← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 49

Sashe 27

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kashegari around 10:45 Inna ta shigo asibitin kallona kawai take tana murmushi kafin su gaisa da Umman su Zinatu, Inna bata yi shiru ba sai da ta ce kuma Laraba sai al’amari ya canja, wancan labari duk k’anzon kurege ne, ai kuwa Ubanta ya ce ba zai yarda ba tunda ya tabbatar sharri aka ma y’arsa ba abinda zai hana shi d’aukan mataki, kuma nima ina bayansa Eehe, ba kunyar da baa saka ni cikin ta ba, musamman a k’aramin gari irin potiskum Allah ya tsinewa Wanda ya ha’da wannan kirumurmura…” Shiru Umman Zinatu dai ta yi kanta a k’asa ta kasa komai, sai da Inna ta yi son ranta sannan ta ce “Ai yaran yanzu ba wai lallai sai an kawar musu da budurci ba, suna soyayyar shan minti Allah dai ya shirya mana kawai…” Inna ta watsa mata wani kallo kafin ta furta “Laraba, na ga ba alheri ne ya kawo ki asibitin nan ba, sai tsabar sharri to ha’de kayanki tsaf ki bar nan wajen, tunda nema kike dole sai kin lalubo sharrin da za ki lik’a mata.” Umman Zinatu kamar jira take ta yi saurin fara ha’da karonta ta yi mana sallama murya a cunkushe ta fice Inna ta ce Allah ya raka taki gona dama tun tana yarinya uwarta ke fama da ita akan rashin fa’dar alheri… ki ga shan minti akan ki da zuri’arki muguwar banza da wofi kawai. Ta gyara zaman ta tana kunce k’ullin da ta zo da shi. Flask ne ta bu’de sai ga kunun gya’da mai zafi ta zuba min a cup d’aya kwanon kuwa chicken pepe soup ne da ya sha kayan k’amshi ta zuba min ta cika bowl da shi. “To maza tashi, irin wannan lalurar sai an tashi tsaye da gyara idan ba haka ba ki zama lusarar mace kina ji kina gani zaki dawo salaf ba ‘dand’ano ko ka’dan kamar kaza na dafa ta ba maggi, ah to ni dai ba ruwana sai an dage haik’an da gyara da cima mai kyau sai ki ga wajen da ya raraka ya dawo.” Na mik’e a hankali na karb’i bowl d’in da cup na fara shan kunun dama ni na San Inna ba k’aramin iya girki ta yi ba. Ina cikin sha sai ga Ustaz ya shigo k’amshinsa gaba d’aya ya gama mamaye d’akin, duk da hassada ta ba zan k’i fa’din ya yi kyau ba, cikin black jallabiyar da take ta shinning kansa ba hula sai hirami da ya saka a kan ya d’an yafa shi kamar yafen d’an kwali. Kallo na yake yana murmushi kafin ya mayar da hankalinsa wajen Inna da yake zaune tana lazimi tana gyangyad’i. Da sauri ta kalleshi kafin ta amsa gaisuwarsa ganin ya zauna saman gadon da nake daf ya ja hannuna yasa ta mik’e tana fa’din “Rasa kunya, kai yaran Zamani sai dai fatan shiriya…” Shi dai murmushi ya saki tana fita kuwa ya kwantar da kansa a jikina yana murmushi ya furta “I really missed you Baby.” Na tureshi ka’dan fuskata a yamutsa na ce “Ni fa ba matarka ba ce, ta mai rabo ce.” Sai jin lips d’insa na yi kan nawa yana gurza son ransa kafin ya d’ago na turo baki na ce “wace irin mugunta ce wannan da zafi fa.” Ya lumshe idonsa sai da ya kai bakinsa kunnena sannan ya ce “Bana son na ji an k’ara maganar sakin nan K’alb, kin san me yasa na dinga jingina ki da wa’dancan maganganun bakomai ba ne kawai don Naga reaction d’inki, anan zan gane za ki aikata ko baki aikata ba, Alhamdulillah irin yarda kika dinga nuna b’acin ranki a fili idan na fa’da Miki magana ya tabbatar min baki aikata ba…” “ko?” Na ce masa ina turesa daga jikina ya ‘d’aga min kai yana saka hannu ya amshi cup d’in hannuna ya kai bakinsa gani na yi ya lumshe ido ya ce “Ma sha Allah.” Na yi tsaki na ce “Ka ajiye duk abinda za ka ce ba zasu yi tasiri a wajena ba, da gaske saki nake so…” Shiru ya yi yana cigaba da Shan kununsa bai kuma damu ba don sai sakin murmushi yake. Har ya gama sha tsaf ya mik’e yana lakace min hanci ya ce “Rigimaty, Am leaving, don naga yau a kusa kike bari na tafi Neman na kai, ki adana rigimarki ba yanzu ba sai second night, ban sani ba ko a lokacin zata Miki amfani…” Daga haka ya bani feck a kumatu ya fice da baya da baya kamar yarda ya Saba. Lumshe ido na na yi kawai ina murzar goshi na a zuciyata kuwa tunani nake Ustazu ya gama mayar da zancena wasa.

