Sashe 1
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 25..
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Arewabooks@nazeefah. Ya duba ga mai son books d’ina.
Ko wattpad@Nazeefah381.
★📖
Tun da na gan mu a k’ofar gidan duk wata nutsuwata ta kau, sam bana son ha’duwa da mamy sai nake ga hukuncin da aka mata kamar ya yi tsauri, bai kamata a yanke mata hukunci ba tun kafin a tsaurara bincike, ni kaina ba su min adalci ba da suke hora ni ba tare da an yi binciken ba. Da sauri na dawo hayyacina jin wata Uwar tsawa da Hajiya Inna ta daka min. “Fice mu je munafukar banza kawai.” Na runtse idona zuciyata cike da jin zafin sunaye iri-iri da ake kira na da su tun bayan afkuwar lamarin. Na fita da sauri tamkar an hanka’dani jin Uban zagin da Inna ta sauke min. Na tura gate d’in gidansu Mamyn a hankali. Shiru ba kowa as usual, gidan koda yaushe a cikin shiru yake. Da yake basu da wasu yara kuma gida ne na y’an boko da wuya ka ji an yi wata hayaniya mai k’arfi. Inna a ciki ta yi sallamar na san banda ma ta san hukuncin rashin yin sallamar yayin shiga waje da bata yi ta ba.
Mama Mahaifiyar Mami da k’yar ta ‘dago ta kallemu kafin naga ta kawar da kanta, ta ‘dan saki tsaki ka’dan. Ta kuma amsa sallamar itama a ciki. A zafafe Inna ta ce “Ba shakka, ai dole ki kalle mu ki watsar Habiba, tunda kun riga kun cucemu me ya rage kuma banda ku zuba ruwa a k’asa ku sha..” Cikin zafin Rai Mama ta d’aga mata hannu “Please Inna ki ja girman ki, bana son ta kai mu ga samun sa’insa, ban ma san me ya kawoku nan d’in ba, tunda dai alak’ar da ke tsakanin mu ya warware kuma ba ‘da tsakaninsu balle kice dalilin d’anki kika zo…” Inna itama a kufule ta furta “Dole nazo Habiba, dole na zo na tambayi makirar y’ar ki dalilin da yasa ta dinga bawa yarinya kayan maye, ai dama ba A’i bace abar zargi ita Fatiman ita ya kamata a tuhuma mu je hujjar da duk dare sai ta ‘dirka mata madara… wato da wannna ta yi amfani ta b’atawa yarinya suna, to sai ta fito mu ji wani k’aton banza ne….” “Ba zata fito ba, Ba zata fito ku saka mata ciwon zuciya ba, ku barta ma da hawan jinin da kuka saka mata, da’din abin akwai Allah akwai kuma hisabi…” Mama ta fa’da tana sake tsuke fuskarta ni kuwa sai gaisheta nake bata ko kalleni ba. Ina ji Inna ta ce “Wallahi sai ta fito ko na saka y’an sanda su fito da ita ta dole, don wannan maganar ba abar da za’a k’yale ba ce ta tafi a banza dole mu binciki wani k’ato ne a hoton can…” Mami da na gani a tsaye ne gabana ya dinga wani fa’duwa fuskarta a d’aure sosai take kallon Inna tana tauna chewingum. Ta zauna tana furta “Ga ni, sai ki gaya min me ke tafe da ku…” Ni kaina ba Inna ba sai da naji shakkar Mami yarda take jijjiga jiki tana tauna chewingum. “Eeh lallai ba shakka, kalarki Zam ta rashin arziki ta bayyana muraran Fatima, dama ashe lumbu-lumbu kika yi mana, kika b’oye wacece ke don kawai ki zaluncemu.” Wani murmushi Mameey ta saki, ta tauna chewingum d’in ya bada k’ara k’as sannan ta turo shi ta yi k’wai da shi. Idonta ta juya kafin ta furta “Hajiya Inna kenan kuma burina ya cika ras! Sai me ya yi saura kuma? Zaku tsireni ne? Ko Police station d’in kika kai ni, baki da hujjar da zaki saka a kama ni da laifi, balle zuwanki police station kamar tona asirin d’iyar ku ne, don duk duniya sai taji labarin abinda ta aikata gwara ma kada ki fara…” Inna wani irin huci take kafin ta furta “Allah ya isa Fateema, In sha Allah sai kin girbi abinda kika shuka, kin zalunci yarinyar da aka baki saboda tausayin rashin haihuwa ashe ke bak’ar muguwa ce makira annamimiya…” Ina kallo Mami ta cije leb’enta ta sake kallon idon Inna ta ce “Kada ki sake zagina, and please ki tattara komatsanki ki bar nan wajen tunda ba abinda ya ha’da ni da ke..” Ni kam ina tsaye kamar an Dasani wani irin hawaye ne kawai yake bulbula a idona, da gaske kalaman Mami sun matuk’ar furgitani Hajiya ta mik’e jikinta a sanyaye ta kalli Mami ta ce “Abinda kika yi Allah ya miki ninkinsa….” “Ameen” Mameey tace tana tauna chewingum d’inta. Idanunta kuwa sai juya su take. Ma fice ina waiwayon Mami na da ko sau guda bata yarda ta k’ara kallona ba, tun bayan kallon farko da ta min. Tun a mota ta cigaba da bambamin masifa. Duka lefin ta tattara ta ‘dora shi a kaina. “Za mu je gidan, don Ubanki zaki gaya min dalilin da yasa ta dinga baki madara baki fa’da ba.” Shiru na mata ina jin abinda take cewa. Sai dai ni sam bata wannan nake ba mamakin da Mami ta bani yafi saka min tashin hankali fiye da masifar Inna.
