← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 49

Sashe 26

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka aka fara zuwa dubiya duk Wanda yazo kuma Anty Khadija bata Jin kunyar ta sanar masa budueci na Kai gidan Ustaz shi yasa na samu raunin da aka min d’inki, ita take fa’da ni take bari da Jin kunya. Har dare ban sake ganin Ustaz ba, tunda ya lek’o yaga jama’a da yawa a d’akin, bai shigo ba ya fice da sauri. Ya dai kira Anty Khadija ya ce ta bani wayarta ta. Ya tambayi ba abinda nake so, shiru kawai na masa maganar duniya na k’i amsa masa, k’arshe dole ya yi cutting wayar. Ni kuwa na bi wayar da harara kamar Ustaz d’in ne ya zama wayar. Yayyena maza ba Wanda bai zo ba, fuskonkinsu cike da fara’a sai dai ni kuma ba Wanda na kula sai Yaya Useey. Da daddare sai ga Abba na a idonsa na hango irin tsabar murnar da zuciyarsa take ciki, duk da bai yi min magana ba, amma irin kayayyakin da ya judo ya kawo asibitin Sun tabbatar min da hakan. A hankali kuma ya ce “Allah Miki albarka 𝑨𝒚𝒔𝒉𝒂𝒕𝒐𝒖, wancan lamari kuma ki bar damuwa in sha Allah zan yi bincike mai tsauri a Kansa.” Shima ban amsa masa ba shiru kawai na yi.

K’arfe 9:00 Ustaz ya shigo, cikin wata azababbiyar Jallabiya coffee color Kansa ba hula hakan ya bawa kwantacciyar sumarsa damar fitowa sai k’yalli take. Kamar yarda sajensa da gemunsa suka kwanta suka yi luf. Wani irin k’amshin turare kake ji kawai a d’akin. Ta gaishe da Umman ZINATU har k’asa. Sannan ya k’araso wajena. Ba mamaki Umman Zinatun kunya ta ji ta mik’e da sauri ta fice bayan ganin Ustaz ya zauna daf da ni a gefen gadon yana kama hannuna. Murmushi ya yi ya bi bayanta da kallo a hankali ya mayar da idonsa kaina ya ce “Na koreta, na San idan ba haka na mata ba ba zata bari na sake da ke ba, ni kuma so nake kawai….” Sai na ga ya kanne ido yana d’aga gira yana kallon boobs d’ina. Tsaki na yi ina k’ok’arin gyara zama na, ya ce “Kada fa ki tashi, k’in ci abinci bari na kira Aunt Tasleem ta duba ki.” Na wurga masa harara na ce “Kai wai baka Jin kunya ne?” Ya yi dariya yana d’an sosai gefen hancinsa ya ce “Kunya for what reason zan ji kunya? Ai ni haka nake so ko ya San dal na b’are Eehsha a leda.” Na turo baki na ina furta “Ai shikkkenan ka ji da’di. D’azu ka ce na gaya maka duk abinda nake so zaka min, da gaske kake ka yi alk’awari?” Y’a d’aga Kai yana Jan karan hanci na ya ce “Gaya min koma me ye zan maki ko zan siya Miki koda duk arzikina za su k’are….” Na yi murmushi ina d’an Jan fatar leb’ena na cija ka’dan, ban Kai ga saki ba sai kawai na ji Ustaz ya saka bakinsa a nawa yana bani deep kiss. Ya yi son ransa kafin ya sake ni yana mayar da numfashi idonsa a lumshe ya ce “Ai sai ki ce min Ustaz I need you…” na ware ido na ce “Haka na ce maka?” Shima narkakkun idonsa ya shigar cikin nawa ya ce “Haka inkiyar ki ta nuna min, oya tell me, me kike so kuma, I promise you zan Miki yanzun nan.” Cikin idonsa na kalla murya ta a sark’e kamar mai mura na ce “Ustaz I want divorce right now…….saki kawai nake buk’ata yanzun nan, kuma kada ka manta muhimmacin cika alk’awari a musulunci…..

