Sashe 43
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yanzu ma zaune nake a cinyarsa ina aikin murza gemunsa shi kuma idonsa a lumshe. Na ce “Ka fa’da min Ustaz yarda aka yi a karo na uku aka sake d’aura min aure da kai?” Idonsa ya lumshe yana murmushi bayan ya ha’da goshina da nasa ya ce “Ko Karen hauka ne ya cije ni dama ba zan sake ki ba AYSHA, ke ce wayonki ya kasa nuna miki wasa ake da hankalinki…. Kowa gudun b’acin ranki yake shi yasa Abba ya ce mu biyo Miki ta wannan hanyar a gwada a gani ko kina so na, idan har baki damu ba da niyyar auren Humaira da na yi to tabbas ba kya so na, sai muka ga kuma sab’anin haka. AYSHA ta shiga tashin hankali marar misali. Ba abinda ya fi bani dariya halin da kika shiga da kika ga Mamuda a matsayin mijin da zaki aura ranar ni da Humaira sai da cikinmu ya kusa k’ullewa don dariya.” Turo bakina na yi duk da nima abin yana bani dariya sai dai yanayin yarda suka dinga tunzira ni sai na ji zuciyata ta hasala na saka masa kuka. Ja na ya yi jikinsa yana furta “Easy mana madam, tsokanarki nake, ki bari na baki labarin yarda komai ya canja mana.” Na lumshe ido na ina rungume a jikinsa ya fara bani labari.
Tun sanda court ta wanke ki daga zargin da take miki, da na hango irin kallon tsanar da kike min sai da k’irjina ya buga. Don na San tabbas kallo ne da yake nuni da sai na rama duk abinda ka min. Ban sake tashin hankali na ba sai da Naga kin min kallon ‘d’iban karan mahaukaciya k’in watsar kina tauna leb’enki cike da tsiwa.
Ban sake sarewa da lamarin ba sai da na biki gida nan ma na ga Babu wata mafita don kin k’i saurarata. Haka na koma gida gwiwata a sanyaye. Mommy na gani a parlor don haka da sauri na zube a kujerar da take kusa da ita. Ta dubeni cike da tausayawa don tun afkuwar lamarin ina hango tsananin tausayi na a idanunta, musamman ganin bana cin abinci bana walwala sam. Lawyoyi iri iri na nema k’wararru don su saka hannu a shari’ar Amma suka ce ba ruwansu ba zasu iya wannan shari’ar mai sark’ak’iya ba. Tunda lamari ne na manyan k’asa minister da kansa babu wanda kuma bai San shi wajen tsaurin rai ba, yana iya sawa a kashe mutum kuma ba abinda za’a yi. Mommy ta dubeni cike da tausayi ta ce “Yayansu ya shari’ar ta kasance?” Murya ta a dashe na ce “Ta yi Free Mommy, sam bata da hannu a duka wannan abubuwan daga wannan Har wancan wata ce can daban mai kama da ita, da ake zaton twins ne.” Mommy ta waro ido tana furta “Are you serious Yayan su? Idan kuwa haka ne da wani ido zan dubi yarinyar nan? Hasbunallah!” Na ja ajiyar zuciya na ce “Ba ke ba ma Mommy, ni kaina kallon tsanata nake gani muraran a idanunta, Ban ga kuma laifinta ba, tunda a sanda abin y’a faru kowa ya kasa mata uziri.” Mommy ta ce “In sha Allah zata zama mai halacci a gareka ba zata juya maka baya ba Yayansu, amma ni kam bani da bakin da zan tareta na nemi afuwarta kunya ma ba zata bar ni ba.” Wannan dalilin ne yasa har yanzu baki ga Mama tazo ta miki magana ba.
Haka na dinga zaryar zuwa wajenki kina k’in fitowa har Usman ya bani shawarar na rabu da ke Har zuwa sanda zaki huce don kan ki. Don yanzu kam zuciyarki a zafafe take wajen son ganin kin yi ramuwar gayya.
