Sashe 15
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallona Kawai yake Yana sakin murmushi a hankali kafin cikin sanyin murya ya ce “Idan suka mayar da ke gidan nawa ki fita kin Ji Aysha.” Daga haka ya fice daga cikin sitroom d’in. Ji nayi kamar ana hura wuta a cikin zuciyata na runtse ido kafin na kwarma wani Uban ihu da yaja hankalin mutanen gidan suka shigo inda nake a guje. Umma ta k’araso tana kamani cikin rawar murya ta ce “Ke menene? Me aka miki?” Ban fasa kukan ba ina kallon k’wayar idonta data bayyana tashin hankalin da take ciki. Na ce “Umma ku yi min rai wallahi Ustaz ba don Allah ya dawo na koma gidan da ba, akwai wani kalar mugunta a ransa wanda Allah ne ka’dai ya sani.” Shiru Umma ta yi kafin ta kama hannuna ta d’aga ta ce “Mu je cikin gida, naji me ya ce miki.” Bin ta kawai nake ina sake kukan da nake. A d’akinta ta saka ni kafin ta ja k’ofa ta rufe. Ta dawo inda nake bakin gado ta zauna ta ce “Oya gaya min, me ya ce miki?” Tsaf na gaya mata abinda ya ce min, sai naga ta yi shiru tana girgiza kai, ta saka hannu ta share min hawayen fuskata ta ce “Ki yi shiru Aysha, a dole dama zaki fuskanci irin wannan matsalar daga wajen duk Mijin da zai aureki.” Ta yi shiru tana share k’wallar idonta kafin ta ja hannuna ta matse a hankali da alama duk abinda take son ya fito daga bakinta mai ciwo ne a zuciya… “Duk macen da ta rasa budurcinta a yawon banza AYSHA dole ne ta fuskanci irin wannan k’alubalen a wajen Mijin da zata aura, don haka dole ki jajirce wa ranki kika saka ranki bautar Ubangiji zaki yi ba bautar Ustaz ba, to shine zaki samu salama!” Hawaye ne masu zafi suka zubo min a hankali na ce “Ni fa Umma ban rasa budurci na ba, kuma wallahi babu wani namiji da ya tab’a rik’e min hannu bayan Ustaz to me yasa zaku yi ta jefa zargi na a zuciyarku…shiru fa kawai nake muku ni ban aikata abinda ake zargi na ba, ku yi bincikien mana ku gani…” K’wayar idonta kawai take zagayawa cikin tawa tana kallo na ta ce “A yau d’aya na yarda da ke Aysha don ban hango k’arya a cikin idonki ba, amma abinda na kasa ganewa how comes duk wa’dannan abubuwan suke faruwa, bincike kuma wallahi ana yi daga Abbanki har y’anuwanki da shi kansa Ustaz d’in tunda abin ya faru har yau basu huta ba, k’arshen lamarin ne kawai bai zo ba….Allah ka dube mu ya Allah, Allah yasa kuma abinda kika fa’da hakan yake. Yanzu ki share maganarsa idan kin je gidansa ya tara da ke ya sameki a matsayin cikakkar budurwa anan lamarin zai canja.” Shiru na mata ina sakin ajiyar zuciya “Kin ji me na ce miki ko?” Na ‘d’aga mata kaina yau d’aya sai naji wani sashe na k’uncin zuciyata yana zagwanyewa. Ta mik’e ta fice cikin matuk’ar sanyin jiki.
Shirye shirye sosai ya kankama duk na komawata gidan Ustaz. Duk wani gyara Umma ta min ta saka kuma an ha’da min wasu shegun kayan gyara daga wajen Maman Fareeda mai kayan gyaran aure. Ni da kaina ina jin yarda jikina ya sauya. Wani irin glowing nake na yi kyau ba ka’dan ba. Ustaz ne dai ban sake saka shi a idona ba tun bayan da ya gama gaya min bak’ar maganar da har yau ta kasa barin zuciyata na kuma rik’e a raina da cewa sai na rama wallahi ko ba yanzu ba.
Tsaf aka shirya ni cikin wata zafafffuyar laffaya da ya sha k’amshin turaren gabbasa, duk inda na wuce k’amshi ne, hatta da gashi na baa k’yaleshi ba sai da aka turarashi jikina fa kamar an min b’arin madarar turare. Umma kuwa kana kallon fuskarta zaka san tana cikin tsananin farin ciki.
K’arfe takwas Abba yasa aka kai ni cikin motarsa don da kansa ya ce zai kai ni gidan Ustaz d’in. Tun a mota yake min nasiha bai fasa fa’din. “Bana son a k’ara samunki da wani laifin AYSHA,ki tabbata kin rik’e mijinki da girma da mutunci kamar yarda mahaifiyarki take min.” D’aga kai kawai nake idona bai fasa zubar da k’wallar da take kwarara ba. Har cikin parlor ya kai ni ya zaunar saman Kujera Ustaz da ya shigo da mu ya durk’ushe a gefensa ba yarda Abba bai yi ba ya zauna a saman kujerar ya k’i. Nasiha ya masa sosai a k’arshe ya ce “Ga amana nan Ustaz na baka Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya ya kawar da dukkan abin k’i. Waccan magana kuma da muka yi da kai kada ka fasa ka cika umarnin da iyaye suka baka, Allah ya baku zaman lafiya.” Ustaz ya amsa da ameeen. Abba ya mik’e ina kallo ta cikin mayafi Ustaz ya mik’e don raka shi. Na runtse ido ina jin wutar tsanarsa da jin haushinsa yana sake nuk’urk’usar zuciyata.
