← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 49

Sashe 24

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Muna isa gida kuwa tas Auntyn Useey ta gyara gidan ta ‘dora abinci. Inna kuwa ta kasa ta tsareni a ‘dakina ta hana ni fita. Sai ga Auntyn Useey ta shigo tana k’unshe dariya ta mik’o min wayar hannunta da na tabbatar ta Ustaz ce, “Ana Miki waya.” Ta fa’da tana dariya ta fice. Wayar na kara a kunnena ina jinsa ya saki ajiyar zuciya Jin muryata ya ce “Ba zaki zo ba ko? Kin bi ta maganar tsohuwar nan?” Na turo baki a hankali na ce “Ba zan zo ba d’in, me zan zo na maka?” “Mhmn” Ya ce, kafin ya ‘dora da “Allah idan baki zo ba zan shigo yanzun nan na aikata abinda tilas Inna ta bar min d’akin…” Tab’e baki na yi na ce “Bismillah idan zaka iya” na kashe wayar na ajiye a gefe, abin haushin hatta da wayarsa k’amshin mayen turarensa da ya riga ya huda jikinsa take. Nocking na ji a hankali kafin na yi magana Inna ta ce shigo mana. Ya kuwa shigo sanye cikin shigar jallabiya sai walwali take da alama wanka ya yi, don na lura akwai soyayya mai kyau tsakaninsa da wanka. Y’a rusuna ya gaida Inna kafin ya tako zuwa bakin gadon gaba na sai fa’duwa yake ganin kamar da gaske yana shirin kunyatani a gaban Inna. Na waro idona ina nuna masa Innar da idona. Ya tab’e baki yana min nuni da ina ruwansa…. Inna kuwa ta zuba masa ido na San so take taga iya gejin rashin kunyarsa. “Tashi mu je za ku gaisa da abokaina Sun zo duba ki.” Ya fa’da yana mik’e min Hijab. Ina mik’ewa Inna ta mik’e itama tana kallonsa ta ce “Banda abinka Ahmad Ai da sai ka ce su shigo, tunda ka ga ai ba zai yiwu ta yi ta zurga zurga ba wajen bai gama ha’dewa ba. Mu je mu gaisa da su ita ta zauna kawai ba sai ta je ba…” Ina kallo Ustaz ya saka yatsa yana murza goshinsa kafin ya ‘d’ago ya ce “Yanzu zata dawo ai, kuma basa jin hausa idan kin je ba ba gane abinda zaki ce za su yi ba…” Inna ta ce “Ai hikkenan, sai ku je Amma dai ta dawo yanzun nan saboda a kiyaye dokar likita.” Ustaz ya ‘d’aga mata kai kawai yana saka hannunsa cikin nawa muka fice daga bedroom d’in. Tun a hanya na fara turje masa, ina turo baki na ce “Pls! Ustaz wai ina zamu?” Ya juyo ganin zan b’ata masa lokaci naga yasa hannu ya d’aukeni cak, ya haye da ni step d’in da zai kai mu ‘dakinsa.

