Sashe 19
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Idona na runtse na sake ware su a kanta, don son na tantance da gaske ita d’in ce. Bata bari na cigaba da tunanin da nake ba ta kama hannuna tana sakin murmushi ta ce “Ayshatu ni ce dai ba wata ba, mu je ciki ko ba kya maraba da gani na, na ga baki welcoming d’ina ba.” Jiki na a sanyaye na bi bayanta ganin yarda ta shige cikin parlorn kai tsaye ba tare da wata fargaba ba. Allah ne kawai yasa na koma cikin parlorn saboda yarda k’afafuna suke kakkarwa. Me Mami tazo yi? Shine abinda nake ta tambayar kai na. Zama na yi a kujera mai kallon tata jikina a kasalance ina kallonta kawai. “Ba gaisuwa AYSHA?” Na ha’diye wani yawu da naji ya tsaya min a mak’ogaro na ce “Akwai Mami, ina yini?” Ta sake murmushi tana zagaye parlorn da idanunta. Ta furta “Lafiya lau Ayshatu, ya amarci hope komai ya wuce Ustaz ya karb’eki as his wife?” D’aga mata kai na yi. Sai naga ta tab’e baki ta ce “Allah ya baku zaman lafiya, amma ban gane ba haka ya kamata ki welcoming bak’i ko kuma nice ba ki so zuwa na ba?” Da sauri na girgiza kai ba wai har zuciyata naso zuwan nata ba sai don ba yarda zan yi da kunya na kalli idonta na ce ban so zuwanta ba. Ta saki dariya ka’dan tana furta “Na san you are not Happy Shatu, baki farin cikin gani na ba, ba yarda za ki yi ni, an gina wata Katanga ta k’iyayya tsakaninmu akan laifin…” Ta ciji bakinta wasu tarin k’walla na zubo mata ta furta “Bakomai shai’dan ne, kema kuma ina son ki saka a ranki ba laifin kowa ba ne sai na shai’dan shi duk ya assasa duk wannan wutar fitinar, ki yi biyayya ga Ustaz AYSHA amma ba irin biyayyar da zaki cuci kan ki ba, ki kima jajirce ki koma makaranta bana son nan gaba ki zama a sahun gidahumai nafi son a ko ina a dinga damawa da ke.” Ta mik’e tana murmushin da kai zan iya kiransa feck smile, ta ce “Am leaving Shatu, dama na so kawai nazo na ganki ne…” Ko kafin na ce komai ta nufi hanyar waje da sauri na bita da ledar da ta Bari a saman center table na ce “Mami you forgot your things…” Ta dubi ledar hannu na ta ce “It’s yours AYSHA, duk yarda zaki amfani da su na rubuta.” Ta shafa kumatu na bayan ta kai min sumbata a gefen kumatu ta ja karan hancina ta ce “Take care care of your self dear.” Ta fice da sauri ta nufi gate. Hawaye na ji sun fara zuba a idona na ja jikina da ya min bala’in weak na shige cikin parlor na. Haka kawai na samu kaina da zama jigum cikin rashin kuzari ina kallon ajiyar ledar Mami, na saka hannu na bu’de ta. Wasu irin turaruka ne masu bala’in k’amshi kana ganin kwalabansu ka san an kashe ku’di wajen siyensu. Sai wani body mist da Turarukan wuta na jiki da na kaya. Gefe guda kuma wasu containers ne da aka zubo magunguna iri iri, da tarkacen su zuma, dukkansu da yarda za’a yi amfani da su. Na lumshe ido na ina jin yarda suka sake cika da hawaye. Na tattara kayan na shigar da su bedroom d’ina, haka kawai yinin ranar sai na ji zuciyata ta yi wani irin nauyi ga kasala da ta addabi jikina.
