← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 49

Sashe 11

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rik’e wajen ya yi da sauri ganin har jini ya fara zuba, amma hakan bai saka shi ya fasa isowa inda nake ba, yana sakin wani kalar murmushi da na rasa fassarar da zan ba shi. Hannu nake ‘d’aga masa ina furuci a zafafe “Don’t come closer Ustaz ka tsaya inda ka ke I hate you…. I hate you whole heartedly….” Murmushin yake kuma bai fasa isa inda nake ba. Na runtse idona zuciyata na wani irin bugu kamar numfashi na zai bar jikina tsabar masifar da take cin zuciyata. Ina ji ya kira sunana da muryar da na kasa yarda tasa ce. “Open your eyes ki kalle ni, ina son mu yi magana…” Ba zan bu’de ba Ustaz, kada ka saka na maka illar da har abada ba zaka manta ba…” na furta da wani irin rawar harshe “Illa?” Ya furta cikin alamar tambaya hakan ya saka ni ware idona a kansa na ce “Ko kana shakka?” Sai naga ya girgiza kai ya lumshe ido ya waresu duka a cikin second d’in da basu fi na k’irga ba… ya ce “Bana mamaki, Saboda komai aka ce za ki aikata yanzu ba zan musa ba, illa kuma ai kin Riga kin gama min illa da kika bari son ki ya Riga ya shiga raina, duk da yanzu ba son ko ka’dan, am just….” Sai naga ya cije leb’ensa ya saki huci ka’dan na ware idona a kansa cikin masifa na ce “You just what? Ka fa’da mana.” “Ina tausayawa Abba da Umma saboda an rasa mai jihadi ya aureki That’s why na yanke shawarar sake aurenki whether you want it or don’t, kawai zan yi manage na aureki….” “Kan Uba!” Na furta cikin tsabar mamaki “Uban waye ya ce na rasa mai so na?” Murmushin ya sake yi ya kuma murza goshinsa ya fice daga ‘dakin yana sake furta “Am not begging you if you wish ki gaya musu ba zaki koma gida na ba, and so what waye ya zama looser….” Ya fita daga d’akin har da y’ar wak’arsa ta larabci. Wasu irin hawaye ne kawai na ji suna zuba a k’unci na zuciyata na wani irin harbawa ina jin kamar na bi Ustaz na kama shi na yi ta duka ko na huta da zafin da zuciya take yi….. Gashin kaina kawai nake ja ina zagin ustaz a fili da zuciyata Samira ta shigo tana kallona kafin ta zauna a gefen gadon ta furta “AYSHA me ye haka, control your self mana, ko kina son wani ciwon ya kama ki nake?” “Na fi so Samira, wallahi ina so saboda ko zai zama Ajalina I hate this world and all the things around it…..” Na fa’da ina sake fincikar gashi na kamar wata mahaukaciya sabon kamu. Ina ji Samira ta ja ni jikinta da k’arfin gaske ta rungume ta fara karanto min addu’oin da suke bakinta. Da k’yar ta samu ta ji na saki ajiyar zuciya ta ja min pillow na kwanta a hankali. Mik’ewa naga ta yi ta fita sai gata ta dawo da magani a hannu. “Tashi AYSHA ki sha magani..” Bu’de idona kawai na yi ina kallonta ta min alama da kai nuni take min tashi na mik’e a hankali ina dafa kai na da yake wani sara min. Na zauna sosai ta saka min maganin a baki ta saka min ruwa, ina runtse idon na ha’diye maganin.

Ban farka ba sai sha biyu da rabi na dare. Da sauri na mik’e tunawa da nayi ban yi sallahr Isha ba Samira da take waya ta juyo tana kallona ta kashe wayar. Tana furta “Kin tashi AYSHA?” Na d’aga mata kai kawai na shiga toilet da ke d’akin duk zuciyata ba da’di na d’aura alwala na fito. Ko da na idar da sallah har Samira ta kawo min tea mai zafin gaske da shortbread biscuit. “Ki ci AYSHA na san dare ya yi ba zaki iya cin abinci mai nauyi ba.” Ruwan black tea d’in kawai na d’auka na kai baki na na dinga sipping d’insa kamar magani ina runtse ido na. Samira dai sai kallona take da k’yar na sha Rabin cup na ajiye ina lumshe idona saboda yarda nake jin zuciyata ta yi nauyi kamar wacce aka sakawa dutse. Turo k’ofa muka ji an yi Anty Khadija ce ta shigo idonta a kaina ta ce “Kin tashi AYSHA sannu.” Na d’aga mata kai kawai. Ta zauna da k’yar saboda cikin ta da ya fara girma ka’dan. Ta dafa ni tana furta “Ki daina yawan damuwa AYSHA, kada ki causing ma kan ki wani problem d’in. Samira ta gaya min duk abinda ya faru, abinda nake so da ke ki saka nutsuwa a ranki, ki cire tunanin komai idan Ustaz kome yazo nema ki amince kawai kin…” Wani kallo da na wurga mata ne ya sa ta ha’diye Sauran maganar ta mik’e jikinta a sanyaye tana furta “Shikkenan, Allah ya zab’a mafi alheri.” Ban amsa ba illa mayar da kaina da na yi na sunkuyar. Zuciyata na zafi ni fa gani nake duk wanda zai ce na koma gidan Ustaz baya so na baya k’aunata. Samira ce ta taso ta kama hannuna muka hau gadon ta kwantar da ni. Sai da ta ga na lumshe ido sannan ta ce “AYSHA ki yi hak’uri da abinda zan ce miki, amma wallahi kada ki yi sake Ustaz ya kufce miki, don ya ha’du ta kowane fanni ga kyau ga gayu ga ku’di ga ilimi to me ake so a wajen namiji bayan wannan, ni idan nice wallahi a yau Zan hak’ura a mayar mana da auren tab irin fa mazan nan wahala suke wallahi…” “Tunda kina son sa ke ki aure shi, amma bari na gaya miki wannan karan na shirya fito na fito da duk wanda ya ce sai na komawa auren Ustaz koda kuwa iyaye na ne….” Samira ta ware ido tana kallona. Kafin ta ce “Da gaske AYSHA? Iyayenki fa kika ce?” Lumshe idona kawai na yi ban tanka mata ba, amma a k’asan zuciyata ina gasgata abinda baki na ya furta. Ina kallo Samira ta ja pillow ta kwanta tana furta “Allah ya kau da fitina to.”

