← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 49

Sashe 41

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuciyata idan banda matsanancin bugu ba abinda take yi. Na dinga ganin wani irin bak’in duhu a idona. Ji na da gani na ya d’auke d’if. Bayan nan ban sake sanin inda nake ba sai farkawa na yi na ganni a gadon asibiti. Na bu’de idona da suka min nauyi sosai na tarar da jama’a birjik a cikin faffad’an d’akin asibitin. Dukkansu attention d’insu na ga ya dawo kai na. Umma ta k’araso bakin gadon da sauri. Tana kama hannuna cike da kulawa ta ce “AYSHA, me damunki?” Lumshe ido na na yi kafin na dafe kaina da yake min matsanancin ciwo. Fuskar wancan mutumin kawai nake gani a idona. Tunda na fara girma na d’orawa kaina son auren kyakykyawan namiji ashe ba zan samu ba. Ko kuma Allah ne zai nuna k’udirar sa a kaina ta hanyar hukuntani da laifin tozarta Ustaz. Allah na tuba na fa’da Wanda furucin iya busassun leb’ena suka tsaya. Sake kwatantoshi da ganin surar sa a zuciyata nake. Mummuna ne sosai wallahi irin munin da kana gani zaka furta kai tsaye. Ban da munin yana da k’aton baki, k’aton ciki. Sai dai daga ganinsa ka San Naira ta zauna daga yarda ya baza babbar rigar shadda mai tsada. Ga k’amshin turare yana ta bazawa. Kana ganinsa kaga irin mutanen nan da suka yiwa ku’di taka haye ba asalin wa’danda suka gada ba. Hawaye ne kawai y’a fara zuba daga kwarmin ido na. Umma na ji tana Shafa min kai daidai lokacin da Abba ya ce “Humaira taje ta kira Doctor maza ta sanar masa na dawo hayyacina.” Ba’a d’au lokaci ba Doctorn ya shigo a d’an hanzarce yana duba na yana Zare robar da take Sadar da ruwa cikin jijiyata. Ya kalleni cike da kulawa ya ce “Yanzu me ke damunki?” Muryata a dashe na ce “Ba komai.” Don kuwa ni kaina na zance ga abinda yake damuna ba gwara kawai na ce masa bakomai d’in don bashi da maganin damuwata. Ina kallo ya jinjina kai yana kallon Abba ya ce “A kula sosai, Alhaji don idan ba haka ba akwai yiwuwar ta iya samun hawan jini. Don a yanzu ma Allah ne ya kiyaye Allah ya bata lafiya. Zamu rik’eta anan for 2 days zuwa abinda ya yi hali, don muga yanayin jikin nata da abinda yake damunta.” Abba d’aga kai kawai ina kallon yarda yake komai a sanyaye. Daga haka likitan ya fice yana sake rok’on a barni na huta sosai kada a dameni da hayaniya.

Daidai lokacin mayataccen k’amshin Ustaz ya cika Ilahirin d’akin Asibitin. Ina kallo AYSHA ta mik’e tana furta “Ustaz ya zo Umma, ga k’amshinsa nan.” Na runtse idona da sauri takaicin Humaira yana sake nakasta wani sashe na zuciyata wato itama ta San k’amshinsa kenan.

Ina jin sallamarsa cikin Husky Voice d’insa da take bayyana zamowarsa jarumin namiji.

Da sauri na runtse ido na. Don bana son a fahimci cewa ba barci nake ba.
Bayan ya gaishe da su Abba. Ina jin takunsa zuwa bakin gadon da nake, yarda yake taku haka zuciyata take bugu da k’arfin gaske. Ya d’an tsaya kafin ya ce “Abba ai barci take bata farka ba.” Abba ya ce “Ta farka fa Ahmad, sai dai idan sake komawa ta yi.” Humaira ce ta k’araso don ta k’asan ido na nake hango tahowarta, ina kallon kuma yarda Ystaz ya bata duk attension d’insa da kulawarsa. Wani irin hawaye na ji ya zubo min a gefen ido na. Ina ji ta ce “Lah, Abba mafarkin kuka ta ke yi.” Abba ya ce “Wani irin mafarkin kuka kuma Humaira ke me yasa baki da kai ne. Matsa na gani.” Abba ya saka hannu y’a shafi hawayen gefen ido na yana furta “Tabbas, da gaskiyarki Humaira sai dai mafarkin kuka take ba, zahiri ne kukan take. Wato AYSHA kina jin abinda Likita ya ce ko? Ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko? To wai ma me aka Miki da y’a tsunduma ki a wannan halin? Na ga dai duk abinda kike so shi muke yi Miki.” Humaira ce ta ce “Abba ka mata a hankali, ba mamaki wancan abinda aka mata ne Har yanzu bai bar ranta ba. A hankali komai zai wuce. Abba ya ce “To abinda ya riga ya wuce ba ya wuce ba, meye na dawo da abu baya. Allah ya mana magani shi yasa fa nake ta lallab’ata gidan Ahmad ma ban tilasta mata komawarsa ba.”