Da yamma ina kwance a parlorn idona a lumshe barci ne yake fisgata sai dai bana son na yi barcin duk da daddare ba barcin nake ba, kwana nake ina sallah sai Asuba yawanci nake barci. Na dinga jin k’amshin Ustaz a hancina, a hankali na bu’de lumsassun idanuna sai kawai naga Ustaz a kujerar da take facing d’ina ya zuban ido. Ban ma san ya shigo gidan ba. Fuskarsa a d’an ha’de yana murza goshinsa ya ce “Baki iya gaisuwa ba ne?” Shiru na masa kafin na turo baki na na sake lumshe ido na a raina ina cewa sai ka shekara a wajen in dai jira kake na gaisheka. Tsaki ya yi ka’dan ina kallo ya tashi ya shiga d’akinsa sai naga kamar duk jikinsa a gajiye yake, don a hankali yake tafiya hannunsa a kansa yana jan gashin kansa. Na ja k’aramin tsaki ina sakin wak’ar da na tabbatar ya san habaici nake masa. Bai kula ni ba ya shige hanyar da zata kai shi bene inda zai hau sama. 1 hour ya d’auka sai ga shi ya sauka sanye cikin wando three quarter da armless Riga black da ta yi matching da light cbrownn d’in wandon, da dai shiri muke da shi da kam na furta masa ya yi kyau duk da fuskarsa a tsare take. Ya zauna still yana sake kallo na duk parlorn ya sake ha’dewa da shegen k’amshinsa mai kassara nutsuwar mutum. Tsawon lokaci idonsa a kaina kafin na gaji na ce “Ni fa kallon nan ya isheni malam, wai me ma kake kallo ne?” Lumshe idonsa ya yi kafin ya furta “Mara kunya kawai, me Zan kalla banda abubuwan da ake kallo a jikin mace, wanda kike rabawa maza.” Shiru na masa ba tare da na bayyana damuwata ba sai can na ce “Na raba musu d’in kuma wallahi baka ji yarda suke zuzuta lamarin ba…” wani irin Zillo naga ya yi ya iso gaba na fuskarsa a mugun ha’de ya ce “Are you mad kike gaya min wannan maganar? Ni kike gayawa wasu banza sun zuzuta ni’imarki?” Dariya na yi ina kallon yarda yake wani irin huci kamar zai ci babu. Na ce “Ai gaskiya na gaya maka, don kam duk wanda ya kusance ni sai ya yi kamar ya hauka ce don d’imaucewa…” wani irin fisga ya kai min a zuciye na fa’da jikinsa ya saka hannu zai tsinka min mari sai naga kawai ya saki tsaki ya ture ni gefe idonsa a runtse ya furta “Stop it AYSHA I hate this nonsense, kin san yarda kike hurting zuciyata kuwa? Ko kina son ki yi ma amaryata asarata ne?” Na tab’e baki na ina kallon yarda idonsa suka wani firgice mai nuna yana cikin matsanancin zafin zuciya. Ya mik’e a zafafe ya shige d’aki. Haka kawai na ji ina son na bisa d’akin naga me zai yi. A hankali na tura k’ofar bedroom d’in da ya shiga ina lek’a wa alamar shashshek’ar kuka na ji, jikina a sanyaye na koma parlorn ina mamakin kukan me zai yi, ba shi ya jawo na gaya masa magana ba, ai kuwa zai sani tunda na gane ba zai iya jure kalamai na ba, ko da su ka’dai sai na dinga hurting masa zuciya, har ya gaji ya daina jifa na da kalaman b’atan ci.
Har Magriba ina parlorn ban mik’e ba, shima still bai fito daga cikin bedroom d’in ba. Sai da aka kusan kiran sallah naga ya fito da alama wanka ya yi jikinsa sanye da jallabiya fara tas gashinsa a kwance sai k’yalli yake. K’afarsa sanye da wani black silifas da ya fito da kyan k’afar tasa. Kallo guda ya min ya ‘d’auke fuskarsa a d’aure ya ce “Ki dafa min Indomie, ki shirya kuma zamu gidanmu anjima.” Bai jira amsa ta ba ya wuce. Harara na wurga masa ina tab’e baki na ce “Wallahi ba zan dafa ba. Gidanku kuma zan je ba don komai ba sai don kada ka ha’da ni da Abba mugu kawai mai kan tumato.”
Bai dawo gidan ba sai da aka yi sallahr Isha’i. Ya shigo da manyan litattafai a hannunsa. Sama ya shige sai ga shi ya sauko. Ya ce “Ina indomien?” Na d’auke kai ina fa’din “Ban dafa ba…” ya girgiza kai yana fa’din kin yiwa kan ki, gobe i yanzu ma ba zaki ganni ba balle ki wulak’anta ni. Tashi mu tafi, ko shima ba zaki ba?” Ban masa magana ba na mik’e ina roller mayafin abayata ya d’an kalleni sama da k’asa ina ji ganin da ya yi abayar bundumemiya ce kamar Boubou sai bai damu ba ya nuna min hanya. Shi ya kulle k’ofar babban parlorn sannan muka fita.