Sashe 3
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba wanda bai bu’de ido yana kallonta ha’de da jin mamakin furucinta ba, ta bimu da kallo d’aya bayan d’aya kafin ta sake jinjina kai ta fice daga d’akin. Ina ji dai Abba mutuwar zaune ya yi. Umma kuwa idanunta ko blinking basa yi tsabar tashin hankali. Ni dai na san na lumshe ido amma bayan haka ban sake sanin komai ba, sai farka wa na yi na ganni shimfi’de a tsakargida jikina sharkaf da ruwa ba kowa a wajen, sai Yaa Usman da Jummai mai aikinmu suna ta faman yi min sannu. Na mik’e zaune ina jin kaina kamar zai rabe biyu ina kallon Ya. Usman na furta “Don Allah Ya.Usman kace min mafarki nake ba gaskiya ba don Allah.” Hawayen da naga suna sauka daga idonsa ne ya tabbatar min da ba mafarki nake ba. Hannu ya kama ya damk’e cikin nawa ya matsa da k’arfi yana furta “Why AYSHA? Me yasa kika zab’i waccan rayuwar mai matuk’ar muni da ba inda take kai mutum sai tashar nadama? A farko dai mutum yana jin da’dinta kafin ta jirkice ta koma saka mutum Nadama! Why AYSHA duk tarbiyyar da aka baki a gidan nan kin hanb’areta kin dasa wata daban, me kika rasa? Ci sha ko sutura ko kayan more rayuwa? Kowa burinsa a gidan nan samarwa AYSHA farin ciki ashe ke kina nan kina bin abinda zuciyar ki take so. Idan wannan hoton na baya da ya nuna mana a buge kike, AYSHA wancan Kuma vedion a ras ‘dinki kike, amma kike zaune akan cinyar namiji… Ga shi nan Kin ja Abba ya yi mummunan fushi da ke, Umma kuwa ta ce kada na shigo da ke d’akinta gwara ki mutu ta huta… Abba ya saki Mami…” Duk abinda yake fa’da idanuna suna kafe a kansa bana ko k’iftawa. Wani irin zafi da tafasa nake jin zuciyata na yi. Ba abinda ke min yawo a kwanya sai furucin Mami ta ji da’di da na zama Karuwa! Ashe burin Mami kenan a kaina…” Na dinga jin zuciyata na wani irin bugu. Ganin kamar bana hayyacina hakan yasa Ya.Usy bani ruwa na sha, ya kama hannuna muka nufi d’akin Umma, binsa kawai nake kamar rak’umi da akala. Umma na gani na ta wani mik’e da sauri tana kallon Usman. Marairaice mata ya yi sai naga ta yi murmushi ta d’aga masa kai. Hakan yasa ya juya ya fita. Tana ganin ya yi nisa ta ‘dago tana kallona da wasu firgitattun idanunta ta mik’e tana furta “Biyo ni nan munafuka!” K’irjina ya buga na mik’e jikina a sanyaye na bi bayanta. Wani ‘d’aki da muke ajiye shirgi nan ta shigar da ni muna shiga ta mayar da k’ofa ta rufe ruf har da murza mukulli. Ta dubeni a tsawace tana furta “Cire kayanki tas! Bana son ganin komai a jikinki sai Brezier da pant… “ na bu’de ido ina kallonta muryata na rawa na ce “Don Allah Um…” “Rufe min baki munafuka! Wani abu zaki b’oye a jikin naki? Wanda duniya bata gani ba, zigidir kike kwance jikin namiji bakomai a jikinki sai pant…” Ta fa’da a tsawace. Ganin ba alamar wasa tattare da ita yasa na cire kayan nawa. Wata irin waya na gani ya ciro a bayanta ta shiga lafta min a jiki. Tun ina ihu har na saduda na yi shiru, don muryarta ma ta daina fita… Tana gama ta cillar da bulalar duk da magi y’ar da su Jummai suke mata bata bu’de ba, ta juya tana kallona “Kuma ki bu’de kunne da kyau ki ji ni, daga yau duk aikin gidan nan ya dawo kan ki… idan wancan hoton a buge kike d’ayan vedion fa ras da k’afafunki muryarki garau kina furtawa wani banzan namiji zantukan ba’dala, Kun cucemu kin karaya zuciyar mahaifinki munafuka!” Daga haka ta fice na runtse idona kukan ma ya k’i zuwa sai tafasar zuciya. Ina jin Jummai ta d’aura min zani na har hawaye take tana furta “Ya Ilahi wani irin duka ne wannan? Bari Usman yazo ya kai ki asibiti.” Tana fita kiran Ya. Usman na mik’e ina layi na zura rigata “Ba Zan iya ba guduwa kawai zan yi na ayyana haka a raina. Duk jikina ra’da’din zafin dukan yake……
