yana furta “Am happy for your happiness AYSHA.”
Ya ja hannuna yana furta “Ya kamata mu tafi gida haka, ki je ki huta ki samu isashshen barci.” Hakan yasa duk Naga sun biyo ni. Ustaz ma yana gefe na kamar ya janye ni daga jikin Yaya Usman ganin yarda yake ta shiga jikina.
Muna fita y’an jarida suka mana caaaa ni kuwa na runtse ido na haushi da takaici kamar ya kashe ni duk tambayar da suka min kawai sai na saka kuka na ce Alhamdulillah!” K’arshe dai na ji Ustaz ya janyeni da sauri na koma gefensa direct inda motocinmu suke ya nufa.
Ganin yarda kowa yake k’ok’ari sai na bi shi hakan yasa Abba ya ce “A’a ta bi Mijinta, idan ta huta sai ya kawota gida.” Zuciyata ta yi wani irin zillo a raina na ce “Ai kuwa wannan karan zaku sha mamaki, ba zan koma gidan mutumin da Uwarsa bata so na ba.” Don haka na ja hannun Ya Usman na fa’da motarsa ina cewa “Kai ni gida Yaya Usman, kaina kamar zai tsage.” Ba Wanda ya lura da shigata motar don ina ganin suna ta waige waige. Ya Usman kuwa ko matarsa bai nema ba ya ja motar da k’arfi muka bar harabar kotun. Sai sannan na saki ajiyar zuciya mai k’arfin gaske ina lumshe ido na. Duk wani bak’in cikin da ya cunkushe min a zuciya naji yana zagwanyewa. Yaya Usman bai tafi da ni gida direct ba sai da ya biya shop rite. Ya ce na zauna a mota ya shiga ya fito. Ya kai 1hour kafin ya fito da ledo di a hannunsa ya saka a mota. Sannan muka hau titi yana kallona ya ce “Gidanki zan kai ki ko gidan Abba?” Wani kallo na wurga masa sai kuma na saki murmushi na ce “Gida na kuma? Ai na bar gidan nan har abada Yaya Useey, kamar yarda na bar mai gidan, wancan karan ma ba yarda zan yi ne an fi k’arfina shi yasa na koma gidansa. Banda yanzu da na San ina da y’anci kowa kuma ya san ban aikata abinda na aikata ba.” Ya Usman ya waro ido ya ce “Ki bi komai a hankali AYSHA, me ye laifin Ustazun naki?” Na turo baki na na ce kada ka sake cewa Ustazuna Ustazun Hameeda dai.” Murmushi kawai ya saki bai musa min ba ya ja mota zuwa gidan Abba. Yana parking ya kalleni yana tsatstsareni da ido ya ce “Banda tuna baya, ki bi komai a sannu bana son rashin kunya balle ramuwar gayya.” Na d’an tab’e baki na kawai na fita daga motar. Shi kuma ya biyo ni da kaya a hannunsa.
