← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 49

Sashe 20

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda muka fita karatun kur’ani kawai ya saka cikin suratur rahman har muka je bai ce min komai ba, nima ban ce masa ba. Sai da ya yi parking a babban parking space d’in gidansu na saka hannu zan bu’de k’ofar na jita a kulle. Juyowa na yi ina kallonsa idonsa ma a lumshe yake na ji yana furta “Idan kin shiga kuma, ki yi behaving like mara kunya kamar yarda kike min a gida, ba ruwana ke zaki zama mai bak’in jini a wajen dangin Miji da Uwarsa…” Turo baki na yi na furta “To ina ruwana sai me?” Waro ido ya yi kafin na ji ya jawo ni da sauri jikinsa duk da k’ok’arin k’wace wa da nake sai dai ya ha’da bakina da nasa ya min wani irin tsotsa a gaggauce yake murzar leb’ena da nasa bakin yana romancing jikina cikin wani irin gigitaccen yanayi. Ban wani hanasa ba don da haka nake son cin galaba a kansa. Sai da ya yi son ransa sannan naga ya sake ni ya kifa kansa a saman sitiyari, yana mayar da numfashi ya furta “Gobe ma ki sake saka jambaki idan zaki fita kin ji?” Ya fa’da cikin wata irin murya. Shiru na masa ina kallon yana danna wayarsa ya saka a kunne bayan an d’aga wayar. “Fito maza ki shiga da ita Habibteey akwai inda zani.” Ya kashe wayar yana min duban k’asan ido, ya furta “Kin jawo ba zan iya shiga cikin mutane a haka ba, dole za’a gane ni, wai ke dole sai kin ja ra’ayi na shine har da saka jambaki da turare ko?” Ya fa’da yana sake kai kansa k’irjina ya shinshina da kyau ya furta “Duk mace mai saka turare dai idan zata fita Manzon Allah ya tsine mata.” Na ture kansa a jikina ya d’ago yana kallona cikin tsare gira ya ce “Don’t tried it again, duk sanda kika sake ture ni daga halak d’ina you will see what I do, mara kunya gantalallen jikin naki ma..•” Isowar Khadija ne yasa ban mayar masa da martanin maganarsa ba, na yi sak ina kallonsa hakan ya saka ya hura min iska a fuska bayan haka ya manna min kiss a gefen kumatu a hankali ya furta “Be a good girl, don’t behave like….” Sai naga ya yi tsaki ya bu’de k’ofar na ce “Ka k’arasa mana.” Hannu na da Khadija taja cikin farin ciki ne ya hana ni k’arasa maganar, ta rungume ni tana furta “Oyoyo Anty Ayshan mu.” Na d’an yi murmushi kawai ina kallo Ustaz ya fito daga motarsa ya nufi ainahin chalet inda d’akunansu suke. Khadija ta ja hannuna muka shiga cikin gidan, tana ta min surutu da nuna min jin da’dinta da gani na da ta yi. Ta ce “Ina ta son zuwa Anty AYSHA, Bro ne ya hana ni zuwa wai bai gama cin amarci ba zan zo na dameku da surutu.” Murmushi kawai na saki ina mamakin shegiyar k’aryar Ustaz.

A yarda Mahaifiyar su ta karb’eni na san sam bata yi farin ciki da zama na surikarta ba, ta dai amsa gaisuwata ta ce a kawo min drinks Daga haka bata da’da bata raga ba, lamarin da ya sanyayar min da zuciya na dinga jin kamar na saka kuka, na tuna wancan lokacin da nazo da ta dinga yin kamar ta mayar da ni cikinta. Ban wani jima ba Ustaz ya yiwa Khadija waya ya ce ta fito da ni zamu tafi. Ina kallon wani banzan kallo da Mommy ta min da ina mata sallama ta ce “Allah ya bamu alheri.” Na fice jikina a sanyaye na bi bayan Khadija da itama na lura sam bata ji da’din abinda Mommyn ta yi ba. Don a hanya ta ce min “Sai hak’uri AYSHA, kin san lamari irin wannan…” na d’aga mata kai ina sakin fake smile.

Tunda ya mayar da ni gida ban sake ganinsa ba tsawon kwanaki shidda, sai dai hankali na bai wani tashi ba musamman da na tsinci wata takarda a saman dinning da ku’di a kai ya rubuta “Ko zaki buk’aci wani abu, kada ki neme ni na yi nisan kiwo.” Na ja tsaki na yaga takardar ku’din kuwa ko kallonsu ban yi ba.

