← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya hau girgiza kai yana furta “Ni ne zan Mutu AYSHA, ni ne kuma a cikin bala’i don bana jin zan iya kwatanta Adalci a tsakaninku, ina tsoron ranar k’iyama na tashi da shanyayyen b’arin jiki. Ba ki ji yarda zuciyata take bugu, ina tsoro AYSHA, Allah ne da kansa ya umarcemu da mu yi adalci tsakanin matanmu. Ya sanar da mu idan Har ba zamu iya ba to mu auri guda kacal. Abinda Har yanzu mazan yanzu suka kasa ganewa wallahi AYSHA ba a adalci, don haka maza da yawa zasu tashi da shanyayyen b’arin jiki. Ina cikin tsaka mai wuya AYSHA ban san menene mafita ba? Ya ya zan yi?” Ya fa’da yana runtse idonsa a hankali ya kai tafukan hannayensa saman k’uncina, kafin ya ware idon yana kallona hankalinsa a tashe. Idanunsa sun ka’da sun yi jajur da alama furucin nasa Har k’asan zuciyarsa gaskiyar maganar kenan. Ni kuwa kuka nake sosai kuka mai bayyana uk’uba da tsananin da zuciya ta take ciki. Kukan nake sosai shi kuma ya kasa rarrashi na ya dai zuba min ido har wayarsa ta fara ringing. Idanuna na kai kan wayar na ga an saka MY WIFE 2… da sauri na janye ido na daga kan wayar ina jin yarda zuciyata take fusga da k’arfin gaske. Numfashina yana shirin sark’ewa kai da gaske kishi bala’i ne musamman idan kana son mutum. Janye jikina na yi da sauri na fice daga d’akin. Ustaz bai biyo ni ba hakan yasa na shige nawa d’akin na zube a saman gado ina kokawa da numfashi na da na ji yana neman d’aukewa. Tsawon mintuna biyar na ji ya turo k’ofar d’akin. Ina jin sa ya zauna a gefen gado. Kafin ya saka hannu ya shafi fuskata “Ta shi K’alb, magana za mu yi.” Na bu’de idona a hankali ina kallon cikin idonsa da suka nuna galabaitar da zuciyarsa take ciki. Leb’ensa ya d’an fusga cikin kammalalliyar murya ya ce “Ki yi hak’uri tamu k’addarar kenan, ki min addu’a kuma Allah yasa na iya kwatanta adalci a tsakaninku ko da a fili ne, don na San a zuciya dai kam ba ni da iko da hakan. Zan tafi ga wata dattijuwa can Mommu ta aiko Miki da ita zata taya ki zama. Da ku’di da komai a drawer zuwa jibi da yamma zan dawo nan, amma gobe ma zan shigo mu gaisa, amma don Allah ki saka Hijabi idan na Miki waya zan shigo.” Wani yawu na ha’diye mai kaurin gaske. Wani abu na ji y’a cunkushe min a zuciyata. Ban san sanda na rik’e hannunsa ba ina murzawa da k’arfin gaske na saki kuka ina furta “Pls Ustaz kada ka tafi ka bar ni, wallahi zuciyata ba zata jure ba. Za ta iya failing.” “Ba zata yi ba AYSHA, ki daure ko wace mace da haka take sabawa. Ba a kanki aka fara kishiya ba, ki dinga tuna haka sai ki samu sauk’i a zuciyarki.” Ina kallo Ustaz ya janye hannunsa ya tafi da saurin gaske. Ban san sanda na runtse idona ba don tsananin kuka idona har yaji ya fara. Shikkenan Ustaz ya tafi wajen Hameeda zai mata abinda yake min, zai mata soyayya za su kwanta tare su yi wanka tare kamar yarda muke yi…” Na ji zuciyata ta buga da k’arfin gaske.

Ni ce Har k’arfe ukun dare ina kwance a haka Sam na kasa runtsawa tun bayan da na je wajen Baba Atine wacce Mommy ta kawo min na bata abinci da wajen kwana, sai na dawo na yi kwanciyata cikin wani irin tunani mai wahalar da zuciya. Har a lokacin zuciyata Imagining Ustaz take a gadon barcin Hameeda suna romancing juna. Ban san sanda na furta kalmar “Na shiga uku” a fili ba. Yanzu haka zan yi rayuwar aure da Ahmad muna sharing d’insa da wata, haka kuma zan dinga ji a duk sanda Hameeda ta karb’i girki? Na dinga jin kamar zan Mutu. Anya zan iya kuwa?

Na d’au wayata ina duba lokaci. Ganin k’arfe uku bai hana ni kiran Mami na ba. Tsawon lokaci tana ringing kafin Mami ta d’aga da alama ma barci take don muryarta ta bayyana hakan. “Baby lafiya? Kira a tsohon daren nan, Allah yasa dai lafiya.” Cikin shashshek’ar kuka na ce “Mami na, na kasa barci, zuciyata ciwo take ga kai na ya yi nauyi.” Mami a rud’e ta ce “Subhanallah, Shi Ustaz d’in yana ina? Kuka zauna baku tafi asibiti ba?”