Na yaye mayafin laffayar fuskata ina k’arewa tangamemen parlorn da ya sha kayan alatu kallo. Sam ba abinda ya burge ni a parlorn don ba abinda nake so ba kenan. Wancan Karon an shigo ni da ni gidansa da tsananin son sa wannan karan kuma na shigo da tsananin k’iyayyarsa a zuciyata.
Jin takun shigowar sa parlorn na sake Kimtsa fuskata ina hura hanci cikin tsananin fushi. K’arasowa ya yi cikin parlorn ya kuma zauna a kujerar da nake kai. Ina kallo ya jingina yana lumshe ido, kafin naji ya fisgo ni da k’arfin gaske na fa’da jikinsa gaba d’aya ya rungumeni yana sakin ajiyar zuciya a kai a kai. Da sauri nayi k’ok’arin k’wace kai na sai dai bai bani damar hakan ba, ya sake rungumeni sosai idonsa a lumshe ya saka lips d’insa akan nawa yana tsotsa hankalinsa kwance k’ok’arin ture shi nake amma bai bani dama ba a kunne ya ce “Shsssh! Bar ni na Mori sadaki na Malama, naga dai ni na biya wani banza ma….” Sai naga ya yi shiru ya runtse ido a hankali kuma ya fara sassauta rik’on da ya min kafin ya sake ni gaba d’aya ya mayar da kansa jikin kujerar idonsa a lumshe, mik’ewa na yi da niyyar na masa rashin mutunci sai naga idanunsa na zubar da hawaye duk da a lumshen suke k’irjinsa yana sama da k’asa. Hannuna ya ja kafin ya bu’de idonsa a kaina da suka ka’da suka yi jajir. Mamaki ya bani ganin kuka yake sosai. Kallona yake yana murza hannuna yana hawayen still cikin wata irin murya ya ce “Why Aysha? Don Allah wanene wannan mutumin da kika…” naga ya runtse idonsa yana jijjiga kai ya furta “Allah ya isa ya cuce ni, wallahi Aysha ya min illa a zuciyata. Gashi zuciyata ta kasa amincewa na bar ki, me yasa Aysha don Allah?” Tsuke fuskata na yi ina jin wani irin takaici a raina da mamakin kukan da Ustaz yake yi. “Har kika iya sallamawa k’ato jikinki hannunsa a saman abinda nafi so yana latsa su son ransa, na rantse duk ranar da ya bari na yi ido biyu da shi sai na kusa hallaka shi kafin na ha’da shi da hukuma, har yau zuciyata tana mamakin wai ke kika aikata haka?” Iya kufula zuciyata ta kai cika kawai nake ina batsewa na masa banza. Still idonsa a kaina, kafin ya sake burkito ni jikinsa idonsa a runtse yake duk abinda yaga dama da jikina, hannunsa ba inda bai zagaya a jikina ba sai dai idonsa a kulle. A kunne ya ce min “Talk to me, me wancan banzan ya fi ni, da kin bari an kawo ki gida na zan maki soyayya da hot romancing da na tabbatar babu kalarsa a duniya, kin k’arya min zuciyata kin saka min rauni a gabban jikina bani da nutsuwa sam tunda abin nan ya faru, bana iya cin abinci duk k’aunata da abincin, bana iya barcin good 4hours saboda da na rufe ido wancan banzan mutumin nake ga ni, me yasa Aysha ki gaya min yaushe kuka ha’du da shi da kuma me ya rud’eki?.” Ya fa’da yana cusa kansa a k’asan wuya na. Da k’arfin gaske na ture shi ina mayar da numfashi na yi pointing d’insa da yatsa. “Ya isheka Ahmad, kada ka kuskura ka sake kawo kanka jikina, na ji ni karuwa ce ka san da haka me yasa ka dawo da ni gidanka da zaka sani a gaba da surutan banza, sanda abin ya faru me yasa baka same ni mun yi magana ni da kai ba ka kai maganar wajen iyayenmu? Ka tambayeni ka ji na aikata ko ban aikata ba? Ka yi bincike ka ji ni ce ko ba ni bace, meye amfanin tambayar yanzu tunda ka Riga ka yanke a ranka ni ce to amsa guda zan baka Eeh ni ce sai me?” Lumshe idonsa ya yi, yana aikin yamutsa kansa kafin ya furta “Na yi bincike bayan faruwar abin har gidan da aka ce kuna zuwa shai’dananci da daddare na je, na kuma tambayi wasu y’an mata da na nuna musu hotonki suka min shewa suka ce k’warai ke ce har suka sake nuna min wani hoton naki mara kyan gani. Duka wannan ba hujja ba ce?” Na lumshe ido na cikin tafarfasar zuciya na ce “Ni ce Ahmad! And so what?” Murmushi na ga ya yi ya Mik’e ya ce “So nothing, nan gaba kuwa zaki ga something da zai yi hurting zuciyarki.” Ya shige d’akinsa. Ido na bi shi da shi kafin na zauna a wajen zuciyata na tuk’uk’in b’acin rai. Tsawon lokaci na d’auka kafin na mik’e na shige d’akin dana tabbatar nawa ne. Ina shiga na kife a saman gado cikin wani irin matsanancin kuka mai saka tafasar zuciya.