Sashe 36
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alk’ali ya girgiza kai ya ce “Atine, muna sauraron ki. Ko zargin da ake Miki ya tabbata ne kamar yarda yaran suka fa’da babu kowace alak’a tsakaninku dukkansu y’an tsintuwa ne?. Da sauri Atine ta d’aga Kai ta zubawa SHANY idonta da suka bayana tashin hankalin da take ciki. SHANY ta turo bakinta tana karka’da ido cike da tsiwa. “Y’an tsintuwa ne?” Muryar alk’alin da ya yi magana ta kara’de kotun Atine ta d’aga kai hankalinta tashe ta furta “Haka ne.” Alk’ali ya jinjina kai Kotu ta b’arke da hayaniya da k’yar aka tsawatar aka samu suka shiru. Alk’ali yana kallonta ya ce “Ikon Allah! A wani gari kika tsinci Har mutane 35? Banda wa’danda baa sani ba? Musamman waccan da tayi kama da wancan baiwar Allah. Don haka ake tunanin suna da alak’a mai k’arfin gaske, ko zaki gaya mana inda kika tsinceta?” Idonta ta kai kaina inda Alk’ali ya yi pointing da yatsarsa. Hankalinta tashe ta waro ido wani irin gumi ya dinga tsatstsafo mata. Alk’ali ya dubeta ya ce “Muna jin ki Atine kuma zancen gaskiya muke so. Sab’anin haka kamar kina rub’anya hukuncin da za’a zartar Miki ne. Gaskiyarki ce hanya mafi sauk’i da zata sauk’ak’a miki hukuncin kotu.. k’arya kuwa itace zata tsundumaki kogin nadama da dana sani….” Ido ta runtse tun daga nesa nake hango yarda k’irjinta yake hawa da sauka, murya a raunane ta d’ago idanunta da suka fara ambaliyar hawaye ta ce “Kamar yarda na fa’da, da gaske nake wasu tsintar su na yi wasu asibiti na same su wasu kuma siyar min aka yi….” ihu aka shiga yi a Kotun… da k’yar aka tsawatar “nima a k’ark’ashin wata mata nake, Wanda ita aikinta kenan safara da satar yara mata don tana fataucinsu zuwa k’asashe daban daban idan Sun girma. Asibitoci take bi wajen samun yara jarirai ko marasa galihu ta siya ko ta sata ko kuma wa’danda iyayensu suka Mutu ta hanyar accident aka rasa makusantansu Har gidan marayu tana ha’da baki da mutane ta yi adopting yara. Ni kaina a irin haka ta same ni, ma’ana ni shegiya ce. Duk abinda ta kashe maka kana yaro sai ta ninkasu sau d’ari kafin ta barka ka samu y’anci. Ko dai ta mayar da mutum karuwa ko tayi fataucinka zuwa wata k’asar. Idan kuwa shekarun tsufa suka zo maka sai ta sallameka kaima ka kafa naka gidan karuwan. Don tana fa’da ba’a aikin banza a kano. A irin haka ni ma na fito a cikin wa’danda aka sallama na kama gidan kai na sai na tsunduma irin harkar da take yi na shahara sosai Har na so na fita. A asibiti nake zagaye na siyo jarirai da ku’d’ade masu daraja a cikin k’asashen Nigeria. A irin haka wata rana yawo na ya kai ni jihar kano inda na isa Har asibitin Nasarawa. A ASIBITIN NA SIYO SHANY, hannun wata mata da ba zan tab’a manta fuskarta ba, ana ce mata FAD’IMA……
Daga Abba har Umma a wane irin firgice suke kallon matar Umma da k’arfi ta ce “Asibitin Nassarawa? Wane rana kuma wane kwanan wata?
Tab gwarama!
Wash Allah na na sha dogon typing don haka Har da na gobe🤣🤗.
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA…..51
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Kotun zuwa lokacin tuni ta d’au hayaniya da cecekucen jama’a da suke ta yi ba k’akkautawa da k’yar aka samu bak’uncin shiru bayan buga gudumar Alk’ali. Umma a razane ta cigaba da kallon matar ita kanta bata San lokacin da ta yi wannan furucin ba murya a sama ta sake maimaita maganar tata, har sai da Alk’ali ya tsawatar mata. A hankali ta ce “A ranar lahadi 17 ga watan july 2000 wata irin razana UMMA ta yi tana nuna ta da yatsa ta furta “Na shiga uku, kada kice min wannan yarinyar
jinina ce don ranar da na haifi Aysha kenan!” Gaba d’aya kallo ya koma wajen UMMA shi Kansa Abba jijjiga kai yake ni ma duk na bi na ru’de don exactly ranar da aka haife ni kenan. Alk’ali ne ya dakatar da Umma da take niyyar zuwa wajen Atine da k’yar aka samu UMMA ta zauna hankalinta tashe tana sake nuna Atine Harka. Ni kaina bugun zuciyata a lokacin ya k’aru sosai ba abinda nake sai zaro ido, glass d’in ma na ajiye sa. Alk’ali ya ce “Muna Jin Ki Atine wacece ta siyar Miki da Aysha?” Ta yi shiru har sai da ya sake daka mata tsawa sannan ta ce “Idan har ban manta ba sunanta Fa’dima ko Hajiya Fateema…” na dinga nanata sunan kamar mai son sanin ya ake fa’dar sunan, bakomai nake tsoro ba sai kada abinda zuciyata take tunani ya zama gaskiya, kada dai ace Mami na itace Fateemah da ake zargi. Ina ji UMMA a hankali ta ce “Ba yafiya tsakaninmu a wannan karan Fateemah matuk’ar na tabbatar da saka hannunki a cikin sace min jaririya.” Na d’ago ina kallonta itama na samu kallona take tana furzar da numfashi hankalinta tashe ta d’aga min kai. “Haka nake nufi Aysha, matuk’ar na samu Maminki ce da aikata wannan abin da gaske ba zan yafe mata ba, shari’a ni da ita har Kotun k’oli.” Zuciyata ta dinga wani irin tsalle cikin tashin hankali na dinga addu’a a raina kada Allah ya tabbatar da wannan lamari…. Alk’ali ne ya ce “A ina zamu sameta? Kafin mu ji su kuma sauran a inda kika samo su.” Ta girgiza Kai a hankali tana fincikar leb’enta ta ce “Ba zan ce ga inda take ba a yanzu dai kam, Amma idan na ganta tabbas zan shaida ta.” Bayan rubuce rubuce Alk’ali ya yi jawabi kamar haka. “Dole ne duk inda take ki gaya mana, kafin zuwan wannan lokacin za’a cigaba da rik’eki a kurkuku ba tare da zab’en tara ba. Samun matar da kuma zuwa asibitin wajen bincike ranar da aka haifeta da wacece ta haifeta idan ma baa samu Matar da ta siyar Miki ba na tabbata zamu samu record na wannan ranar In sha Allah.” Umma ta mik’e da sauri tana kuka ta ce “Wallahi ranka ya da’de y’ata ce wannan idan baku yarda ba aje asibiti a yi gwajin k’wayar halitta (Genetics) zaku tabbatar da haka.” Shiru Alk’ali ya yi kafin ya yi rubutu ya d’ago yana kallon UMMA ya ce “Duk wannan zai biyo daga baya, saboda kada ki manta har yanzu mai laifi ce ba zai yiwu mu naku ita ba. Alfarma guda zan muku shi likitan yazo ya d’ebi samples nata, da sauran duk abinda ake buk’ata aje a yi gwajin daga ranar da aka dawo kotu aka tabbatar taku ce za’a baku ita bayan hukuncin da Kotu ta zartar a kanta.” Jikin UMMA ya yi sanyi sai kallon SHANY take da dukkan idanunta da suka ka’da suka yi jajur. Ganin yarda hankalinta yake Neman fita daga jikinta sai kawai na damk’a hannunta cikin na Abba. Shi Kansa sam hankalin nasa kamar ya yi nisa daga jikinsa Amma haka ya yi k’ok’arin rik’e mata muka fita waje. Bayan UMMA ta sake fashewa da kuka ganin yarda aka fita da SHANY, itama Shanyn tana waiwayenta.
Koda muka isa gida jikina a sanyaye nake jan k’afata. Bakomai yake dagula min lissafi sai tunanin MAMINA. Fatana kada Allah yasa Mami tana da hannu a cikin wannan abin da zan iya kira son zuciya. A raba d’a da Uwarsa a ranar da yazo duniya…. Idan har ya zama da saka hannunta a ciki ya makomar Mamin zata kasance? Wasu hawaye masu zafin gaske suka dinga bin idanuna.
★★★
Haka na kwana da zancen a zuciyata. Da safe ko karyawa ban yi ba na nufi Umma da zancen. Da ido ta dinga bina da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya ta ce “Tunani na yazo d’aya da naki, da na Abbanki ma duka. Shima zargi da hasashen da yake kenan. Sai dai zan kwab’eki kamar yarda shima na kwab’eshi. Kada ku kuskura ku furta wannan zancen ga kowa har sai gaskiya ta bayyana, kada a zo a sake jin kunya don ba lallai ne abinda muke tunanin ya zama haka ba. Amma ya rantse wannan karan idan ya samu Fateemah ce silar salwantar yarinyar sa ba zai yarda ba sai ya yi shari’a da ita. Ba zai mata sassauci ba. Burinsa kawai a yi gwajin k’wayar halitta ya samu k’wakwkwarar shaida a kotu…” A hankali na ja numfashi na fesar murya a raunane na ce “Kai jama’a! Wallahi duniya abar tsoro ce.” Umma ta jinjina kai kawai. Na gyara zama na ce “Umma don Allah zan je gidan Ahmad akwai wasu kaya na da books da nake son na d’auko.” Ta d’an kalleni kafin ta ce “Ahmad d’in ai yana nan gidansa mai kallon gidan nan, ki masa magana mana ya kawo miki, balle ma meye na d’ebo kayan ke da zaki tattara ki koma gidanki, ko shikkenan kina nufin kin barwa Kishiyarki Mijinki kenan?” Na turo baki na kamar yarda na Saba ya zame min jiki na ce “Ni fa Umma ba zan koma ba, don Allah ki bar ni na je yanzu zan dawo.” Ta d’an kalleni sai kuma Naga ta saki ajiyar zuciya ta ce “Ai shikkenan, sai ki buga waya ki sanarwa Mijinnaki ko ki gayawa Abbanki zaki fita don ni dai ba zan baki izini ba kin sani.” Na marairaice fuska na ce “Allah Umma yanzu zan dawo. Baba driver ne ma zai kai ni.” Umma ta kafe ba zan fita ba sai na sanar da Ahmad ta mik’a min wayarta “Maza ki tura masa text, ai ba a garin mahaukata muke ba.” Dole na tura masa message. Sannan Umma ta barni na fice da sauri.
Ko Drivern ban nema ba, don ba gaskiya na gaywa Umma ba, ba wani gidan Ahmad da zani gidan su Mami na zan tafi. Na k’agu an gano koda. Saka hannunta a ciki.