Ana idar da Sallahr azahar, Inna tana zaune tana lazimi muka ji nocking na amsa da k’yar da cewa Come In… Matar ta shigo sanye cikin dogon hijabi fuskarta sanye da nik’ab. Kallo na bita da shi ina son sanin wacece. Har ta iso gado na bata cire hijabin ba bayan ta gaishe da Inna da itama ta bita da ido. Sai da tazo bakin gadon nawa sannan ta d’aga nik’ab d’in. Ta d’an sakar min murmushi. Da k’yar na mayar mata don ban Santa ba, kamar ta shiga zuciyata sai Naga ta ajiye kwandon abincin a gefena ta ce “Ga sak’on da na kawo na San baki sanni ba, bari na baki wayar ki ji wacce ta aiko ni.” Ta latsa wayarta sannan ta kara min a kunne, muryar Mami na na ji tana furta “𝑨𝒚𝒔𝒉𝒂𝒕𝒐𝒖, ya jikin? Ga sak’o nan na bayar a kawo miki, ki tabbata naman ke kika cinye ko romo ba’a san wani ya lasa, shi yasa na sako a roba daban pls kada ki wasa da shi zaki gan shi a roba mai blue murfi d’aya mai Jan murfin kowa ma zai iya sha, ki kula sosai Allah ya bada lafiya…” Kafin na ce komai ta katse wayar. Jiki na na rawa na kalli matar da ta bu’de basket d’in ta Ciro exactly robar da Mami ta ce ta saka min a cinya a hankali ta ce “Maza ki cinye, don umarni ta bani kada na matsa ko nan da can sai kin gama tas, na tafi mata da robar….” Jikina ba inda ba ya rawa duk na shiga ru’dani….

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️

A yi hak’uri Kakata ce ta rasu, shi yasa gobe da jibi ba zan yi
Posting ba wannan ma don kada ku ji shiru ne. Kuma already ina da shi a k’asa. Na gode sosai da adduoinku gareni Allah ya saka da alheri👌
[10/16, 5:44 PM] Aunty Nazeefa 🥰: Wani irin Sarawa kaina ya yi, sarawar da na ji shi Har tsakiyar k’wak’walwata na runtse idona ina jin jiri na d’ibana. Tunani na guda menene wannan yaushe na aikata wannan abin da ko a mafarki ban san zan iya rik’e bindiga ba. Amma yau gani dumu dumu rik’e da bindiga. Kasa motsin kirki na yi don bani da k’arfin da zan iya motsa koda gashin idona ne balle wata gab’a ta jikina. Ina ji suka sanya min hand cuffs suka tasa k’eyata zuwa motarsu ta shiga ba biya fita da Allah ya isa. Da jiniya sosai muka bar cikin harabar gidan. Tuni zuciyata ta cunkushe waje guda. Bana iya tunanin komai sai na dama Allah ya d’au raina na huta da irin wannan rayuwar daga wannan masifa sai wannan, me yasa? Ni dai na San koda wasa bani ba ce a jikin Hoton nan Amma na San ko zan Mutu ina rantsuwa ba yarda za’a yi ba. Tsabar tashin hankalin da nake ciki yasa ko k’walla babu a idona illa iyaka idanun nawa Sun fito waje.
Chapter 27 · 0% Book details