← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sanda muka isa madina wani irin sanyi na dinga ji a zuciya ta. Musamman gani na ga ni ga kabarin Manzon Allah. Ban san sanda na saka kuka ba. Haka ma a makka da muka je ka’aba. Shima kuka na dinga yi ina yiwa duka dangina addu’a. Sannan na tsananta addu’a akan Allah ya daidaita Abba da Mami su dawo da aurensu don shine abinda na fi so fiye da komai a yanzu. Ustaz siyayya yake jibgawa duk inda kuma yaga kayan baby siya yake, sai ya ce wai ya san nan da 8 months ya d’Au babynsa “Allah Ameen.” Na ke cewa a zuciyata don nima ina son na ga Baby amma ni nafi son namiji shi kuma Ustaz ya fi son mace. A gida kuwa babu Wanda ya nemeni, sai dai Ustaz ya dinga ce min Sun yi waya da wane yana gaishe ni.” Tab’e baki nake in ce “Shine basa nema na.” Ustaz ya yi k’asa da muryarsa yana furta “Sun San kina can kina karb’ar lamari mai girma wajen Ustazun ki ya za’a yi su neme ki Madam?”

A yi hak’uri remain few pages mu k’ark’are In sha Allah.

Nazeefah★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….63

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Na turo bakina kawai don ni sai na ji abin ya bani haushi. Ustaz dai bai yi min magana ba ya ja bakin kawai ya mik’e ya fice daga bedroom d’in yana dariya k’asa k’asa.

Kashegari Ustaz shi ka’dai y’a fita don a kwana biyun da suka gabata wani matsanancin zazzab’i nake fama da shi ga amai da jiri. Shi kansa Ustaz d’in ba inda yake zuwa sai masallachi. Ina zaune ni ka’dai na zuba tagumi da hannu bibbiyu ba abinda nake tunani sai yarda rayuwa ke juyin waina. Da yarda lamarin duniya ya zama abin tsoro. Tabbas na amince da cewa duniya ba matabbata ba ce. Babu komai a cikinta sai ru’dani. Rayuwar yanzu ta zama abar tsoro yau gareka gobe ga waninka. Duniya ta rikice masu ku’di kawai ke jin da’dinta yayinda talaka ke cikin wata irin rayuwa babu abinda ya dace ga bawa irin ya nemi kusanci ga Allah. Ya tsaya ya jajirce wajen bautar Ubangijinsa. Idan bawa ya yi hakan fak’at ya gama, sai ya tattara ya mik’a dukkan lamarinsa ga Allah ya yi addu’a Allah yasa ibadar da ya yi karb’abbiya ce. Saboda ba Wanda ya san ranar mutuwarsa Amma kam a wannan k’adamin da ake ciki sakankancewa ba ta bawa ba ce, wallahi duniya ta zo k’arshe. Kada ka manta da mak’asudin da ya saka aka halicceka don ka bauta wa Allah ne ba don ka shagala ba… wannan tunanin da na yi sai na ji hankalina ya tashi. Tsoro ya cika min zuciya ba tsoron komai ba sai na mahaliccina. Hawaye suka dinga ambaliya a idona. Na lumshe ido na kawai ina jin saukar su. Ban san sanda ya shigo d’akin ba sai ganinsa na yi durk’ushe a gaba na, ya dafe duka cinyoyina yana kallona cikin tashin hankali. Cikin wata irin murya ya ce “Me ya faru K’alb? Ko ciwon ne?” Na girgiza masa kai na. Ina k’ok’arin tsayar da hawayen ido na Amma na kasa. Ustaz bai fasa matsa min hannuna ba cikin sigar lallashi ya ce “Tashi mu je asibiti, da ina da iko da na mayar da wannan ciwon jiki na K’alb.” Kumatunsa na Shafa na ce “Ba ciwo ba ne Ustaz, tuno wa da tabbas za’a Mutu za’a ha’du da Allah shi ya d’aga min hankali, ina kuma tausayin Wanda bashi da shi a wannan halin da ake ciki na rashi a duniya mai ku’di ne kawai yake walawa.” Ustaz ya saki ajiyar zuciya, Ya lumshe idonsa ya ce “Da wannna tunanin nake kwana nake tashi AYSHA, kuma duk wani mai imani dole ne y’a dinga tuna mutuwa ha’duwa da Allah, da azabar kabari. Wallahi a duk sanda na tuna lahira na tuna akwai hisabi akwai wucewa ta kan sira’di na kan samu kaina da rasa duk wata nutsuwata, ina fatan Allah yasa mu dace. Wannan halin da mutane suke ciki kuwa bakomai ya dace garemu ba irin mu koma ga Allah mu nemi tuba da tsark’akakkiyar niyya mu k’udirce a ranmu tuba ne muka yi shi na Har abada ba zamu koma ga zunubi ba, idan muka aikata hakan tabbas zamu samu sauk’in wasu lamuran.

