← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 49

Sashe 12

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwana biyu sosai na ‘d’au fushi da mutanen gidan. Bana kula kowa sai ta kama. Kowa ma haushinsa nake ji. Yau na tashi da wuri na yi wanka ban yi wani kwalliya ba illa powder da lipgloss da na saka. A parlor na ga mutanen gidan suna karyawa. Yaya Muhammad yana gani na ya wani saki murmushi na lura tunda Ustaz ya dawo yana musu nacin a mayar da aurena da shi yake sakar min fuska. Yanzu ma cike da walwala ya furta “Ayshatu Gaye kin tashi?” Tsuke fuskata na yi na furta “Ina kwana?” Kamar bana so. Ya amsa ba tare da ya damu da fisgar da nake masa ba. Ki zo ki karya, zan kai ku gaba d’aya can gida ku wuni.” Tab’e baki na na yi na ce “Ina azimi…” Ya juyo yana kallona ya ce “Azimin me kuma AYSHA naga yau Talata…” Shiru na masa har sai da ya sake tambayata sannan na ce “Azimin kada Allah ya bawa Ustaz da duk wani mugu sa’a akan mayar da aure na da shi…” Sak naga ya yi cup d’in tea d’in a hannunsa yana kallona ko k’iftawa ba ya yi. Ni kuwa ban damu ba na ‘d’auke kaina daga kallonsa sai ta k’asan ido na dinga kallonsa sai can na ji ya yi k’wafa ya ce “Ni da iyayenki mu ne mugayen kenan?” Ban amsa masa ba na mik’e zan bar wajen ya yi saurin fisgo ni na dawo gabansa na durk’ushe. Sai kuma na ga ya sake ni yana murmushi kawai ya mik’e kin ci sa’a na yiwa Ustaz alk’awarin ba Zan sake kai hannuna jikinki ba, Allah da yau kin sha mamaki, tashi a nan mara kunya kawai don ma kin ga ana lallab’aki, kuma aure kamar kin koma gidan Ustaz kin gama…” “Sai dai idan ni Ayra ce… amma wallahi ba zan koma ba…” wannan karan har Anty Khadija kallo na take da mamaki fal fuskarta ta ce “Ayshatu are you out of your mind…” Ya sake ni bayan ya yi blowing wani zazzafan huci ya zari car keys d’insa ya ce “Khadija maza ku fito mu je can gidan, yau za’a yi ta ta k’are dama duk Ustaz ne ya ja da har ya ce wani a lallab’ata ga shi nan tana niyyar yiwa mutane rashin kunya, yau zaki san nima ina iko da ke kamar yarda nake iko da Ayran…” Ya fa’da idanunsa fici fici cike da zallar masifa. Ban wani damu ba na mik’e na zura hijabi na a zuciya nake furta “Mu je gidan mana sai me wallahi ko me za’a yi ba zan koma gidan wancan wawan mutumin ba….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 34….

MIKIYA WRITERS🕊.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

Ba wanda ya bi ta kaina a cikinsu, hirarsu suke a cikin mota fuskokinsu cike da nisha’di. Hakan ya sake dugunzuma zuciyata ganin da gaske basu damu da damuwata. Ita kanta Anty Khadyn sai na fara jin haushinta. Har muka isa gida huci kawai nake zubawa na tsabar turirin da yake zuciyata.

Fuskata a d’aure tamau na shiga gidan ina yi ina ciccije baki don ma a san duk abinda zan fa’da d’in har k’asan zuciyata haka yake.