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 24.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Ina saka kai tsakargida Ya.Usman shima yana shigowa hankalinsa tashe yake kallo na. Kafin na ga ya kama hannuna da sauri ya ja ni muka koma cikin d’akin. “Ina zaki Aysha?” Shine tambayar da ya fara jeho min. Madadin na amsa masa wani hawaye ne ya shiga suntiri a kumatuna. Ya zaunar da ni yana kunna fitilar d’akin. Wani guntun tsaki ya ja, yana furta “Nan Umman ta kawo ki? Anan d’akin shirgin zaki kwana?” “Usi ba wannan tambayar ya kamata ka mata ba, ka kamata mu tafi asibiti ji fa jikinta yarda duk ya yi Shatun Bulala. Sai sannan ya kalli jikin nawa da sauri naga ya waro ido yana furta “Ya Ilahi! Tashi AYSHA tashi mu tafi asibiti.” Na mik’e da k’yar ganin ina layi yasa Ya.Usi ya kama ni muka fita zuwa tsakargidan. Turus ya yi Jin Umma ta ce “Gidan Uban wa zaku? Usman ba zaka fita shirgin gallafirin yarinyar nan ba?” Fuskarsa a tsuke ya ce “Umma abin ya yi yawa, ji fa jikinta ji yarda kika mata rauni da bulala.” A zafafe ta ce “Sai me? Sai me don na raunatata ba gwara na illata jikin da take tak’ama da shi wajen jan hankalin mazan ba, ba wani asibiti da zaku wuce ki koma ciki. Kai kuma idan ka sake ka bita ban yafe maka ba..” Ina ji cikin sanyin jiki Ya.Usman ya zame hannunsa daga cikin nawa, ya wuce zuwa part d’in su. Wasu zafafan k’walla ne suka shiga zubo min, Ina ji Umma ta sake jan tsaki ta koma d’akinta. Jummai ce ta ja hannuna idonta fal k’walla muka koma cikin d’akin da muka fito. D’akin ta tsaya tana kallo na san ba mamakin da take sai ta yarda Ni AYSHA y’ar gayu zan kwana a d’akin nan, da aka tabbatar da ba komai a cikinsa sai shirgin b’eraye da muk’arebansu. “Ko zamu je zan wajen mu ki kwana AYSHA kafin komai ya lafa.” Jummai ta fa’da na girgiza mata kai na, na ce “Bar ni kawai Jummai, bar ni na kwana a inda Umma take son na kwana, fata na Allah ya ‘d’au raina a daren nan na huta….” Da sauri Jummai ta saka hannu ta rufe min bakina. “Ki yi shiru AYSHA kowane bawa baya wuce k’addararsa, kawai ki yi ta istigafari Allah gafururruhimu ne, duk girman laifin ki matuk’ar kika yi tsarkakakken tuba zai yafe miki…” Ido na k’ura mata cikin jin mamakin lafazin bakinta, kenan itama Jummai ta yarda ni zan aikata zina. Madadin na bata amsa takaicin da yake cin zuciyata ya hana ni kawai sai na lumshe idona ina zurarar da hawaye. Jummai ta mik’e ta fita daga d’akin sai gata ta dawo da bargo da zanin gado har da pillow ta mik’o min. Karb’a na yi na saka a gefena ta min sai da safe ta fita bayan ta bani panadol. Ban bi ta kan maganin ba, don ba buri na waraka ba ni ban k’i na mutu a ranar ba. Har jiri nake ji tsabar jigata da rashin cin wadatacen abinci tun bayan afkuwar lamarin. Alwala na samu kai na da fita yi kamar an tuna min a wannan gab’ar Ubangiji ne kawai gatan ki Aysha. Na shiga toilet d’in masu aiki duk da k’yama ta a ranar neman k’yamar na yi na rasa na fito na d’aura alwala a famfon tsakargidan mu. Na koma d’akin da a yanzu ya zama mallaki na. Sallah na tayar na dinga jerata ina kaiwa Allah kuka na a cikin sujjada da son ya agajeni ya tona asirin duk mai hannu a cikin wannan sharrin da aka min. Don dai na san ba ni ba ce, ba zan kuma tab’a yarda da ni d’in ba ce.
Ban kwanta ba sai k’arfe uku da kwata na dare. Kiran sallahr farko kuwa Umma ta banko k’ofa ta tashe ni. Da k’yar na bu’de idona ina kallon yarda take min kallon tsana ta furta. “Fito y’ar banza lokacin hutu Ai ya k’ure miki, fito maza ki ha’da wutar kunun sadaka ki kuma wanke wake na k’osan sadaka. Don na gayawa su Jummai wannan aikin daga yau ya dawo kan ki, wanke wanke da shara kawai za su dinga yi.” Wani irin kallo nake ma Umma kallo mai cike da mamaki kamar ina tantamar zamowar Umman Mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeni. Bata bi ta kan kallon da nake mata ba ta mik’e ta fice. Jikina ciwo yake matuk’a da gaske amma hakan bai hana ni tashi na isa inda ta ce na je d’in ba. Ba tun yau ake koko da k’osan sadaka ba a gidanmu. Don haka na san duk inda su Jummai suke yi musamman kasancewata mace mai son girki. Tukunya na ‘dora a wuta babbar gaske mai cin kwano goma. Sannan na dinga d’ebo ruwa a bokiti in zubawa sai da na zuba bokiti uku na paint. Na ha’da wutar da k’yar su Jummai dai suna tsaye suna kallo na da Umma ta ja kunnensu akan bata amince su taya ni ba. Sannan na koma kan wake kwano biyar na ‘debo don ma a surfe yake shi yasa ban sha wahala wajen wanke shi ba. Ina gama wankin waken aka yi kiran sallah. Na zame jiki da k’yar na je na tada sallahr ina hawaye saboda matsanancin ciwo da jikina yake yi.
Ban bar gaban murhu ba sai k’arfe goma na safe zuwa lokacin duk wanda ya ganni sai ya tausaya min, lokaci guda duk na fita daga hayyacina kamar ba Ayshan Mami ba.