← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 49

Sashe 31

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali duka lawyoyin suka gabatar da kansu. Kafin Mammy ta mik’e ta isa gaban Alk’ali ta gabatar da kanta. Mamaki ya kama ni jin Mami zuwa ta yi don ta kare ni. A hankali lawyern mai k’ara ta isa gaba na ta tsaya tana murmushi ta ce “Ayshatu, shaidu da dama Sun bayyana cewa ke kika yi nufin kisan nan ina son kada ki wahalar da shari’a ki amsa laifinki madadin Kwan gaba Kwan baya da kike mana… ki amsa kawai sannan ki jero sunayen abokan aika aikar taki…” Shiru na yi idona a lumshe cikin wani b’acin rai na sake girgiza Kai na a karo na biyu na ce ban san su ba.” Mami ce ta mik’e tana gyara glass d’inta ta nemi izinin Alk’ali wajen yin magana ya bata dama. Har gaba na ta iso ta kalleni sosai irin kallon da take min da ina yarinya idan tana son na kwantar da hankalina… “Ki nutsu Aysha ki amsa laifin da kika San kin aikata kada ki kuskura ki amsa abinda baki aikata ba.” Sannan ta juya gaban Justice ta ce “Ba ta yarda za’a yi a ce Aysha ce ta aikata laifin da ake tuhumarta da aikatawa don kawai an ga hotonta, hoto ba zai zama hujjar kama mutum dumu dumu da aikata laifi ba. A Karon farko idan har da gaske an yi attacking minister me ya Kai ministern gayya tar su wad’anda suka yi nufin kashe shin zuwa cikin hotel d’in? Shin yana da wani deal da su ne? Me ya yi musu suka yi nufin tozarta shi? Abu na gaba akwai mutane a gidan wannan baiwar Allahn, akwai masu aiki akwai wa’danda suke kula da harabar wajen gidan ya kamata a ji ta bakinsu, shin Aysha ta fita a wannan ranar ko bata fita ba?” Alk’ali ya jinjina Kai kafin ya ce “Ina buk’atar ganin maaikatan gidan gaba d’ayansu idan zai yiwu yanzu.” Mami ta girgiza kai kafin ta ce “Na gode, ya mai girma mai shari’a suna nan a waje dama tuni na saka aka zo da su.” Ya yi umarnin a shigo da su. Sai gasu kuwa gaba d’ayansu aka jere su a gaban kotu. Mami ta dinga bin su da kallo d’aya bayan d’aya sannan ta ce “A rana ta d’aya ga watan nan da muke ciki Wanda ya kama sati uku cif fa ya wuce, shin uwar d’akin ku ta fita?” Kusan a tare suka jijjiga kai suka kuma ha’da baki wajen cewa “Ai Hajiya tun ranar da Yallab’ai ya tafi ba inda ta je gaskiya…” Mami ta jinjina kai ta ce “Ko da wannan ya isa Kotu ta yiwa 𝑨𝒚𝒔𝒉𝒂𝒕𝒐𝒖 adalci ta San cewa bata da hannu wajen kisan nan….” “Objection My lord!” Barrister mai kare Wanda ake k’ara ta mik’e “Wannan bai zai zama hujjar da za’a wanke mai laifi ba, saboda ko bakomai za’a iya ha’da baki da masu aikin gidan wajen wanketa daga zargin da ake mata, don haka Alk’ali a yi duba da wannan hoto da aka gani muraran a zartar wa da Ayshatouh hukunci ba don komai na sai don k’ok’arin kisan Kai da kuma b’atawa babban mutum irin D’an Audu suna. Ta hanyar watsa hotunan tsiraicinsa a media…” Alk’ali ya jinjina kai ya yi rubutu kafin ya d’ago yana kallon Mami ya ce ko kina da abin cewa? Mami ta sake mik’ewa ta ce “Ina da shi My lord, ina son a zo da minister nan don shima ya fa’di yarda ya ha’du da su da kuma me ya aikata musu da suka yi k’ok’arin b’ata masa suna… Abu na gaba lallai hukuma ta yi gaggawar kamo wa’dancan masu laifin don su tabbatar da 𝑨𝒚𝒔𝒉𝒂𝒕𝒐𝒖 ce ta aikata laifin idan ba haka ba kotu bata damar tsare 𝑨𝒚𝒔𝒉𝒂𝒕𝒐𝒖 bisa laifin ni da kai da kowa ma muka tabbatar ba ta aikata ba…” Alk’ali ya jinjina Kai ya yi dogon rubutu kafin ya d’ago ya ce “Kotu ta sake d’age sauraran k’ara zuwa 10 ga watan mayu kwana goma kenan cif, kafin wannan lokacin muna umartar duka b’angaren lawyoyi da su zo da shaidun gani da ido Wanda zasu tabbatar da faruwar lamarin ko akasin haka!” Wani irin fa’duwar gaba ce ta riskeni Jin yarda Kotun ta d’au hayaniya kamar me na runtse ido na kafin na Ware su ganin kamar k’amshin Ustaz ne a daf da ni. Shine kuwa yana tsaye ya Zare Shades d’in idonsa yana kallona da jirkitattun idanunsa da suka ka’da suka yi jajur hawaye mak’ale a k’asan idon. Na ji ya sunkuyo kaina. Bai yi la’akari da d’audar da ke jikina ba ya manna min Kiss a forehead a hankali ya ce “Stay Strong K’alb, In sha Allah you will be free…” na lumshe idona kawai hawaye na saukar min. Y’an gidanmu ma gaba d’aya Sun kewaye ni. Suna hawayen Umma ma na tsaye ga Abba da Inna a gefe sai rusa kuka take. Ina ji ina gani Police suka sake tasa k’eyata muka wuce. A hankali na tauna leb’e na ina Jin hucin da zuciyata take fitarwa. Har bakin motar Mami ta je tana kallona tana murmushi ta furta “Stay strong daughter, nothing will happen In sha Allah.” Sauke idona kawai na yi hawayen suna cigaba da zubo min. Ina ji aka ja motar da wata irin jiniya da ta kara’de wajen.

