Sashe 28
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muna zuwa Office d’in y’ansanda suka tasa ni a gaba da tambaya. Tambayoyin da suka dinga saka zuciyata wani irin harbawa da k’arfin gaske. Har ban San sanda na runtse idona na furta “Ko ke ake tuhuma ta ni na aikata a yi min hukuncin da ya dace…” Tsit station d’in ya yi ina kallon Yaya Usman da su Abba suka runtse idonsu. Sam ban damu da tashin hankalin da suka shiga ciki ba damuwata a yanzu bata wuce ta barin duniya ba. Na gaji da rayuwar gaba d’ayanta. Dpo ya k’ura min ido ya ce “Kika ce ke ce kika aikata?” Na d’aga kaina kawai ba tare da na yarda na kalleshi ba. Ya ce “To ina sauran y’an uwa naki su bakwai da aka ce tare kuka aikata?” Na datse leb’ena da k’arfin gaske na ce “Ban San inda suka tafi ba…” ina kallo ya yi rubuce rubucensa yana kallon wasu y’an sanda mata guda biyu ya ce su je da ni su tuhumeni sosai na fa’di inda sauran y’an uwa na suke. Suka kuwa ingiza k’eyata muka tafi. Tambayar duniya da izayar duniya ba wacce basu min ba Amma na ce ban San inda suke ba. To ina zan sani tunda su kansu ban san su ba, asalima ban tab’a ganin fuskarsu ba, ban sani ba ko Aljannu ne suke siffata su aikata son ransu. Ba yadda za’a yi na yarda Biladama ne, saboda idan ana kwaikwayar fuskar mutum, ba ta yarda za’a yi a kwaikwayi komai da komai na jikin mutum ace hatta da farce ba banbanci. Abu d’aya da na tambayi kaina, me na yiwa Wanda ya min wannan sharrin da yake son ganin baya na? Aka ajiyeni a cell cikin kyakykyawan matakin tsaro da ba a barin kowa ma ya ganni. Ina ji Dpo na yiwa Abbana bayani “Alhaji ba Wanda zai sake ganinta sai ranar shari’a, ku nemar mata lawyer kawai.” Ina kallo Abba da Yaya Useey suka saka hannu suka share k’walla suka bar wajen. Na ji wani irin Abu ya tsaya min a mak’oshi. Tun daga ranar kuwa ban sake ganin kowa ba har tsawon kwana uku kafin zuwan lokacin kuwa na ji gata sosai, jigatar da ta bayyana har a saman idona. Ranar ina zaune a d’akin mai duhu sosai na dinga Jin murya kamar ta Ustaz tana dumfaro d’akin. Ina Jin muryarsa sama sama yana furta “Wallahi, idan ba’a sameta da laifin komai ba, sai na yi shari’a da Dpo d’inku… matata za’a tozarta don wulak’anci kuma ance mutumin da ake zaton an kashe d’in ma bai Mutu ba, to saboda me ba zaku saketa ba?” Ban ji amsar da wancan ya basa ba, naga dai an bu’de k’ofar Ustaz ya shigo tun daga fuskarsa har gangar jikinsa Sun bayyana tsagwaron tashin hankalin da yake ciki. Idanunsa tuni suka ka’da suka yi jajur. Ya fara cizon leb’ensa yana k’arasowa inda nake, ya zube a gabana murya a sark’afe ya ce “Ke ce a haka K’alb?” Kuka yake sosai ya kama hannuna ya ce “Sai jiya labari ya isar min wai an kulleki a station, how come Aysha da gaske ke ce a jikin hoton?” Na runtse idona tunda abin ya faru sai lokacin naji kuka yazo min Amma na yi dakiya na share na k’i kukan muryata a raunane na ce “Idan ka yarda nice a Hoton shikkenan ba abinda zan ce sai ni na aikata su yi min abinda ya dace Ahmad…” Murzar hannuna kawai yake ya kasa furta komai sai huci da yake furzarwa goshinsa sai fitar da zufa yake, ya ce “I wish I was dreaming….. bana son wannan abin ya zama gaskiya, kin fita ne da ba nan?” Ban amsa ba illa rufe idona da na yi kawai ina kokawa da numfashi na da naji yana fita ba daidai ba… Ustaz muryarsa a k’asa ya furta “Stop it Aysha! Na yi alk’awarin ko duka dukiya ta zata k’are sai na wankeki daga wannan laifin…. Zan kuma tsaurara bincike har sai na hango waye ya Miki wannan sharrin…” Da sauri na girgiza Kai na ce “Ba na so Ahmad, ka bari kawai su min duk abinda ya dace, ba Wanda zai ce ba ni ba ce a jikin hoton nan don haka wahalar da kanka kawai zaka yi…” Kuka na saki sosai, kukan da tuntuni nake son yinsa bai zo ba sai yanzu… na dinga kukan har Ahmad ya jani jikinsa bai damu da dau’dar da take jikina ba ya manna min Hot kiss Wanda hakan yasa naji zafin zazzab’in da jikinsa ya d’auka… Da k’yar ya cikani sanda aka zo aka ce lokaci ya cika. Ya harari d’an sandan sai kuma ya mik’e yana tsane hawayen da suke zuba masa a ido. Na bi bayansa da kallo hawayen na cigaba da yi min suntiri a idona. K’irjina ya min nauyi sosai kamar an saka min block ten inches a kaina.
ZAMAN KOTU (COURT)….
Kaina a k’asa yake saboda na kasa yarda na ha’da ido da dandazon jama’ar da suke zube a court d’in. Hannayena duk a gark’ame da handcuffs. Lawyoyi ne birjik a gaban court d’in sai a sannan nake jin ma mutumin da aka kusa kashewar aka kwashe musu American dollars wai Minister ne.
