Sashe 8
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
★★✍️
Umma ta juya ta fita ta bar d’akin ba tare da ta sake min second look ba. Jikina a sanyaye na mik’e na bi bayanta ina fatan duk da abinda za su zo min yazo min da sauk’i.
Sanda na yi sallama duka a ciki suka amsa min sallamar. Fuskarsu a mutyuke musamman Baffa Mutari sai ka rantse da Allah bai tab’a dariya ba. Ina zama Baffa Mutarin dai shi ya fara magana muryarsa a kaurare ya ce “Ke duba nan, duk nan kin san ba abokin wasanki ba kuma sa’anki ko? To ki bu’de kunne ki ji da kyau abinda za mu gaya miki, bana son wasa da hankali kuma, a ina zamu samu abokin shai’danancin ki? Abu na gaba mun yanke hukuncin aurar da ke da zarar kin gama iddar da ta zama dole a kanki, duk da shi ya ce bai d’ora miki idda ba sai dai mutane ba su san wannan ba… ba zaki mayar da mu mutanen banza ba, kina ji ko?” Jikina a sanyaye na ‘d’aga kai. Ya girgiza kai yana yin k’wafa ya ce a haka kamar wata mutuniyar kirki, ki gaya mana a ina zamu samu wancan mutumin banzan?” Hawaye ne ya fara son zubo min na yi k’arfin halin hana shi zubowa. Wata tsawa da ya saka min ban san sanda na runtse ido ba na furta “Zan fa’da wallahi.” Baffa Yahya ya yi wata dariya ya ce “Kin ceci kan ki don wallahi da ba ki fa’da ba yau idan na dinga dukanki a gidan nan sai kin kasa tashi.” Wani irin huci suke fitarwa hakan ya sake tsorata ni a hankali na ce “Wallahi Allah ban san shi ba…•” wani irin mari Baffa Yahya ya kai min suka cigaba da zagina. Ni dai ina durk’ushe ina zubar da wasu irin hawaye ina kallo suka gama ci min mutunci suka fice. Na mik’e tun kafin Abba ya bani dama na shige d’akina cikin rawar jiki da bugawar zuciya.
Haka rayuwa ta cigaba da gargara min, wasu abubuwan tuni na saba da su yayin da wasu abubuwan har a kullum sake firgita ni suke yi. Ta gefe guda na samu sassauci a wajen Umma da Abba suna amsa gaisuwata duk da dai ba sakin fuska a tare da su. Yayyena ma su kan d’an kula ni ka’dan. Hakan ya saka na d’an samu sauk’in zuciya. Sai dai ba dama na fita an dinga zun’dena kenan a cikin unguwa hakan yasa na rage fita. Dama ba Bari na fitar ake ba Umma dai ta daina gallaza min da kaso talatin cikin d’ari. Hakan yasa na d’an samu nutsuwa ta wani b’angaren.
Wani dare Abba ya dawo tun daga yanayin yarda yake tafiya na san ba lafiya ba. Kamar jiri yake ka’dan fuskarsa ba walwala ko ka’dan. Na masa sannu da zuwa ya ‘dan amsa min yana d’auke kai na karb’i ledar hannunsa shi kuma ya shige cikin sasansa. Ina zaune a tsakargida Umma ta fito tana kallo na ta furta ki je In ji Abban ku.” Da sauri na mik’e duk da zuciyata ta yi wani irin bugawa na isa wajen Abban.
Yana zaune idanunsa akan t.v ya zuba ido yana kallon labarai. A gefe na durk’usa nima ina kallon t.v ‘din ba tare da ya kalleni ba ya ce “Ki je waje zaki gana da bak’on da na zab’a miki a matsayin Miji, kada kuma ki sake ki bujircewa Umarnina a yayin da idanunki suka yi tozali da abinda bai gamsheki ba…” Zuciyata ce kawai take bugu na mik’e jikina a sanyaye ina tunanin waye Abba ya zab’a min a matsayin Miji, sai dai ina tunanin koma waye zan jure zan kuma yi biyayya na amsheshi da hannu biyu ba don komai ba sai don na faranta ran Abba.