Ranar da ya kwana shidda da tafiya ina kwance wajen 11:30 na dinga jin nocking a babbar k’ofar shiga parlorna. Na mik’e jikina sanye cikin atamfa ban damu da tambayar waye ba don na san ba zai wuce Ustazu ba. Na saka hannu na mur’da handle d’in sai idona ya fa’da cikin na Asma k’awata. Da murmushi ta ce “Amare, kun yi wuyar gani, koda yake yanzu Uwargida sarautar mata zan ce.” Sam ban gane furucinta don haka na tab’e baki na ce “Asma yanzu idonki kenan?” Ta ha’de rai tana furta “Kya ce haka mana, yaushe rabon da ki neme ni ko a waya.” Na tab’e baki na ce “Ina naga wata waya, ni Ai yanzu ba ni da waya haka nake rayuwa kamar wata y’ar prison, ya su Mama?” Ta ce “Haba dai, har yanzu wai kina nufin baki da waya?” Na d’aga mata kai ina d’an murmushi sai naga ta saki ajiyar zuciya ta ce “AYSHA ya kika ji da fargabar kishiya kuma? Ni fa wallahi na zata ke Ustaz ya kai gidan da yake gina wa na kusa da gidanku, ina ta murna zaki sake zama mak’otanmu, wai sai jiya na shiga in k’are miki tsiya kawai naga Ustaz da wata banza a zaune a parlor ta bi ta kanainaye shi, na dinga zare ido ina kallonsu sai na ji ta ce “Zauji wacece wannan? Na ji Ustaz ya ce aminiyar Uwargida ce. Wallahi ban san sanda na fita daga gidan ba a gigice….” “KISHIYA?” Na furta ina kallon Asma? Sai na ga ta yi tsilli tsilli ta ce “Ba dai baki sani ba?”

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA… 40.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387. (WhatsApp only pls!)

Ji na yi k’irjina ya buga da k’arfin gaske, da sauri na saka hannu don na amshi wayar sai dai Mommy bata bani damar hakan ba, ta rik’e wayar gam a hannunta, tana jifana da wani irin kallo da ban isa na musanya mata abinda ta gani, amma cikin k’arfin hali kuma once a rayuwata na tab’a yin k’arya da wayo na dai. Na ce ba ita ba ce Mommy, sharri ake son k’ulla mata…” Ta dubi numberr da aka turo sak’on sannan ta mayar da kallonta kai na ta ce “Shi Shareef d’in ne zai mata sharrin?” Na yi saurin girgiza mata kai, zuciyata na wani irin bugu ga damuwata ta kasa b’uya a idona, na yi nadamar ajiye hoton a wayata d a vedion ma gaba d’aya, na san tabbas sai Mommy ta nemi Shareef don jin gaskiyar lamari. K’wafa naji ta yi ta kuma cilla min wayar tana furta “Mazinaciya kenan zaka aura Ahmad? Ka sani amma so ya rufe maka ido, zaka iya rantse min da Allah wannan ba AYSHA ba ce? Ga kamanninta nan zahiri amma kana son ka raina min hankali, amma wallahi ka bari na tambayi Shareef ya tabbatar min ita ce wallahi ko itace autar maza ba zaka aureta ba, ka ji na gaya maka?” Na ‘d’aga mata kai duk da rawar da zuciyata take yi. Tana fita daga bedroom d’in na yi saurin kiran Shareef a wayata. Tun kafin ya yi magana na ce “Please Shareef do me a favour please..” Shareef da yake ji na ya ce “Wai menene Ahmad, ka gaya min mana.” Na ha’diye yawu da k’yar na ce “Ko Mommy ta kiraka ta tambayeka AYSHA ce a vedion nan ka ce ba ita ba ce ka rufa min asiri, wallahi ba zan iya rayuwa ba Ay….” tsaf furucin baki na ya ‘d’auke ganin Mommy a tsaye a kaina da alama ta ji duk abinda nake fa’da daga kallon da take min mai kama da zata kai min duka. Wata dariya ta yi ta girgiza kanta. “Wato Ahmad ka amince ka saka kanka a bala’i ko? Ka yarda zaka auri Aysha ko da karuwa ce ko? To wallahi sai dai idan ni Uwarka ba na raye, ba shashashar uwa ba ce ni da zan bari a gurb’ata min zuri’a da b’aragurbi, Allah na gode maka da bata kai ga tarewa ba, a yanzu nake son ka saketa wallahi ko na yi maka baki shashasha kawai…” wata irin zufa ce ta dinga zubo min, ban san sanda na isa gabanta ba na zube gaba d’aya cikin rawar murya na ce “Please Mommy don Allah ki rufa min asiri wallahi son AYSHA ne zai kashe ni…” wani kallo ta min ta ce “Sai dai ka mutu kuwa? Don wallahi ba zan fita daga d’akin nan ba sai ka saketa kuma idan ka k’i bin Umarni na zan rok’i Ubangiji ya mana sakayya tsakani na da kai…” Kaina na ji ya wani irin sarawa na runtse ido da k’arfin gaske na ce “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna ina kallon farar takardar da take mik’o min. “RUBUTA Ahmad tun kafin taron jama’ar nan su san me ya faru…” Na dasa biro akan paperr sai dai rawar da hannuna yake yasa na kasa rubutun sai da Mommy ta sake daka min tsawa sannan na rubuta saki guda. Na ninke ina runtse idanu zuciyata na min wani irin suya. Ina kallo Mommy ta fita daga d’akin cikin dishi dishin ido na da hawaye da suke zuba. Na kifa kai na akan gadon ina kuka, a daidai lokacin kuma kika dinga kira na akan na zo na kai ki wajen dinner shine dalilin masifar da kika ji na miki a cikin waya ta gefe guda ke nake jin haushi ina tunanin komai ma ya samu da auren mu ke kika janyo.
Chapter 20 · 0% Book details