Sashe 37
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan karan Mama da fara’a ta tare ni Har mamaki abin ya bani. Duk wannan d’acin ran da bak’in ciki Babu shi. Mami na kuwa tashi ta yi ta rungumoni sosai jikinta tana furta “Oyoyo Ayshatu na.” Ni dai murmushin yak’e kawai nake saboda yarda zuciyata take dukan tara-tara. Daga haka Mami ta jani cikin d’akinta har da turo k’ofa muka zauna a gefen gado. Kawai na ji Mami ta jefo min tambaya. “Ayshatu y’a aka k’are da zaman kotu? Wannan karan ai k’in zuwa na yi tunda Naga kin yi free na ce me zan je na yi..” D’an murmushi na jefeta da shi. Zuciyata na sake kambama zarginta da nake. Murmushin nawa San bai kai zuci ba na ce “Ai kuwa Mami da kin sha kallo, SHANY dai ana zaton ni da ita Twins ne, don rana guda aka haife mu, a kuma asibiti guda…” Da sauri Mami ta zaro ido ta ce “In ji Uban wa kuma?” Na gyara zama cike da mamakin firgicin ta na ce “In ji matar da ta raine su ita ta fa’di inda aka yi tazo hannunta, matar ta tabbatar da cewa siyanta ta yi a asibitin bisa jagorancin wata mata…” A hanzarce ta ce “Wata mata kuma? Wacece ta fa’di sunanta?” Na yi shiru ina nazarin yanayinta kamar dai tun yanzu zuciyata na son tabbatar min da zargi na. Na jinjina kai na ce “Ta fa’da mana, sunanku d’aya da matar da ta ce ta yi hanya an siyar mata da y’ar.” Wani irin kallo naga Mami tana min kafin ta mik’e tana zagaye d’akin hannayenta sak’ale da bayanta. Jikina ya yi sanyi k’alau ko Mami bata fa’da ba na San tana da hannu dumu dumu a cikin wannan lamarin. Wata k’walla ta kawo ido na. Na mik’e ina d’aukan handbag d’ina. Na k’arasa gabanta idanunta a lumshe suke na ce “Mami zan wuce.” Da k’yar ta bu’de idanunta da suka juye lokaci guda ta d’an lashi leb’enta ta ce “Ki gaida gida AYSHA.” Ta fa’da da wata irin murya da na rasa yarda zan kwatanta. Ina fita na ratsa bayan gidansu Mami na zauna na ci kuka na sosai don na San Mami ce da wannan laifin bana haufi.
Sai da naje k’ofar gida Sannan na tuna k’arya na shiryawa Umma akan zan je d’ebo kaya. Hakan yasa na juya na nufi gidansu Asma da sauri. Ashe rabon na yi mugun gani don Ustaz na gani tsaye da zank’alak’ok’in matarsa a daidai k’ofar gidansu da alama fita za su yi. Muka yi four eyes da shi. Wani abu na ji ta tokare min k’irji. Na zabga masa harara na shigesu ba tare da na musu magana ba. Muryarsa na ji a daf da ni yana furta “Ban yafe fitar da aka yi ba da izini na ba.” A masife na juyo na masa wani irin kallo mai nuna bala’in da zuciyata take ciki ba. D’aga min gira ya yi yana lumshe ido ya ce “Abinda na ce kenan Mara kunya.” Wani yawu mai d’aci na ha’diya na kasa furta masa komai saboda takaicin da yake cike da zuciyata. Kuma muddin na tsaya zan iya saka masa kuka a wajen ni kuma ban shirya zubar da aji na ba. Don haka na wuce fuskata a d’aure na fa’da gidan su Asma. Ina jin zuciyata kamar ta fito don tsananin zafin kishi tabbas na yarda da gaske kishi masifa ne, don haka na sake damk’e wa a raina ba ni ba gidan Ustaz Har abada. Da na koma gida Umma bata ce min komai ba ganin kaya na da gaske a hannu na.
Bayan kwana biyu. Sai ga Abba ya shigo gida a yammacin ranar hannunsa d’auke da takarda ya same ni da Umma a kitchen ya mik’a mata ta dubesa da sauri ta ce “Na menene?” “Result d’in genotype ne ya fito…” Hannun Umma na rawa ta fara bu’de takardar…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….57.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Akwai a arewabooks masu nema dafa farko.
Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni, fa’duwar gabar da ta saka ni jin matsanancin ciwon kai. Na kasa gane a wani mahalli zan saka abinda Abba ya ce. Tashin hankalina bai sake yawaita ba sai da Naga Ustaz ya zato jotter da biro da alama cika umarnin Abbà zai yi. Tsaf na daina fahimtar abinda ake cewa Amma miskilancina ya kasa bari na na ‘d’ago na ce wa Abba na janye buk’ata ta. Ina kallon Ustaz kuma ya yi rubutun fuskarsa d’auke da wani yanayi da na rasa mahallin da zan ajiye shi farin ciki ko bak’in ciki. Ya mik’awa Abba takardar yana furta “Ku taya ni murna y’an uwa da karamcin Abba ba abinda zan sakawa da Abba da shi sai addu’a. Abinda ya yi AYSHA Ai shi ya yi Humaira kamanninsu guda ba wani banbanci na gode sosai.” Abba ya ce “Bakomai Ahmadu, ka cancanci fiye da haka, sam ba zan so na rasa ka cikin zuri’ata ba. Allah ya yi muku albarka.”