Fuskata a d’aure tamau na shiga gidan mu. Gaba d’aya suna tsaye a tsakargida da alama dawowata suke jira. Babu Wanda na kalla na yi hanyar wancan d’akin da suka bani lokacin da abin ya faru. Na shiga kai na tsaye. D’akin yana nan a gyarensa na dubi d’akin ina sakin murmushi da kai tsaye na San na takaici ne. Yaya Ysman ne ta turo k’ofa yana kallo na ya ce “Me ye haka AYSHA?” Na ware hannu na ce “Me na yi?” Tashi ki koma b’angaren Umma kiyi wanka a can.” Shiru na masa sai naga ya fita da sauri. Sai ga shi Sun dawo da Abba. Abban ma yana kallona ya ce “Shatu na me kenan? Tashi tashi don Allah, tashi ki koma cikin gida.” Bani da damar yi masa musu Amma ina ji a jikina wannan karan sai na d’ana. Kallonsa na yi da idona da yake cike taf da k’walla na ce “Abba ina zani? Nan d’in ai shine d’akina da kuka zab’ar min.” Gani na yi kawai ya zauna daf da ni, ya kamo yatsun hannu na cikin taushin murya ya ce “AYSHA banda tuna abinda ya wuce, komai ya faru a baya ina son ki d’aukeshi a matsayin k’addara, ba k’in ki ne ya saka muka yi Miki wancan talalar ba sai zallar soyayya, ba Wanda zai so yaga nasa a cikin waccan rayuwar. Wani gata ne bamu nuna Miki a gidan nan ba? Ina ji kaf yara na ba Wanda na so irin son da na Miki Shatu, to abinda aka ce kin aikata ne dole ya sosa zuciya dole mutum ya ji ba da’di a ransa duk mai sonki dole ya ji haushi amma ba tsana ba ce, mun yi haka ne don samun nutsuwarki AYSHA, tunda abin nan ya faru a kullum daren duniya sai na rok’i rabbil Izzati y’a shirya min ke, idan kuma bake kika aikata ba Allah y’a bayyana gaskiya…” kuka ne ya k’wace min na ce “Amma Abba me yasa baku yarda da ni ba? Me yasa ba ku yi tunanin a irin tarbiyyar da kuka bani ba zan iya aikata haka ba? Ya kamata tun a lokacin ku yi min uziri a yanayi na ya kamata ku San abinda zan aikata da Wanda ba zan aikata ba.” Ja na jikinsa Abba ya yi kawai yana bubbuga baya na. Cikin muryar lallashi ya ce “Ki yi hak’uri hak’ik’a mun yi kuskure…” Lunshe idona na yi a jikinsa ina tuna irin k’untata min da wulak’anta ni da aka yi, duk akan laifin da ba nawa ba. A kullum kallon tsana nake gani muraran a idanunsu. A hankali na ce “Ba wanda fa ya min uziri Abba sai Ya Usman Anty Khadija da Mami na, yanzu Abba da wani idon zaka kalli Mami na?” Sai naga ya runtse idonsa kawai yarda ya yi d’in y’a tabbatar min tabbas lamarin ya girmama a zuciyarsa cikin wata irin murya ya ce “Tabbas na zalunci Fateema, ban san kuma da wani ido zan kalleta ba, da ina da dama dana janyo wancan lokacin na goge abubuwan da suka faru a baya, sai dai lokaci ya k’ure min. Ayshatu na zalunceku don Allah ki yafe min…” sai naji Zuciyata ta yi rauni mahaifina ne ya zan yi da shi? Tilas na hak’ura Amma kam zan rok’eshi ya k’yaleni ba zan koma gidan Ustaz ba.
Muryata na rawa na ce “Abba ka daina rok’ona wacece ni? Ni fa abar ikonka ce kana da dama a kaina zaka iya aikata fiye da hakan a kaina baka yi laifi a wajen Ubangiji ba, ballantana kuma ni, alfarma guda zan nema a wajenka don Allah kada ku matsanta min zama da Ustaz! Ina son ya sake ni.” Abba ya d’ago a hankali yana kallona sai naga ya girgiza kai ya ce “Me yasa AYSHA?” Bana son sa Abba a yanzu aurensa gaba d’aya ya fitar min daga rai, karatu nake son na koma, bana son na yi aure sai nan gaba.” Shiru Abba ya yi yana kallona kafin ya girgiza kai ya ce “Shikkenan, tashi yanzu muje ki yi wanka ki shirya a d’akin Ummanki, ga y’an uwanan fal a gidan suna jira ku ci abinci.” Na mik’e fuskata a dame da hawaye na bi bayan Abba.
Har a lokacin suna nan a farfajiyar gidan mu. Ustaz yana zaune daga gefe idanunsa a kaina sai sakin mayalwacin murmushi yake. Ko d’igon fara’a babu a fuskata na shigesu na shiga d’akin Umma.