Kashegari kuwa sai ga Ustaz ya shigo wani d’an sanda a bayansa. Ban San me ya gayawa Police d’in ba na ga dai ya juya bayansa. Ustaz ya jani jikinsa a hankali yana ha’de bakin mu waje d’aya. Bayan haka bai sake magana ba illa hoto da ya zaro min. Wasu y’an mata ne su takwas ta tsakiyarsu kam Nima na tabbatar nice cikin shigar English wears da ta fitar da duk shape d’insù. Kana ganin idanunsu ka San kunya ta yi k’aranci. A hankali Ustaz ya ce “Kin san su?” Na girgiza kaina. “Wallahi ban san su ba, ban kuma tab’a ganinsu ba.” Sai na ga ya mayar da hoton ya shiga murza goshinsa ba tare da ya sake magana ba, ya dai manna ni da jikinsa a hankali ya furta “Ya Ilahi! What happened ne?” Shiru kawai na yi a jikinsa. Shi Sam bai damu da yanayin jikina na haka ya sake manna ni da jikinsa ya lalubi bakina ya tura min chewingum d’in da yake taunawa sai Naga ya mik’e kamar ma jiri yake ya fice daga wajen cikin wani irin taku mai bayyana rauninsa. Ban iya komai ba sai lumshe nawa idon da na yi nima ina kokawa da numfashi na da sai naji kwana biyu yana sassark’e min.

Ranar da za’a yi zaman kotun. Ban ita runtsawa ba saboda yarda gaba na yake fa’duwa dalili? Ban san ya shari’ar zata kaya ba. Ban san wani irin hukunci za’a yanke min ba idan aka rasa shaidar da za’a kareni. Hakan yasa na gagara komai sai salloli da na dinga jerawa ba tare da na San adadinsu ba. Hawaye kuwa ina ji da tara nake zai iya cika wani abin.

Ina ji da safe aka sake shigowa aka fita dani. Wannan karan raunin da yake zuciyata ya kasa b’uya sam a tare da ni. Don tun bayan da na sauka a mota idanuna suke zubar da hawaye ga wani matsanancin ciwo da suke min Wanda na tabbatar na yawan kukan da nake ne. Jiri yana d’ibana Amma haka aka shigar da ni cikin inda zan tsaya a wajen shari’ar. Na yi k’asa da kaina bana burin ha’da ido da kowa don a jikina nake jin kamar daga yau rayuwata zata canja. Kamar daga yau iyaye y’an uwa Miji na zasu yi Allah wadarai da halayena… nan da nan aka fara gudanar da shari’ar da yau ina jin duka lawyoyin da zafin su suka zo. Dole aka shigo da mutumin da ya ce mun damfareshi mun kuma b’ata masa suna ta k’ofar baya. Ta k’asan ido nake kallonsa Wallahi ban san shi ba, ban kuma tab’a ganinsa ba ko a t.V ma balle a zahiri. Barrister Mami tana kallonsa fuskarta a tsuke ta ce “Malam, ina ka san waccan baiwar Allahn? Kuma meye ha’dinka da ita da Har suka bika hotel?” Ina kallo ya jijjiga kansa da alama lamarin yana b’ata masa rai ya ce “Sanin abinda yasa na gayyaceta hotel duk bai taso ba don zai iya zama sirrina…” “Ya kuwa taso, tunda a k’ank’antar shekarunta na sha takwas za’a iya cewa ka cuceta ka yaudareta ka saka ta abin da bai dace ba, irinku ne masu lallata tarbiyyar yara, ba mamaki ka nufi yi musu wani mugun abu ne yasa suka aikata maka wannan tozarcin don haka zamu so sanin a inda kuka ha’du da kuma yanayin mu’amalarku ta nan zamu san irin hukuncin da zamu yankewa abinda ta aikata maka idan ma ta aikata d’in.” Kowa ya kalli yanayin Mami a lokacin y’a San cike zuciyarta take da b’acin rai ta yarda lamarin ya kasa b’uya a saman fuskarta da ma idanunta gaba d’aya. Kaftawa iya kaftawa aka yi a wannan rana Amma D’an Audu ya k’i bu’de baki ya amsa laifinsa na jan yara k’anana hotel ya dai ce damfararsa dama suka shirya yi shi yasa suka aikata masa haka, yana kuma rok’on kotu ta masa adalci akan abinda aka masa. Abubuwa suka damalmale k’arshe sai da Alk’ali ya buga guduma sannan kotun ta samu bak’uncin shiru… Ya yi gyaran murya ya ce “A yau kotu zata zartar da hukuncin da take ganin ya dace, Kotu ta kama Aisha da laifin…….” “A dakata ya mai girma mai shari’a!” Aka fa’da daga bak’in k’ofa gaba d’aya idanun mutane suka koma can. Police suka shigo da wasu matasan y’an mata duka fuskokinsu a rufe aka k’araso da su, idanu suka koma kansu ni kaina kallonsu nake da son sanin su wanene? Cikin daka tsawa Police d’in ya ce “Ku bu’de fuskokinku kafin na ci Ubanku!” Suka hau yaye fuskarsu illa d’aya daga cikinsu da ta k’i bu’dewa, Har sai da Police d’in ya saka hannu ya yaye mata fuskarta idanuna suka fa’da cikin nata a tsorace a wani irin yanayi muka dinga nuna juna….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 47…..

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.
Chapter 31 · 0% Book details