Gaba d’aya jin magangansu nake suna k’ara harzuk’a zuciya ta. Na mik’e da sauri fuskata a tsuke na mayar da gashina da ya kwanto saman fuskata. Ustaz yana gefe ya zubo min ido ni kuwa wata harara na zuba masa. Madadin na ga b’acin rai a tare da shi, sai naga ya saki murmushi ya ce “Aysha, ya jikin?” ban ko amsa ba na shige toilet duk da ban san me zan yi a ciki ba. Amma har ga Allah kawai su d’in ne bana son gani gaba d’ayansu har su Abban.

Ina shiga toilet na saki kuka a hankali. Irin kukan nan me cin rai. Ba na so su ji muryata don haka na toshe bakina da d’ankwalina. Don har abada na daina nuna musu karayata.

Tsawon lokaci ina cikin toilet d’in da ban san me nake ba banda kuka. Har sai da na ji ana buga min toilet Umma tana kiran suna na. Hakan yasa na watsa ruwa a fuskata na goge fuskar don bana son a ga alamun na yi kuka. “Fito AYSHA ga mijinki ya zo.” Shine abinda na ji Umma ta fa’da wani irin tarnak’in b’acin rai na ji a zuciyata. Da wani irin k’arfin hali na murza lock d’in k’ofar na fito fuskata ba yabo ba fallasa. A tsaye na ganshi da k’aton cikinsa wayoyinsa manya a hannunsa. Gefensa kuma abokinsa ne me irin kamanninsa. So nake na danne abinda yake raina don na nunawa Ustaz hundred percent na amshi Mijina da hannu bibbiyu. Sai dai gabban jikina Sun k’i bani ha’din kai musamman idona da ya sake kawo ruwan hawaye, da gaske ko ganin mutumin bana son yi. Tuni hawaye suka fara zubo min batun bawa Ustaz mamaki ya kau. Na zauna a gefen gadon ina share ido na da handkerchief d’in da yake hannuna. Ina kallo Ustaz ya mik’awa mutumin hannu suka yi musabiha. Ustaz d’in Naga ya kalleni sai kawai ya tab’e baki ya saka kai ya fice daga d’akin. Abin haushin haka duk mutanen d’akin suka dinga ficewa da sauri kamar ha’din baki. Mutumin da ko sunansa ban sani ba ya kalleni ya ce “Amaryata, ku gaisa da babban abokina mana.” “Amaryar Ubanka…” Haka naso na furta a zahiri sai dai na kasa, sai ha’diye wani irin yawu mai d’aci nake. Na tsuke fuskata ban kuma gaishe shi ba, ji nake kamar na kashe shi ko na daina ganinsa balle har ya kira ni da amaryarsa mutum kamar wani basamude. “Ku gaisa mana.” Ya fa’da da y’an muryar hassala hakan yasa na d’ago na zabga masa harara. Sai na ji abokin nasa ya ce “Ka mata a hankali Mamuda, ai yarinya ce sai ka bi da ita a hankali kafin ku saba.” Duk maganar duniya da suka yi na k’i amsa musu ko guda ina ji gajiya suka yi suka mik’e suka min sallama ha’de da ajiye min bandir d’in dubu guda biyu. Na bi bayansu da kallo duk a maganganunsu ba Wanda ya min ciwo kamar cewar da suka yi wai matarsa ce ta Mutu a haihuwar d’ansu na biyar wato ma zuwa zan yi rainon yara. Kasa jurewa na yi na saka kuka sosai. Wannan karan ban toshe baki na ba don ban k’i kowa ma ya ji ba sai me? Gwara ma su sani Da gaske ba zan auri wannan abin ba.

Kwana biyun da na yi a asibiti na yi su ne cikin wani yanayi da zan iya kira na ciwon zuciya. Hakan kuma ya kasa b’oyuwa gareni. Ni ka’dai na San zafin da nake ji a zuciyata. A haka dai likita ya tattara ya sallame ni don ana shirin fara biki jibi. Bikin da naji suna cewa wai har da d’aurin aure na da tariya ta za’a ha’da, wai mijin zai wuce da ni Abu Dhabi. Inda a can yake gudanar da dukka harkokinsa. Ba irin abinda ban kissima a raina ba na son gujewa auren mutumin nan sai dai duk inda na b’ulla sai naga hanyar ba mai b’ullewa ba ce.
Chapter 41 · 0% Book details