Shigowar Alk’ali ne yasa court d’in ta samu bak’uncin shiru.. hakan yasa na d’an d’ago kaina na saci kallon jama’ar da suke court d’in. A gaba na hango kaf yayyena sai Ustaz da yake saye cikin jallabiya idanunsa da black shades fuskarsa ba walwala ko ka’dan. Na d’auke idona a Kansa ina Jin zuciyata na sake k’arfafa min tsanar aurensa ba don komai ba ina tunanin silar Auren nasa muka rasa duk wani farin ciki a gidanmu. Ba mamaki da ban ha’du da shi ba duk wa’dannan ibtila’in ba zasu same ni ba. Al’kalin na kalla sai Naga na San shi mutumin Abba na ne sosai don Abbana ma Alk’ali ne kafin ta ajiye aikin da kansa… Alk’ali ya gabatar da kansa kafin lawyoyin mai k’ara da na wa’danda ake k’ara suma su mik’e su gabatar da kawunansu. Barrister Jamilu Nashe… shine lawyern da zai kare ni…
Sunana suka tambaya na kuma sanar musu sannan Barrister Fateemah J. Nashe mai kare mai k’ara ta matso don yin tata tambayar.
Duk tambayar da ta min kasa bata amsa ko guda na yi saboda yarda zuciyata ta yi wani irin nauyi ga idon mutane a kaina. Har sai da ta sake maimaita tambayar “Ayshatu me ye ha’din ki da Minister D’an Audu da har kika yi k’ok’arin kashe shi bayan kun k’wace masa dukiya mai tarin yawa…” Na girgiza kaina murya a shak’e na ce “Ba ni ba ce.” Ta ce “Ba ke ba ce kamar Yaya? Bayan ga zahiri an ga kamanninki kwabo da kwabo a hoto? Kuma da bakin ki kika amsa a station cewa ke ce?” Runtse idona kawai na yi ina fisgar leb’ena hawaye suka fara zubo min na k’i kuma na ce komai naja bakina na tsuke.Barrister Fateema ta jijjiga Kai ta ce “Ya mai girma mai shari’a da alama Aysha ta shirya wasa da hankalin kotu, bayan hoto da komai Sun nuna ita ta aikata abinda ake tuhumarta da wannan damar nake rok’on kotu da ta zartar da hukuncin da ya dace da Aysha ba don komai ba sai don Jan hankali ga b’aragurbi irinsu Aysha…” Da sauri Barriste Jameel ya mik’e ya ce “Ya mai girma mai shari’a bai kamata kotu ta yi hukuncin gaggawa Akan wannan baiwar Allahn ba alhali ba a tabbatar da laifin da ta aikata ba, tsananin b’acin rai yakan saka mutum ya amsa laifin da ba nasa ba. Hoto kuma ba zai zama hujjar da zia saka a kamata a nanik’a mata k
Laifin da ba nata ba, duba da cewa za’a iya kwaikwayar fuskar mutum don son jingina masa wani laifi da bai aikata ba. A bada dama ta hanyar tsaurara bincike a kuma gano sauran y’an uwanta idan suka zo suka tabbatar itace sai a zartar mata da hukunci da ya dace. Dafatan Kotu zata amince da wannan nazari nawa…” Alk’ali ya jinjina Kai kafin ya yi rubutu ya d’ago ya ce “Bisa ga tarin hujjojin da Barriste Jameel ya bayar kotu ta gamsu ta kuma d’age saurarar k’ara zuwa zuwa ashirin da bakwai ga watan nan da muke ciki, kafin nan kotu bata amince da bada belin Wanda ake tuhuma ba…” ya buga guduma daga nan shari’ar ranar ta tashi. Ina kallo aka sake ingiza k’eyata zuwa motar shiga ba biya. Na dinga kallon su Ustaz da suke share hawaye akai akai.
Haka aka sake gark’ame ni a d’akin da zan kira k’anin kabari, dalili ba wuta ba haske ba fanka a ciki. Window k’walli guda ne kuma d’an mitsitsi a can saman katanga. Zuciyata ta yi rauni na zube a wajen ina sakin kuka a hankali. Daga ranar ban sake saka kowa a idona ba, sai lawyer na Ustaz Jameel da yazo ya min tambayoyi Amma amsa guda bake bashi ni ban sani ba….
Ranar zaman kotu na biyu suka sake zuwa suka tafi da ni. Wannan karan ma Kotun a cike take mak’il da jama’a. Ban yarda na bu’de idona ba saboda hasken sai Naga ya min yawa. Ko don na da’de ban ga hasken ba ne. Na dubi inda jama’a suke. Anan na hango Duka y’an gidanmu. Sai Ustaz da yake gefe ya sunkuyar da kansa yana murza goshinsa. Na mayar da duba na wajen lawyoyin da suka mik’e suka fara gabatar da kansu. Mami na furta a hankali ganinta sanye da rigar lawyoyi fuskarta ba fara’a ko ka’dan idanunta sanye da black shade… sai a sannan na tuna Mami fa lawyer ce mai zaman kanta. To me tazo yi? Wa kuma tazo karewa?
Ban amince a fitar min da pages d’in da ban Saki a normal groups ba. Jdan kin San kin siya Vip be don ki fitar Uwar gwaninga gaya min da wuri na baki ku’dinki. Ko ban ce ban yafe ba na san Allah ba zai k’yaleki ba dalili? Na bayar da kyautar ina kan bayarwar ma.
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA …..44.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.