Muna zuwa gida muka tarar Abba ya dawo. Inna tana kallonsa tana amsa gaisuwar sa a ciki. Ta shiga parlorn sa idanunta kuwa sai zubar da k’walla suke. Ni dai ban bi su ba don tsoron Abba nake ji, ina gaishe shi ma da k’yar ya amsa gaisuwata. “Ina kike Munafuka?” Daga tsakargida na jiyo maganar a sama, ko ba’a fa’da ba na san da ni ake, don sunan nawa ya tashi Daga Ayhsa ya koma irin wa’dannan sunannakin.
Jikina a salub’e na shiga parlorn Abban na durk’ushe a gabansu. Tana girgiza k’afa ta ce min. “Don Ubanki, yaushe kika yi lalacewar haka da Ubanki da Uwarki ba su sani ba?” K’asa na yi kawai da idona ina zubar da hawaye ba furta “Wallahi Inna ba ni ba ce…” “ke ina wasa da ke ne d’ago ki kalleni ta yaya ya zama ba ke ba ce, ga ki zahiri a hoto.” Na ‘dago ina kallon hoton ina runtse ido, sam bana son ganin wannan hoton. Shiru na mata don na san idan na cigaba da cewa ba ni bace d’in ma babu mai yarda… “Kaga ni ko? Kaga illar ilimin boko ko Imamu? Tun farko da an aurar da yarinyar nan da duk haka bata faru ba, yanzu kun yi bincike a kai ko kuwa zuba ido kawai kuka yi kuna jiran azo har gida a gaya muku an kama shegen k’aton, ai sai yazo mu ji dalilin da yasa ya lallata ta don Ubansa… Don Ubanki a ina yake kuma a ina za’a same shi?” Inna ta fa’da tana kai min duka. “A jiya aka samu nasarar sanin wanene? Sai dai abin mamaki da ya fahimci abinda ya aikata nemansa ake ruwa a jallu wallahi Inna ashe ya gudu tun wancan satin ba kuma a san k’asar da ya tafi ba…” Inna ta runtse ido tana furta “Ba sai a baza police ba, duk inda yake Ai za’a kama shi.” Abba girgiza kai ya yi. Ya furta “Hakan naso a yi Inna, sai dai shi wanda yaso ya aureta da d’in ne, ya ce kada a yi haka don idan har magana ta je wajen police to kamar fa ta kara’de duniya ne, don haka muka saka Dss kawai suke binckiken sirri da ikon Allah kuma za’a kama shi, zaku ma a tuhume shi idan har da gaske saka shi aka yi ba laifinta bane wallahi sai na ‘daureshi na ga Uban da ya tsaya masa.” Inna ta share k’wallarta tana furta “Tun farko abinda ya kamata kenan, sannan kuma tun kafin zancen ya baza duniya dama Imamu ka nemi wani ka bashi ita, a ‘d’aura auren baki alaikum ba wanda ya ji ya gani, don idan aka bari mutane suka farga wallahi ba mai aurenta, duk da dai duniyar ta lallace ba kamar Zamanin mu na da ba.” Abba ya jijjiga kai “In sha Allah Inna ba zata sake ko wata hu’du a gaba na ba, tunda shi da kansa ya fa’da bai ‘dora mata idda ba.” “Ya dai fi!” Inna ta fa’da tana mik’ewa takalmanta ta zura ta ce “Ni zan wuce.” Abba yana kallonta cike da mamaki ya ce “Tafiya kuma Inna? Ai da kin bari sai da safe.” “Bar ni na tafi Imamu, bak’in cikin ganin Hadiza ba zai bar ni na zauna ba, wallahi ko kallonta bana son yi, mata kamar ba jininmu ba, Uwarki Ai na nan tafe zata zo ta sameki da tare ma zamu zo sai ta tashi da mashashshara, haka kawai ki damk’a tarbiyyar y’arki a hannun kishiya, wa yake haka sai kace wani a zamanin Annabawa, ba gashi yanzu ta cucekiba, ai har abada kishiya sunanta kishiya wallahi koda yaushe burinta ta cusa miki bak’in ciki, koda kuwa zata dinga goyaki kullum don tsabar soyayya to kullum zuciyarta da tsanar ki da haushinki take kwana, shashashar banza.” Umma lumshe idanunta kawai ta yi hawaye na zurara daga kwarmin idonta. Ta mik’e don raka Inna ita da Abba. Wannan ya bani damar tashi da sauri na shige cikin d’akin da a yanzu yake amsa sunan nawa. Mayar da k’ofar na yi na kulle sosai. Sai sannan naji wani kuka na tashin hankali yazo min. Ai kuwa na dinga yinsa ba k’akkautawa kamar zaa zare min rai, ranar dai kam ba abinda zan ce ya shiga bakina, tsabar rashin jin da’din da nake ji a zuciyata haka ya bayyana har saman harshena wani d’aci nake ji, na ji bana sha’awar shan ko ruwa, duk abinda ake min baya damuna kamar yarda Mami ta amsa da bakinta wai ta aikata duk zargin da ake mata, ita ta gurb’ata min tarbiyyata, wannan magana ita take dugunzuma tunani na.