Abba da Umma muka tarar a zaune suna ta kallon kayan garar Yaya Usman da aka kawo. Ko kallon kayan ban yi ba na mik’e zan shige parlorn Umma na k’asa. Abba ya saka baki ya kira ni, kiran da naji har tsakiyar kai na. Ba don komai ba sai don mamakin yanayin yarda ya yi kiran a tausashe cikin nutsuwa kamar dai Abba na na wancan lokacin kafin komai ya juye. Cak na tsaya ba tare da na juyo ba. “Ki zo na ce Ayshatu..” Ya sake furtawa. Na juya na koma na zauna ina jingina da kujera idona a lumshe. Bai min magana ba suka cigaba da tattaunawar da suke akan yarda za’a raba ma dangi kayan garar. Sai da ya gama tas sannan ya juyo yana kallona ya ce “AYSHA! D’ago ki kalleni.” Na yi saurin d’aga ido ina kallonsa, zuciyata na wani irin bugu don na san tabbas ba mamaki maganar Ustaz zai min. “Waye ni?” Tambayar ta min wani banbarakwai don haka na rasa amsar da zan ba shi, “Ki gaya min waye ni na ce miki? Matsayin me nake a wajenki?” Sai yanzu na gane tambayar tasa. Muryata cike da rauni na amsa masa da “Kai Mahaifina ne…” Ya girgiza kai yana furta “Madalla da kika fahimci haka, kin san ina da iko da ke ko? Musulunci ya bani damar na baki umarni kuma ki yi min biyayya dole matuk’ar ban kaice hanya ba ko? Sab’anin hakan kin san hukuncinki a wajen Ubangiji ko?” Madadin amsa masa lumshe ido na na yi kafin naji wasu tarin hawaye suna zubo min. “Ki amsa min mana? Kin san wajibi ne biyayya ga iyaye ba sunna ko mustahabbi ba?” Na ‘d’aga kai kawai sai naga ya girgiza kai “amsa ta fatar baki Aysha..” murya cike da rauni na ce “Na sani Abba.” Yauwa a yanzu zan gaya miki ni mahaifinki Imam Khalil na yarjewa Ahmad Sulaiman sa’eed aurenki a karo na biyu, a yau da daddare zan karb’i sadakin ki a d’aura auren….” Zuciyata na ji ta yi wani irin matsanancin bugu, na dinga ware ido ina kallon Abba cikin kakkarwar murya na ce “Wallahi Abba bana son sa….” bayan haka ban sake sanin inda kai na yake ba, sai farka wa nayi na ganni saman gadon Umma gefe guda Umma ke zaune hannunta rik’e da nawa an saka min drip. Na bu’de idona sosai maganganun d’azu suna dawo min ina fatan duk abinda ya Farun ya zama mafarki ba zahirin gaskiya ba. Shigowar Yaya Usman ce ta saka ni sakin ajiyar zuciya, sai a sannan Umma ta san na farka ta juyo da sauri tana kallona ta ce “Aysha kin farka?” Na d’aga kai na a hankali ina jin kan yana wani sara min. Na ce “Umma zan sha ruwa…” Sai naga ta mik’e da sauri tana furta bari na kira likitan na ji ko za’a iya baki ruwan..” Yaya Usman ne ya matso inda nake, idanunsa cikin nawa kafin ya zauna a saman drawerr da take gefen gadon. Murya k’asa ya ce “Sannu Aysha Gayu, me yasa kike son sakawa kanki damuwar da take neman haddasa miki ciwon zuciya, kina son ki mutu ne?” Da sauri na d’aga masa kai. Sai naga ya bu’de ido ya ce “Why?Aysha sai kace ba musulma ba? Duk musulmin k’warai fa ya kamata ya yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau, me ye aibun Ustaz a duk abinda nan da ya faru da ba kya son ki koma gidansa. Duk namijin da hakan ta faru a kansa fa abinda zai aikata kenan, ko nine a shoe d’insa zan aikata fiye da hakan ba tare da wani bincike ba, kin san yarda kishin maza yake kuwa, change your mind AYSHA Ustaz Shine Mijin da ya dace da ke, pls kada ki sake hurting zuciyar su Abba a karo na biyu. Ki kawar da zugar da shai’dan yake miki akan ki bijirewa umarnin iyayenki hakan ba zai zama alheri a gareki ba, biyayya ga Abba da abinda yake so sai kiga kin dace fiddunya wal Akheera..” Runtse idona na yi da k’arfin gaske, jin abinda Yaya Usman ya ce, idan har na fahimcesa so yake lallai na koma gidan Ustaz don yin biyayya ga Abba, amma ina sai nake jin zuciyata ba zata iya d’aukar nauyin k’addarar komawa gidan Ustaz ba. Ya kama hannuna ya matsa a hankali. “Ustaz yana son ki Aysha fiye da tunaninki, banda yana sonki ba abinda zai dawo da shi neman aurenki a karo ba biyu…” Hannuna na zare ina share hawayen ido na na ce “Baya sona Yaya Usi yaudara ce kawai, wallahi baya sona da abinda ya saka ya dawo neman aurena ne don kawai ya tozarta ni ya kuma cimma wata manufa tasa.” Dariya Yaya Usman ya yi ya ce “wallahi yana sonki fiye da zatonki, tunda abin nan ya faru bai sake samun kwanciyar hankali ba, kada ki sake saka shi a tunanin baki da kunya ba kuma kya biyayya da iyayenki, ki min alk’awarin za ki yi hak’uri….” na lumshe ido na kawai ba tare da nace masa komai ba. Shigowar Umma ce tasa ya mik’e yana shafa kumatu na ya ce “Be a good girl dear, bari na je sai da safe Umma.” Umma ta ‘daga kai tana ce masa Sai da safe Usman ka gaida Husna. Ya amsa yana d’aga min hannu, da murmushi fal a fuskarsa. Ban mayar masa don bani da sukunin murmushin zuciyata nake jin kamar ana hura min wuta a cikinta.
Chapter 12 · 0% Book details