Bai dire ni ko ina ba sai saman gado, ya kalleni yana murmushi kafin yabi jikina ya kwanta ya rungumeni sosai yana sakin ajiyar zuciya. Zan yi magana naji bakina a cikin nasa sai da
Ya yi son ransa sannan ya sake ni yana mayar da ajiyar numfashi ya ce “Ba abinda zan
Miki matsoraciya barci kawai nake son yi a jikinki….” Hawaye ne ya kawo idona na ce “Kada ka sabawa kanka abinda ba zai d’ore ba, am serious ba zan zauna a gidanka ba, ka cika ni na koma kada Inna ta yi fa’da…” Bai cika ni ba sai ma sake shiga jikina da ya yi sosai ya ce “Kina sake magana kuma, zan canja mind d’ina na sake bu’de d’inkin can…” Shiru na masa ina jinsa yana wasu irin abubuwa a jikina
Kafin barcin gaske ya d’aukeshi. Wayarsa da take vibrating ce tasa nima na farka daga barcin da ya fara fusgata ina kallon wayar naga an saka Hayateey sai kawai naji ina son sanin wacece don haka na kara wayar a kunnena ba tare da na yi magana ba. A zafafe na ji Mommy ta ce “Wato Ahmad ka
Mayar da ni abokiyar wasanka ko? Wannnan ne dalilin da yasa fa da farko na k’i amincewa da auren nan don naga gaba ‘d’aya hankalinka na wajen yarinyar can son da kake mata ya yi yawa, to bu’de kunnenka ka ji
Da kyau wallahi gobe sai kun tafi da Hameeda ba fashi idan
Kuma ka k’i bin umarni na ban yafe maka ba, zan kuma yi sanadin da zan raba auren naku Har abad…” Ji na yi ya zare wayar daga kunnena ransa a b’ace ya mayar kunnensa yana
Cigaba da sauraran Mommyn tasa… idanunsa kafin ya gama wayar sun ka’da sun yi jajir. A hankali ya sauke wayar daga kunnensa yana lumshe ido. Wani abu mai kama da tausayinsa na ji yana fisgata sai dai ban yi magana ba na d’au Hijab d’ina na zura da niyyar tafiya na ji ya rik’o hannuna da sauri na fa’da jikinsa. Bakina ya kama da k’arfi yana kissing cikin wani irin yanayi. Bai daina ba har sai da leb’ena suka yi jajur sannan ya saki murya a raunane ya ce “Wa ya ce ki d’aga min wayata K’alb?” Na turo baki na ban yi magana ba. Sai na ga ya saki murmushi ya ce “Am…na San kinji abinda kike so ki ji. Fine…” Ya fa’da yana murza goshinsa a hankali ya mik’e daga gadon gani na yi ya d’auke ni cak mun shiga wata k’ofa sai a lokacin na tabbatar toilet ne. Da sauri naja na tsaya ina furta “Me.. Me zamu yi anan?” Ya lumshe idonsa a hankali ya furta “Love bathing….” Ya fa’da yana bu’de jirkitattun idanun cikin nawa. Na waro ido ina furta “Ni a’a…” Matsowa ya yi daf da ni ya ce “Pls! K’alb, mu yi ko don na dinga tunawa da ke, kin dai ji Mommy ta ce tilas mu tafi da Hameedah gobe kuma na San zan iya kaiwa 8weeks ban dawo ba, ban san yarda zan yi da rashin ki ba, gashi sau ‘d’aya na yi tasting amma kin zautar da ni. Ko da yake ina zuwa zan fara Miki processing Visa kema ki biyo ni…” Tab’e baki na yi na ce “Allah ba inda zan bika, ai yanzu ma na sake jin aurenka ya fita daga raina tunda Babarka bata sona, ba zan zauna a inda ba’a so na ba na San ko nan gaba wahala zan sha, don haka dole kafin ka tafi ka sake….” Ji na yi ya jani jikinsa ya ha’de bakinsa da nawa kafin na ce komai sai jina na yi a cikin bathtub da ya cika da ruwa, ranar kam ni Naga wanka a wajen Ustaz duk da bai yi min komai ba amma jikina ya wahaltu.

Da kansa ya sauka sai ga kaya ya taho min da su. Ina kallonsa kamar na yi kuka na ce Inna fa?” Ya tuntsire da dariya ya ce “Tana can tana barci, Allah dai ya yiwa matar Usman albarka da ta kawo idear saka mata maganin barci…” na waro ido ya d’aga min gira yana sake jana jikinsa a kunne ya ce min “Yau kin sake gigita ni da surar jikin ki Eehsha! Anya nan gaba akwai wata macen da zan sake yiwa kallon mace…” “Har ita y’ar mutuncin da ta San martabar iyayenta….” Goshinsa ya goga da nawa ya ce “Har ita Eehsha, Har kowa ma ke ta daban ce a cikin mutane na daban…. Na tabbata a cikin mata dubu da k’yar a samu biyar irinki, Wai Zuma kenan…” Turesa na yi ina tab’e baki na yi nufin sauka ganin yarda lokaci ya ja. Ina ji ya saki ajiyar zuciya ya ce saura dare zan zo d’aukan ki mu yi bankwana….” Tsaki na ja a hankali na ce “Wallahi kada ma ka fara…” ina ji yana dariya na sauka a hankali. Gidan shiru da alama Auntyn Useey ma ta tafi. Ta dafa mana abinci kuwa na lek’a ko ina ban ganta ba sai takardar na gani akan dinnig ta yi rubutu ka’dan. Ki yi hak’uri AYSHA Yayanki yazo mun tafi a sha amarci lafiya na tausayawa Ustaz ne shi yasa na taya shi samun abinda yake so..” Na yi k’wafa na yaga takardar na cilla dustbin kafin na tura k’ofar cikin d’akin. Inna ce ta motsa a hankali ta mik’e tana kallona ta furta “Kin dawo kenan?”

Na gode da addu’oinku da masu waya yi min gaisuwa da masu zuwa jazakumullah Khaira Jaza’ihi.
Allah ya bada lada Allah ya ji k’an mamatanmu ya kyautata namu zuwan.

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA…. 41.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.
Chapter 24 · 0% Book details