Ban koma d’aki ba da dogon Hijabi na na fita harabar gidan. Ba kowa a harabar daga Idi mai gadi sai Tanimu driver. Isa wajensu na yi ina furta “Sannunku, don Allah ina wanda ya zo wajena.” Sai na ga Tanimu ya mik’e yana washe baki, ya furta “Ai ba wani ba ne Hajjaju ni ne…” Cak na tsaya ina kallonsa sanye yake da koriyar shadda da hula orange sai yage hak’ura yake kamar me, babu aji sam a tare da shi, ni da nake son mutum d’an gayu miskili mai ilimi mai iya soyayya da kalamai masu kwantar hankali ta ina zan iya da Tanimu? Na dinga cijar leb’ena ba tare da na san ina yi ba. Ya kuwa cigaba da gyara tsayuwarsa yana furta “Anan zamu tsaya ne Hajiya Aisha, akwai maganganun da nake son na rattabo miki….” Samun kaina na yi da tafiya da baya da baya ina girgiza kai na. Hawaye kuwa suka fara zuba kamar famfo… ina ji Tanimu na kira na sai dai nan tsaya na saurareshi ba na shige cikin Gida da sauri. Karaf na ji na yi karo da mutum… da sauri na ja baya ina mayar da numfashin da naji yana min wuyar fita kamar ana shak’e min mak’ogwaro. Da sauri na ji Yaya Usman ya rik’e hannuna yana furta “Nutsu Aysha menene me ye ya baki tsoro haka?” Hannuna na saka na dinga nuna masa waje sai dai baki na ya kasa furta abinda nake son fa’da masa. Gani na yi kawai ya ja hannuna mun nufi cikin gida. Sai da muka isa d’akina ya zaunar da ni, sannan ya tsiyayi ruwa a cup ya saka min a baki. Ruwan na sha sosai kafin na saki ajiyar zuciya ina kallonsa na lumshe idona hawaye yana zubo min daga ido na ce “Yaya Usman wai Tanimu Driver Abba ya bawa aure na. Wallahi Yaya Usman wannan karan ba zan jure ba, da na auri Tanimu gwara na bar gidan nan na bi duniya ka….” Da sauri ya saka hannu ya rufe min baki, yana furta “A’uzubillah!!! Kina da hankali kuwa AYSHA kin san abinda kike fa’da kuwa? Ba kya cikin hayyacinki ko? Ki nutsu ki min magana yarda zan gane, waye ya ce miki za ki auri Tanimun?” Cikin shashshek’ar kuka na ce masa Abba ne Abba ne da kansa ya ce ya bashi aure na…” Yaya Usman ya zaro ido ya ce “Ah haba wallahi wannan karan hakan ba zai yiwu ba, ko kisan kai kika yi Ai sai haka? Akan wani dalili ina matching a aurenki da wani Tanimu? Ina zuwa zauna anan yanzu zan dawo…” ya fita da sauri duk ransa a b’ace binsa na yi da sauri na rab’e a jikin windown parlorn Abban ina jin abinda Yaya Usman d’in yake fa’da. Ina ji Abban ya amsa sallamar yana furta “Usmanu yaya dai?” Yaya Usman ya gyara zama ya ce “Abba wata magana na ji AYSHA ta gaya min, wai ka bawa Tanimu aurenta, Haba Abba Ai abin zai yiwa AYSHA yawa, sam babu matching a ha’din, Abba ka yi tunani da kyau, Tanimu mara ilimi AYSHA mai ilimi Tanimu d’an k’auye Ayshatu y’ar birni, Tanimu marar wayewa AYSHA mai wayewa, ta ina wannan ha’din gambizar zai hadu fisabilillah, Haba Abba ku tausaya mata don Allah dama itace namijin shi mace sai a ce ha’din zai tafi don Allah Abba ka yi hak’uri kamar hukuncin ya yi tsauri da yawa…” wani murmushi na ga Abba ya saki ya ce “Ka gama Usmanu? Na ce ka gama? Duk na ji abinda ka ce abu guda da ka manta baka fa’da ba a banbancin na su shine Ayshatu y’ar iska Tanimu kamilalle, ashe ba Tanimun aka cuta ba da za’a lik’a masa ragowar wani? Idan ba mu godewa Tanimu ba bai kamata mu tozarta shi ba, don haka maganar aure babu fashi fak’at bana son na sake jin wata magana bayan ta ta amince da zab’i na, idan ba haka ba d’aga kai Har AYSHA wallahi za ku har gidan nan…” wata irin harbawa zuciyata ta yi da sauri na bar wajen cikin matsanancin tashi hankali.
A daren ranar dai ban sake ganin Yaya Usman ba, yarda na ga dare haka na ga rana zuciyata ba abinda bata sak’a min ba na aikata sai dai na kasa yarda na gudu na bar gida. K’arfe shidda na safe Yaya Usman ya shigo d’akina yana kallona ya ce AYSHA tashi…Tashi tashi mu tafi potiskum don Abba ya rantse a gobe zai d’aura miki aure da Tanimu da zarar manema auren sa sun zo… ki tashi ba mu da lokaci….” Wani irin kallo nake masa ido na ko blinking basa yi tsabar ka’dawa da zuciyata ta ke. Ji nake kamar wasu abubuwan basa aiki a Gangar jiki na… AURE DA TANIMU? Shine abinda zuciyata take ta nanata min…
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 28.