Sai da aka yi sati ana shan shagalin bikin su Ya Usman, zuwa wannan lokacin kullum Anty Khadija sai ta fita daga gidan kullum Ustaz kuma sai yazo gidan Yaya Muhammad amma koda wasa na k’i yarda ya ganni. Sau d’aya na tab’a hangoshi ta window gefen fuskarsa da plaster da alama inda na ji masa ciwo ne. Na yi tsaki Ina sakin labulen na furta “Ina ma idon na cire maka, mugu kawai!” Anty Khadija da ke baya na ta furta “Da kin cuci y’ay’anki, don dai na san tabbas shine Uban y’ay’anki.” Guntun tsaki na ja kawai na furta “Anty Khadija bana son irin wannan maganar.” Gani na yi ta saki murmushi kawai ta fice daga d’akin. Na bi bayanta da harara saboda yawan zuwansa har na k’agu na koma gidan mu. Don Yaya Muhammad ma duk masifarsa ya gaji ya k’yaleni ganin ba zan tab’a saduda ba.

A daren ranar da na kwana goma a gidan Yaya Muhammad ina kwance d’akin da nake Ayra a gefena sai surutu take. Anty Khadija kuma tana parlorn Yaya Muhammad. Turo k’ofa na ji an yi ina d’aga ido na ga Yaya Muhammad ne kafin na gyara kwanciyata ya matsa yana kallon Ustaz ya ce shigo gata nan.” Da sauri na mik’e ina gyara mayafin abayar da ke jikina. Na b’ata fuska sosai kamar ban tab’a dariya ba. Gefen drawerr na kalla sai naga yajin da naci waina yana nan. Murmushi na saki a raina na ce yau zaka san baka da zuciya. Yaya Muhammad ya juya hannunsa d’auke da Ayra tana yiwa Ustaz gwarancin da alama har ta saba da shi. Ina gani ya mik’a mata Bounty chocolate sai naga ta saki dariya suka fita da Daddyn ta. Zama ya yi a kujera k’waya d’aya da take d’akin ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana k’are min kallo. “Mara kunya…” ya furta cikin wata murya mai bayyana k’asaitarsa. Muryata a dake na ce “Ka tashi ka fita!” “Idan na k’i fa? Me zaki min?” Wani murmushi na saki ina gyara zama na na ce “Zai fi maka sauk’i ka tashi ka fita wallahi, kafin an aiwatar da abinda na shirya…” shiru ya yi bai fitan ba sai dai ya kafa min ido yana cije leb’ensa ya ce “Gaisuwar ma kin manta yarda ake yin ta?” Na zo fa iya wuya don haka na kasa amsa masa, sai furzar da huci nake. “Ba kya ji ne AYSHA?” Jijjiga k’afata nake yi kawai zuciyata na ayyana min na watsa masa yajin kawai. “Ki sassautawa zuciyarki AYSHA ki nutsu magana nazo mu yi ba tashin hankali ba..”. “Ba zan sassauta ba Malam, bari na gaya maka kada banzar zuciyarka ta fara Kimtsa maka ka mayar da aure na, wallahi zaka yi nadamar hakan matuk’ar nadama…” cikin mamaki Ustaz yake kallo na ni kuwa na masa funfurun fus sai masifa nake masa. Bai yi min magana ba naga ya mik’e ya fita k’ofa jikinsa a sanyaye, na zabga tsaki ina tashi na rufe k’ofar har da murd’a key. Sai sannan wasu hawaye masu zafi suka zubo min. Na zauna kawai ina dafa k’irjina da naji ya matsanta min da bugu.
Chapter 11 · 0% Book details