Na k’i bin shawarar Usman na dangana ga Abba. Shi ma exactly irin shawarar Usman ya ba ni. Hankalina ya sake tashi gani nake kamar na sake rasa ki Har abada. Don haka na dinga yiwa Abba Aiken manyan mutane Har Abba ya gaji ya bada shawarar yarda aka yi. Abba ya san ba takardar saki
Na baki ba takarda ce kawai mai d’auke da kalaman soyayya. Ba kuma wani Humaira da zan auri Cousin d’ina ne ya ganta wqta rana ya raka ni wajenta ya mak’ale yana son aurenta don haka Abba ya b’ullo da wannan dabarar muka dinga wasa da hankalinki…” turo baki na yi alamar shagawab’a na ce “Shi kuma waye wannan mutumin?” Ustaz ya yi dariya sosai kafin ya ce Manager na ne na companyn shinkafa duk muka shigo da shi don a sake b’atar da hankalinki. Ban tabbatar kina so na ba sai da Naga yarda hankalinki ya tashi akan an ce Miki Humaira zan aura. Ba Wanda baki bawa dariya ba a parlorn ganin yarda taurin kan ki zai saka ki rasa abinda kike so, saboda miskilanci. Duk abinda kike yi sau tari Humaira tana min vedio ta tura min, na dariya na yi dariya na tausayinki na tausaya miki. Yanayin da kika shiga a asibiti da kika ga Mamuda shine abinda yafi bani dariya ina kallon yarda kika dinga wurga masa kallon tsana zuciyarki na harbawa don ana gani ta k’irjinki yarda take harbawa da sauri sauri. Miskilanci da nurk’ufanci AYSHA bai yi ba ki rage kin ji K’alb?” Huci na furzar ina masa hararar wasa na ce “Amma Allah ya sani kun wahlar da ni iya wahalarwa kun kuma
Bawa zuciyata matsananciyar wahala don ko barci gagara ta ya yi Allah ne ya yi da kwana na a gaba.” Ahmad ya mintsini kumatuna ya ce “Ba wanda ya ja miki sai miskilacin ki, yanzu alal misali ace wannan mutumin aka baki ya .za ki yi?” Na runtse ido na kafin na furta “Ba yarda zan yi, sai dai na San tabbas zaman aure da shi zai iya zamowa ajalina wallahi murus zan iya mutuwa.” Ustaz ya yi dariya ya ce “Na san yarda zuciyarki take son auren mai kyau don haka na ha’daki da shi, sai ga shi kin fa’di jarabawar warwas!” Na mik’e daga cinyarsa ina turo baki.
Nazeefah★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….64.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
*Gagara gasar masu gasa, tsohuwa kuma fasihiyar marubuciyarku HABIBA ABUBAKAR IMAM IKARA ta sake yunkuro mu ku da wani shahararren littafin ta wanda babu nadama a cikin tafiyar, KUSANCI , littafin da zai zamo gagara tsara, littafin da ba'a taba zuwa da irin salonsa ba, tafiyar ta na da nisa mikakkiya ce wacce na ke son duk wani masoyin littafan Hausa da masoyin Yar Gidan Imam ya shigo ayi tafiyar da shi, ku yi sauri ku shigo gidan kusanci domin samun abinda zai tafi da dukkan damuwarku. Maza ku biya kudin karatunku domin morewa wannan labarin ta wannan asusun 2083086009 Habiba Abubakar Imam UBA BANK Naira 1000 daya ne kacal amma ga bonanza ga mutane dari da zasu fara biya zasu biya nera 500 ne kacal kafin ya koma asalin farashin sa sai ku yi tururuwa ku shigo domin ku ci garabasar bonanzar, za ku tura shaidar biya ga wannan lambar 08033484021 ko kuma 09069067488.*
*Mun gode.*