← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru na mata, don ba amsar da zan bata, na shige toilet na ‘daura alwala. Ina fitowa na sake ganin still ta koma barcin murmushi kawai na saki ina tunanin abinda Ustaz ya aikata. Sau biyu yana shigowa d’akin da daddare yana min inkiya da na tashi mu tafi, turo baki na nake fuskata a tsuke na girgiza masa kai. Sai ya karyar da kai kamar yaro yana neman Uwarsa. Yana kallon Inna da take barci ya ce “Ki tashi mu tafi, tunda Har ta yi sallah ta sake komawa barci ba zata tashi ba, wallahi na yi alk’awarin ba abinda zan miki, sai d’an Kiss kin san bana gajiya da bakinki ban k’i kullum na dawwama a haka ba.” Harara na watsa masa na tab’e bakina na ce wallahi ba inda zani, kuma don ka ji ma Har yau ina nan kam baka na ka sakeni kafin ka wuce da matar so…” wani kallo ya jefa min yana sakin murmushi k’asa k’asa ya ce “Matar so? Mhmn, ai ni bani da matar son da da wuce ki, ki tashi mu je ko sai na d’auke ki.” Wannan karan tsuke fuskata na yi sosai na mayar da kaina na kwanta don haushinsa nake ji sosai. Ina kallo ya hawo gadon ya jani jikinsa “Shikkenan, tunda ba zaki tashi ki taya ni ha’da kaya ba, bari na kwanta anan…” na bu’de ido ina kallonsa a hankali na ce “Wallahi ka tashi ba ruwana idan Inna ta farka fa? Na San dole zata farka…” Ya sumbaci bakina yana furta “To menene don ta farka? Tun kafin a haifo iyayenmu ta San me ake aikatawa a cikin aure.” Ya fa’da yana k’ok’arin zuge min zip, na yi saurin rik’e hannunsa na ce “Tashi kawai mu tafi, Amma wallahi kada ka sake ka tab’a ni, don ban shirya zaman aure da kai ba…” sauka ya yi ya bi bayana yana dariya muna fita corridor na ji ya d’aga ni cak muka haye sama. Wani irin dare ne da sam ba zan manta da shi ba, duk da bai k’etare dokar likita ba Amma na ji a jikina na kuma tabbatar Ustaz yana bala’in sona a yau kam, shi yasa naji zuciyata tana rauni akan ramuwar gayyar da nake son na masa… sai da muka yi wanka sannan na mik’e ina niyyar fita ya sake ja na jikinsa a hankali ya zaunar da ni samar cinyarsa a kunne ya ce “K’alb, ki ce kin yafe min, please! Bana son tafiya na barki kina Fushi da ni, 3weeks kawai zan yi na dawo sai mu koma da ke, tunda aiki e da zai d’auke ni tsawon 3months, hope kin hak’ura?” Na girgiza kai na idona na kawo k’walla na cije leb’ena na ce “Ta yaya kake zaton zan hak’ura? Kana son ka ce min na hak’ura da duk abubuwan da ka min, Har da munanan maganganun da ka dinga jifa na da su, Karuwa fa Ustaz karuwa ka dinga ce min, kai da y’a kamata ka zama kai ne farkon mutumin da zaka shaideni, ba zan b’oye maka a yanzu kam bana jin sonka ko ka’dan, gaba d’aya ya fice min a rai kawai dai zan zauna da kai ne zuwa wani d’an lokaci bana son a karo na biyu a sake jin aurena ya mutu, na San zan shafawa kaina bak’in paint ne, amma da gaske bana son aurenka a yanzu kam….” Kuka ne ya k’wace min na zame daga jikinsa na mik’e da sauri duk da kiran da yake min ban saurare shi ba na yi hanyar fita, ban tsaya ko ina ba sai cikin d’akina na kuma mayar na kulle har da murza key na bar mukullin a jiki. Na jingina da k’ofar wani kuka mai saka k’unar zuciya y’a cigaba da zuwa min. Haka na kife a saman gado na dinga kukan ba k’akkautawa. Da Asuba Inna ce ta tashe ni sallah, bayan na idar da sallah na ji wata matsananciyar yunwa hakan yasa na tafi kitchen ba shiri daidai lokacin Ustaz ya fito tsaf cikin shigar Black suit da Riga long