Sashe 45
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Da Azahar sai ga Mami na da Umma. Suka shigo fuskokinsu a ha’de. Da na ha’da ido da su sai da na ji fargaba tazo min don ban saba ganinsu a haka ba. Gaisuwata ma basu amsa ba suka fara min masifa fa’da suke sosai ta inda suke shiga bata nan suke fita ba. Cikin rawar harshe na furta “Ni fa ban san me na yi ba.” Mami ta wurgo min pillow tana furta “K’in ci gidanku AYSHA, kamar ya ba ki San me kika yi ba, saboda bak’in kishinki na banza kin saka an saki yarinya haka kawai.” Da sauri na waro ido na ce “Ni kuma? Wallahi ban san zancen ba, ba ruwana shi ya ce ba zai iya adalci ba ya saketa Wallahi ku tambaye shi ku ji.” Na fa’da hawaye yana zuba a idona. Ustaz ne ya zauna a gefensu bayan ya gaishesu ya shiga wanke ni tas a wajensu ya ce “Wallahi ba ruwanta Mami, ni ne da kaina na yanke wannan hukuncin.” Tsaf ya gaya musu dalilinsa sai na ga Sun saki ajiyar zuciya. Mami ta ce “Allah ya so ki, dama da da saka hannunki wallahi Mihammad ko Aliyu zan saka su zo su zaneki.” Daga haka suka mik’e suka tafi suna sake jaddadawa Ustaz sam bai kyauta ba, da ya aikata hakan. Duk da hakan da ya yi shi yake nuna shi mutum ne mai adalci. Shi dai shiru ya yi yana sosa kai. Muka raka su Har mota. Tun daga hanya Ustaz ya ja hannuna da sauri muka shige d’akinsa, ni da kaina a ranar na San ya yi missing d’ina.
*****Ranar da muka yi sati biyu da dawowa Ustaz ya ce na shirya mu je ziyara gidanmu da gidansu.
Gidansu muka fara zuwa nan na ga kulawa da soyayyar surika. Mommy mutuniyar kirki ce ashe, ta dinga ina ka saka ina ka ajiye da ni cikin mayalwaciyar fara’a. Haka ta tasa Ustaz a gaba ta dinga masa nasiha da ya kula da amanata da aka basa. Kada ta ji kada ta gani. Tabbas Momny mutuniyar kirki ce kamar surikar Nazeefa. Allah ya k’ara mata yawan rai baiwar Allah da bata damu duniya ba. Ta cika ni da abubuwan arziki muka tafi. Daga nan gidanmu muka je.
A tsakar gida na tarar da su gaba d’ayansu Har Humaira da San bata rabo da zuwa gida. Na d’ane Mami na da sauri cikin murna ina furta “Mami k’iba fa ki ke yi? Ke da ba kya son k’iba.” Umma da take gefe ta ce “To Mara kai, ki kula da kyau kada ki kada ita… duk da ban so gaya miki ba.” Na waro ido ina kallon Mami da take ta rok’on Umma kada ta gaya min. Tana nuna Ustaz da yake tsaye yana d’an sakin murmushi. Da sauri na isa wajen Umma ina furta “Umma don Allah menene?” Umma na murmushi ta ce “Ai abin murna ne, gwara kawai a gaya mata na San sai ta fi kowa farin ciki, Mamin ki ta kusa samar miki k’ani.” Na wani irin waro ido kafin na daka tsalle….
A yi hak’uri kun ji ni kwana biyu shiru na d’an yi tafiya ne. Na gode masu bincikae Lafita ta.
Jikar Nashe★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….62.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Ina zaki?” ya fa’da yana cafko hannuna. Screen d’in wayarsa da ke ringing Na bi da kallo ganin an saka My wife tuni hankali na ya tashi, sai sannan zuciyata ta tuna min ba ni ka’dai nake da Ustaz ba ashe, wani kishi ya dunk’ule min a k’irji Har ina jin kamar ba zan iya numfashi ba. Cikin hanzari na janye jikina na fice daga d’akin da sauri, amma abin mamaki Ustaz ko sunana bai kira ba balle ya yi yunk’urin biyo ni. Ina ji yana kashe murya yana amsa wayar kamar Wanda yake waya da budurwa zafin k’irjina ya sake yawaita na fara tunanin haka zan cigaba da rayuwa da Ustaz muna sharing d’insa da wata. Tuni k’walla ta fara suntiri akan fuskata. Na zauna saman kujera na zuba uban tagumi kawai.