Tamkar wani magana’disu haka idanuna suka game da idon Ustaz kawai sai naga ya d‘aga min hannu ya saki murmushinsa mai kyau. Da alama manufarsa sai wata rana. Zuciyata ta buga da k’arfin gaske wannan shi ake kira da yiwa kai Me na janyowa Kaina Ni AYSHA? Ina miskilanci na ya kai ni yau?
Jikina a salub’e na mik’e Har jiri nake ji na shige gida zuciyata na harbawa da saurin gaske. Zuciyata a cunkushe da tunani ina tunanin tabbas wata mak’ark’ashiya Ustaz ya shirya min. Wato yaga Humaira ta fi ni wayewa ta fini faran fatan shine dalilin juya a kalar soyayyata zuwa tata. Sam bana ganin laifin abinda na aikata ni balle na hango kuskurena. Don kuwa ko sonsa zai kashe ni sai dai ya kasheni don ba zan tab’a nuna masa na damu koda hakan zai zama Ajali na tabbas miskilanci bai yi ba. Wani irin yawu na ha’diye mai kaurin gaske, sai a sannan hawaye suka shiga suntiri a k’uncina. Na fara kamar jin haushin Humaira da tsanarta a zuciyata tamkar laifinta ne, tamkar ita ce ta ce tana son sa. Kowa ma na gidan haushinsa nake ji tuni dama na yarda Umma tafi son Humaira a kaina don yanzu janta da take a jiki na bata ja na. Ni kam ai na yi rashin mai k’aunata Mami na. Na zaro waya da sauri don kiran Mamin nawa amma still wayarta not reachable hakan yasa na mayar da alamar kiran nawa zuwa Mamanً ta. Ta d’aga muka gaisa na tambayeta Mamin nan take sanar da ni ta wuce England karatu kwana biyu da suka shige Amma zata turo min numberr da ake samunta ta can.” Jiki na a salub’e na kashe wayar ina goge zufar da na ji tana tsatstsafo min a goshi na. Ashe wancan lokacin ban ga komai ba yanzu ne NA GA RAYUWA NI AYSHA. Har dare ban fito ba haka na kwanta da yunwa ruwan tea kawai na sha. Ba Wanda ya nemeni har Umman.
Da Humaira da Khadija da Maryam muke kwana d’aki d’aya wani lokacin Humaira ta gudu d’akin Umma. Su kuma sauran biyar d’in suna d’akinsu da yake b’angaren Mami.
Har asuba ranar ban yi wani barcin kirki ba, ina salloli. Shi yasa da barcin ya d’auke ni y’a d’aukeni da k’arfin gaske. Hayaniyar su ce ta farkar da ni daga nauyayyan barci kaina na ji ya sarà ganin yarda suke ta hayaniya suna shiryawa. A tsawace na ce “Malamai kun dameni fa, kun hanani barci.”
Humaira da tsallenta ta dirò saman gadon tana jan bargon. Cikin masifa na ce mata “Ke meye haka?” Langab’r kai ta yi. Kafin ta furta “Sissy, kin manta da batun zuwa potiskum d’in, ki shirya kada Su Yaya su tafi su barki ni a motar Ustazu na zan tafi.” Wani kallo nake mata ina jin kamar na k’unduma mata zagi wato da iskanci ma da sunan da nake kiransa take kiransa. Sai dai na ha’diye ina jan tsaki na ce “ku je kawai, ni ba zan je ba.” Bata ce komai ba ta fice daga d’akin. Tsawon lokaci sai gata Sun dawo da Umma. Umma ta kira suna na ni kuwa na yi shiru kamar mai barci. Sai na ji ta ce “Humaira mu je barcin ne a kanta. Sa zauna da masu aiki.” Na bi bayan Umma da suke ficewa daga d’akin da kallo. Wato abinda na lura da shi sam Umma bata damu da ni ba balle ta tambayeni damuwata. Na datse leb’ena ina jin raunin zuciyata na sake rub’anya.
Na mik’e a hankali na shiga toilet wanka na yi sosai kafin na fito na hau shafe shafe a jikina. Abinda ban cika yi ba yau nice har da kwalliya ba don komai ba sai don na burge Ustaz, don ban ban sani ba ko kwalliyar SHANY tana daga abinda yake janye hankalin Ustaz d’in.
Na shirya cikin black abaya mai masifar kyau kalar kuma ta amsheni sosai kalar light pink da adon black stones a jikinta. Ni kaina na San na yi kyau ba d’an ka’dan ba. Fuskata kuwa sanye nake da wani black shade da ya sake fito da kwalliyar tawa. Ni kaina sai da na sake duban kaina a mudubi kafin na saki murmushi don na San ba Ustaz ba duk Wanda ya ganni sai ya yi mamakin kwalliyar da na zauna na rincab’a.
Ina fita kuwa suka zuba min ido suna furta Wow Ma sha Allah. Na d’an d’aiuke kaina bakina nake d’an motsawa ina tauna chewingum d’in da yake cikinsa.
Motar Ya.Usman na bi, don ko da wasa nan nufi motar Ustaz ba. Jan aji da shan k’amshi na ba zai bar ni na aikata hakan ba. Shima ina kallo sau ‘d’aya ya kalleni bai sake ba, Ya tattara dukkan nutsuwarsa ya mayar kan Humaira da take ta masa surutu da dariya shima kuma ina kallon yana mayar mata da murmushin kamar dama jira yake.