Na sake sakin kuka da k’arfin na ce “Mami ya tafi wajenta.” Cikin ki’dima Mamin ta ce “Ita wa?” Na sauke ajiyar zuciya na ce “Matarsa Hameeda.” Mami ta saki ajiyar zuciya ta ce “Wallahi Baby kin bani tsoro. Idan har na fuskanci matsalarki bakomai ke walagigi da ke ba sai kishi, Ya kamata kuwa ki ajiye shi a gefe, duk da an San yana da ciwo Amma yana zuwar wa mutum a inda ya d’auke shi. Idan ka d’auke shi da zafi zai zo maka da zafi, idan ka d’auke shi da sauk’i yazo maka da sauk’i. Don haka ina so ki dauke shi da sauk’i kamar yarda kika ga ni da Ummanku mun d’auke shi da sauk’i. Sai hakan ya zame mana alheri. Kada ki ba mu kunya.” Na runtse idona ina k’ok’arin sakawa kaina nutsuwa sai dai abin ya gagara na ce “Wallahi Mamina ba zan iya ba, kowacce mace da yarda Allah ya halittar mata nata kishin, ni Allah ya yi yo ni cikin mata masu tsananin kishi.” Cikin tsawa Mami ta ce “Za ki iya AYSHA, kowacce mace da kika gani koya ta yi kuma ta iya Har ta Saba. Don haka ba dalilin da zai saka ke kika sa iyawa, sai dai idan kin sakawa kanki son zuciya. Mata nawa aka yi wa kishiyar kuma suka zauna lafiya.” Fashewa na yi da kuka jin fa’dan da Mami take min madadin rarrashi. Hakan da ta ji ne ina ji ya saka ta tausasa harshenta ta ce “AYSHA, saurare ni, yi shiru haka, maza ki tashi ki je ki yi alwala ki yi sallah, za ki samu sauk’i a zuciyarki, kin ji? Maza tashi.” “To” na ce a sanyaye ina zame wayar daga kunne na na shige toilet.

Cikin k’arfin hali na yi alwala kafin na fito na fuskanci alk’ibla na tada ik’ama. Ina sallah Ina hawaye ina rok’on Allah ya saka min nutsuwa a zuciyata ko na samo na tsallake wannan jarrabawar. Tabbas wallahi Babu maganin kishi a duniyar nan irin addu’a. Don na samu sauk’in zuciyata daga cikin kaso d’ari na b’acin rai na kaso talatin ya tafi. Sallahr da na yi na samu nutsuwa sosai sai ga shi barci ya d’auke ni mai nauyin gaske. Akwai magani sosai a cikin Sallahr dare maganin damuwa da b’acin rai da duk wani k’unci da aljihu da na zuciya. Allah ka bamu jumurin yin k’iyamallaili.

K’arar waya ne y’a farkar da ni daga nauyayyen barcin da ya d’auke ni. Ina kai duba na kan wayar na ga an saka REALITY. Na d’an d’auke kai na ina kokawa da abinda na ji yana son dawo min. Ban d’aga wayar ba na ajiyeta a gefe na mik’e zuwa toilet. Cikakkiyar alwala na d’aura na fito na yi Sallahr asuba na koma na kwanta.

Cikin barci na dinga jin hannayensa suna yawo a saman fuskata. Na bu’de idona da suka min nauyi a hankali ina zuba su a kansa. Tas da shi ya yi wanka ya yi wani fresh da alama ya yi kwanan nutsuwa ni ya barci cikin kwanan b’acin rai. Hakan yasa na mik’e fuskata a d’aure na shige toiket na banko k’ofar da k’arfin gaske Har da murza lock. Wanka na yi sosai na fito daga ni sai mitsitsin towel, dangwaliliya zan masa tunda har wani ce min yake na saka Hijab idan zai zo. Gashi na a baje yake sosai a saman wuya na. Har da y’ar wak’a ta na isa gaban dressing mirror na zauna. Ina kallo Ustaz yana ta sakin murmushi daga zaunen kafin ya kasa hak’uri ya mik’e ya iso inda nake zaune ina ta laila ya mai a cinyata.

Zuro kansa ya yi ta baya na, yana goga hancinsa a wuyana yana shinshina a hankali ya ce “Baki missing d’ina ba ne K’alb, ina can duk kewarki ta dameni na rasa sukuni gashi ba dama na kira ki ina tare da Hameedah, amma gaba d’aya hankalina na kan ki. Idan na kira ki kuma zai zama kamar cin fuska ne…” ture shi na yi a jikina ina turo baki na. Don haushi ma maganar tasa ta bani. Wato sanar da ni yake tare suka kwana da matarsa kenan? Kamo hannuna ya yi ya manna ni da jikinsa ya rungume sosai. “Tsaya na samu nutsuwa AYSHA.” Da sauri na sake ture shi daga jikina ina furta “Ina ruwanka da ni, tunda kai ka yi kwanan farin ciki ni kuma na kwana da ciwon zuciya.” Murmushi kawai ya saki yana lotsa hannunsa cikin kumatu na ya furta “Kwantar da hankalinki K’alb, daga yau Ahmad ya zama naki ke ‘d’aya ba maganar sharing da wata. Ban baro gidan ba sai da na saki Hameeda, don bana son na cuceta ko na ci amanarta.” Na zaro ido don gulma na furta “Saki kuma? Why Ustaz?” Ya ‘d’aga min gira yana lumshe ido ya ce “Bana daga cikin mazan da zan iya adalci, ina kuma tsoron ha’duwata da Allah da shanyayyen b’arin jiki, shi yasa na zaunar da ita muka fahimci juna na bata dukiya mai yawa kafin na saketa, ina fatan hakan da na yi yasa ya zamo alheri gareta ta kuma fahimceni. Alhamdulillah kuma ta fahimceni kamar yarda iyayenta suka fahimceni haka Mommy ma tana fatan Allah yasa hakan ya zama alheri garemu baki d’aya. Amma fa na mallaka mata dukiya da kadara mai tarin yawa.” Lumshe ido na yi kawai wata dukiya da ya mallaka mata duk bata dameni ba. Wani irin sanyi na dinga ji a zuciyata sai dai haka kawai sai na ji sakin bai min da’di ba. Duk da dai ban sani ba.
Chapter 44 · 0% Book details