sleeve a ciki Ash color. Ba k’aramin kyau ya yi ba Amma hakan bai saka na saki fuskata da na tattara na tsuke ba na shige kitchen da sauri, ina shirin kulle k’ofar ya saka hannunsa banda tausayin musulunci ba abinda zai hana ni datse hannunsa, wato tafiyar zai yi ya bar ni da y’ar gold d’in tasa, zai tafi honeymoon ya tokare k’ofar yana k’ok’arin lallai sai mun ha’da ido ni kuwa na b’ata fuska ina d’auke kai na na juya baya na koma kitchen d’in. A gaban fridge na tsaya ina duba abinda zan iya ci. Ban yi auneba na ji shi a bayana ya min kyakykyawar runguma yana sakin ajiyar zuciya. A kunne ya rad’a min “Haba K’alb ki tsaya mu yi sallama mai kyau mana, kina kallo tun d’azu ake kirana zan iya missing flight fa…” “d’aure maka k’afafu na yi?” Na fa’da ina janye jiki na. Ya yi narai narai da idonsa da suka tara k’walla ya furta “Ba kyau fa, mala’iku zasu… ki daina yiwa Mijinki tsiwa…” Hancina na gatsine na cigaba da abinda nake. Still ya sake rungumata yana bani wani irin hot romance da suka kusa zautar da ni. A hankali ya janye jikinsa yana mayar da numfashi ido a lumshe ya furta “Allah na gani wannan tafiyar a dole zan tafi na barki, banda Mommy ma ta kafe ni zan iya hak’ura da duk abinda zan samu a wajen aikin…” na tab’e bakina kawai haushi kamar ya kasheni zai wani fake da Mommy Ai dama can ya shirya tafiyarsa yanzu ne zai canja mind d’insa da ya kusance ni ya ji ni dal, ai kuwa zai sha mamaki. “Na bada sak’o anjima za’a kawo Miki, sannan Aliyu zai zo ya dinga koya Miki mota…” “Bana buk’ata.” Na furta ina jan jikina na fice daga kitchen d’in. Ina ji ya saki ajiyar zuciya. Ina zama a gefen gadon ya shigo bedroom d’in jikinsa a sanyaye ya durk’usa har k’asa ya gaida Inna da sanar da ita zai yi tafiya. Inna ta masa fatan alheri sannan ya mik’e sai kallona yake na San so yake mu ha’da ido ni kuwa na fuske. Yana fita Inna taja tsaki ta ce “Yau Naga shegantakar banza, zai yi wannan k’ololuwar tafiyar amma ba zaki raka shi mota ki masa a dawo lafiya ba? Idan wata matar arziki ce ba har tashar jirgin zata raka shi ba. Maza ki mik’e kafin na sab’a miki.” Haushi kamar ya kashe ni haka na fice daga d’akin ko hula babu a kaina. A kujera na ganshi zaune a parlorn ya rik’e kansa. Na tsaya daga gefensa fuskata a d’aure hannu ya saka ya jani jikinsa kafin na ce komai ya manna bakinsa cikin nawa. Tsawon minti biyu kafin ya sake ni ya manna min atm card a hannu na yana furta 5656.. Ya mik’e da sauri ya fice daga gidan. Lumshe idona na yi wasu hawaye da ban san kona menene ba suka zubo min. Ina jin tashin mota fargabata da haushinsa Har ma da mommynsa da matarsa suka k’ara k’ulle ni.hawayen na share sannan na mik’e jiki a salub’e na koma d’aki. Ina ji Inna na magana ban amsata ba na shige cikin bargo hancina sai shak’ar k’amshin turaren Ustaz suke musamman Atm card d’in da ya bani, na lumshe ido na kawai. Wayarsa da ya bar min ta fara k’ara ina dubawa naga sak’o ta turo min. “Na tafi na bar zuciyata a hannunki, duk da ke ce zuciyar tawa… I missed you K’alb, I missed your cutable lips… I missed…. Sai ya saka emojin murmushi ya furta “Kunyarki nake ji ba zan iya fa’dar sunansu ba Amma dai ki kula min da twins d’ina da suke k’irjinki… I love them kana dawo naga komai ya same su…” K’irjina kawai naji ya buga da kalamansa na cillar da wayar gefe a raina na ce yanzu haka itama yana can yana mata da’din baki mayaudari kawai…
Chapter 29 · 0% Book details