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….42.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Wani irin tashin hankali na gani kwance a cikin idanunsa, Har idanun ya fara tara k’walla. Hannunsa shaking yake a cikin nawa hannun sosai. Ya dinga kallo na yana cije leb’ensa. Har kallon ya isheni na janye nawa idon ina jin a zuciyata abinda na zartar d’in Shine daidai bana sonsa a yanzu ba kuma zan iya cigaba da zama da shi ba. Abinda nake so a gane an gane to kuma me zan yi? Ai yanzu nawa wasan zai fara. “Eehsha!” Ya fa’da cikin rawar murya yana dawo da fuskata saitin tasa fuskar. “Ki kalle ni pls, I want to talk.” Na k’i kallon nasa don ban shirya ya karyar min da zuciya ba. Inaga ganin ba zan kalleshi d’in ba ne yasa ya matsa hannu na a hankali ya furta “Please kada mu yi haka da ke K’alb, wallahi ba zan iya ba, zuciyata zata raunana Kada kice zaki min ramuwar gayya ta wannan hanyar wallahi ba zan jure ba AYSHA ko magagin mutuwa nake ba zan iya furta Miki kalmar saki ba….” Na ware ido na ina kallonsa kafin na saki murmushi da shi da kansa na San ya san na rainin hankali ne na ce “A yanzu ne ba zaka iya saki na ba kenan? Da ka tabbatar ni ba karuwa ba ce, mai yasa wancan lokacin ka sake ni alhali ba wuk’a aka saka maka a mak’oshi ba, wallahi Ustaz sai ka sake ni don na ci alwashin ba zan zauna da kai ba, I hate you Ustaz! Na maka tsanar da bana jin ina yiwa wani abin halitta ita….” Gani na yi ta runtse idonsa da suka yi jajur ya ce “Baki yarda da abinda na ce Miki ba kenan, wallahi Mommy ce ta tilastani wancan sakin ma ba son raina ba ne…” Na janye hannuna ina tab’e baki na ce “Ina ruwa na kuma, kai da Mommyn kuka jiyo kuma ku ta matsewa ni dai wallahi sai ka sake ni don daga nan ba zan koma gidan ka ba.” Da sauri yasa hannu ya rufe min baki yana furta “Shshhhh, kin san Allah ba ya son mace ta ce mijinta ya saketa hakan illa ce a wajenta wallahi don mala’iku tsine mata suke…” “Haka nan Allah ba ya son saki don Al’arshi girgiza yake idan an yi sa, don haka da ni da kai duka masu laifi ne wajen Allah tunda ban maka komai ba sai zalunci ka sake ni ranar da na tare a gidanka akan zargin da baka tabbatar ba, to wallahi a yanzu nima sai ka sake ni ko na maka ka a kotu….” Bakina ya bi da kallo yana d’an sakin murmushi ba mamaki ganin yarda bakin yake tsiwa yake ko kuma ya d’auki magana ta wasa. Don haka a zafafe na ce “Wallahi d a gaske nake, ba mai saka ni na canja abinda na yi niyya…” Ya mik’e tsaye ya ‘dan rankwafo da kansa saman fuskata ina jin hucin numfashinsa ya manna min kiss a lab’b’aina duk k’amshin turarensa ya bi ya baibayeni… “Har abada ba saki a auren mu, wancan ma k’addara ce aure na da ke Mutu ka raba ne Madam….” Na ce “ko?” Ya d’aga min gira yana lumshe ido. Na yi k’wafa na ce “Za mu gani.” Dariya ya yi ya sake manna min deep kiss a goshi ya ce “Mu ga alheri, na lura rigima kike ji bari na tafi ga wayata zan kira na dinga jin lafiyar K’alb…” na wurga masa harara bai bi ta kai na ba ya shafi kumatuna da inda ya tsole masa ido ya fita da baya da baya yana blowing min kiss… yana fita naji wani hawayen takaici ya zubo min haushinsa nake ji sosai a raina, musamman auren can da ya yi na tabbata yanzu ma can wajenta zai je, a hankali na ja tsaki na furta “Mayaudari kawai, mai k’aton kai…” sai kuma na saki murmushi ni ka’dai ganin yarda Ustaz yake neman saka ni na zauce. Umman Zinatu ce ta shigo don haka na ja baki ja tsuke don bana son mata magana sam, na lumshe idona kamar mai barci ina ji tana furta “Ba dai barci kika yi ba tun Mijin naki bai tafi ba.” A zuciyata na ce “Almunafuk’ati ban sani ba.”

Tun biyun dare ya dinga kirana a wayar ina ignoring d’insa. K’arshe don dole na d’aga wayar ganin ba zai bar kira na ba. Ina ji ya saki wata ajiyar zuciya, ya furta “Na kasa barci K’alb.” Zuciyata a tunzire na ce “Ko? Me zai hana ka barci bayan ga ka ga matarka….” Ina ji ya katse wayar bayan ya yi dariya sai kuma ga kiran vedio call ya shigo. Haka kawai na ji ina son sanin a inda yake wata ballagazar mata ce mai barin mijinta waya cikin dare… na d’aga kiran sai na ganshi a d’akin da muka sha budiri jiya. “Kin ganni, rungume da rigar barcinki mai d’umbin tarihi a wajena sai shinshinar k’amshin turaren jiki nake amma ya kasa kawar min da feeling d’in da nake ji a raina. Jikina maha’dinsa kawai yake buk’ata, ga Tasleem ta ce sai na baki koda 1 month ne kin warke sosai…” k’aramin tsaki na ja, ganin yarda yake wayar jikinsa ko riga babu sai wani lumshe ido yake. “Ka koma wajen matarka mana.” Ya d’an bu’de ido yana kallo na ka’dan cikin wata irin murya ya ce “Eehsha, are you jealous?” Na zabga masa harara na ce “Allah ya kiyaye na yi kishinka, kawai shawara na baka ko ka manta ita ce y’ar mutunci, y’ar gidan mutane masu mutunci ba ni da na watsar da martaba da mutuncin iyaye na a idonka ba….” Ina kallo ya runtse idonsa ya na jijjiga kai kafin ya yanke kiran. Sai ga msg d’insa ya shigo. “Idan na zo gobe, I will explain to you clearly…” na yi tsaki na cillar da wayar… ina jin haushin Ustaz ne zai kashe ni, zan jira gobe na ji da wace k’aryar zai zo…
Chapter 26 · 0% Book details