Gaba d’aya jikin mu ya yi sanyi, ranar ko siyayyar da Ustaz ya yi ban duba ba. Haka muka zauna shiru sai da la’asar ta yi sannan muka tafi harami. Bama dawowa dama sai An yi sallah Isha’i. Amma yau yarda jikina ya matsa min a haramin yasa ba shiri Ustaz ya tattara ni zuwa asibiti.

Dubawar farko da aka min, likita ya tabbatar da samuwar ciki a mahaifata na watanni biyu. Wata iri murna Ustaz ya dinga yi don Ban san sanda na ji ni a cikin jikinsa ba cikin tsananin farin ciki ya rungume ni. Yana furta “Alhamdulillah, bi ni’imatihi tatummussalihat..” ni kuwa murmushi kawai nake saki cikin matsananciyar jin kunyar likitan da duk Wanda yake wajen. Wai ni AYSHA ni ce da ciki na haihuwa a jiki na. Haka Ustaz ya ja hannuna cike da tausayawa muka fita zuwa harabar asibitin. Nan ma tsayar da ni ya yi a cikin hasken futilu ya saka duka tafukan hannayensa ya tallafi fuskata yana murmushi ya furta “Sorry K’alb, how I wish zan iya mayar da cikin nan jiki na da dukkan lalurar da yake saka ki. Amma ki saka a zuciyarki ibada kike. In sha Allahu za ki samu rabo mai girma a wajen Ubangiji.” Na lumshe idona kawai farin ciki yana sake cika min zuciyata. Da gaske na yi dacen Miji na bugawa a jarida na kerewa sa’a kuma. A hankali na furta “SHUKRAN LILLAH!”

Sati guda muka k’ara jirginmu ya d’aga da mu zuwa Nigeria.

Cikin walwala nake saukowa daga jirgin zuciyata cike da murna da zakwa’din ha’duwa da y’an uwana.

Gaba d’aya ahalin Babanmu da na Baban su Ustaz suna tsaye a wajen jiran passenger. Wani irin farin ciki ne ya mamaye ni hango su da na yi Sun zo tarar mu. D’aya bayan ‘d’aya suka dinga rungumeni har Mommyn Su Ustaz. Ina jikin Ta na ji an ja hannuna ina juyawa na ga wata mata mai nik’ab ta rungumeni a jikina na San Mami na ce tun kafin ta bayyana kanta gare ni. Da sauri na d’age Nik’ab d’in ban san sanda na saki ihu ba na ce “Mami na!” Ta ce “AYSHA ta!” Na daka wani tsalle na ce “Allah yasa addu’a ta ce ta karb’u.” A hankali na ji Ystaz ya ce da Mami “Maminmu ta yi a hankali ba ita ka’dai ba ce.” Mami ta sakar masa dak’uwa ta ce “Ahmad ni kakar ka ce.” Murmushi ya yi yana sosa kai ya bar wajen. Nan kuwa Humaira ta tasa ni a gaba da tsokana sai da Mami ta tura ta wajen Umma tana furta tafi wajen Uwarki kafin ranki ya b’aci ba zaki wahalar min da y’a ba.” Humaira ta turo baki ta ce “Ni wai Mami me yasa kike min haka?” Mami harararta ta yi kawai. Yaya Faruk ne ya ce “AYSHA ina mijin naki Alhaji mai tumbin Naira?” Gaba d’aya suka saka dariya ni kaina dariyar nake. Na isa wajen Umma itama na rungumeta. Murmushi kawai ta yi tana furta “y’ar gidan Mami an dawo lafiya?” Humaira ta ce “Har na hango sanda kike wani irin huci idan kin ganni..”. Na kai mata duka da sauri ta isa wajen Mommyn Ustaz ta b’uya a bayan ta tana furta “Taimake ni Mamanmu.”

Har muka isa gidana ina jikin Mami Ina sangartar da na da’de ban yi ta ba. Ita kuma sai ririta ni take yi.

Tunda aka bu’de wawakeken gate d’in nake binsa da kallo. Wani irin gida ne mai kyawun gaske da ya sha farin paint da adon bak’in k’arafa da k’ofofi da winduna. Ba k’aramin tafiya da Imani na gidan ya yi ba. Shuke shuken da suke gidan sun matuk’ar sake k’awata gidan. Daga gefen wajen parking space muka yi parking. D’ayan gefen kuma wani k’ayataccen garden ne da ya yi kyau sosai. Hannuna cikin na Mami na muka shiga gidan da ban san yaushe Ustaz ya gina shi ba. Kyau da tsarin gidan kam ba’a magana. Kamar Ustaz ya san irin gidan da nake mafarkin Mijina ya mallaka kenan. Sai gashi Allah ma ji rok’on bawa ya cika min duka burina na duniya sai dai fatan dacewa da samun tagomashin Aljanna.

A babban parlorn gidan aka baje ana ta zuzzuba abinci. K’amshin abincin ne ya ishe ni na mik’e da sauri na shige wani bedroom da yake can lungu. Mami ce ta biyo ni don dama Mommyn Ahmad da Ummanmu basu zo gidan ba.
Chapter 47 · 0% Book details