← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 49

Sashe 48

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A toilet ta ganni ina ta kakarin amai tana shigowa Ustaz yana biyo bayanta. A tare suka dinga min sannu hakan ya bani dama na sake narke wa na kwanta a saman gadon ina mayar da numfashi. Mami ta kalli Ustaz ta ce “Kun je asibiti kuwa?” Ustaz ya d’aga mata kai hankalinsa duk a tashe. Mami ta jinjina kai tana furta “Sai a hankali shi ciki mai laulayi haka yake, Allah ya raba lafiya Amma dai AYSHA ki dinga daurewa. Jeka ka samo mata lemon tsami ta matsa a bakinta.” Da sauri Ustaz ya fita. Mami ta kama hannu tana min tausa a hankali. Wannan ne ya bani damar jefo mata tambayar da tun d’azu nake fargabar amsarta. “Mami kin koma gidan mu ne?” Ta girgiza kai fuskarta a d’aure ta ce “Ban koma ba, ba kuma zan koma ba, yanzu ma hutu na zo daga England.” Na turo bakina ido na suna cika da hawaye. Na janye jikina daga nata. mami ta bu’de baki tana kallona cike da mamaki ta ce “Au Har yau baki girma da shegiyar shagwab’ar taki ba?” Kuka na saka mata sosai bata rarrasheni ba kallo na kawai ta tsaya tana yi. Sai can ta ce “Da wannan sangartar AYSHA zaki haifi d’an da zaki masa tarbiyya?” Na turo bakina na ce “To ba na ce ki koma kin k’i ki koma ba?” Dariya ta tuntsire da ita kafin ta ce “MAFARKI DA BURIN AYSHA YA CIKA na koma gidan ku, me za ki ba ni?” Wani irin sufa na yi na shige jikinta
Cikin matsananciyar murna na furta “Alhamdulilah! Mami na
how comes Ban ji labari ba?” Ta gyara zamanta tana furta “Kawai dai na gaji da magiya da nacin Abbanki da Ummanki da Aiken da yake gidanmu, hakan yasa na hak’ura na koma. Bayan na tabbatar da nadamar Abban Ayshatu.”

Murmushi na saki ina goge hawayena bayan na gama jin bayanin Mamin AYSHA na komawa gidansu AYSHA.

Mami ta share min hawaye na, tana furta “Na sani AYSHA, na San duka zuri’ar gidan ku suna so na sai dai shai’dan da yaso ruguza dukkan farin cikin mu. Alhamdulillah a farko ya ci galaba akan wasu daga cikinmu sai dai ni tun a farkon da zuciyata ta yi zafi na zauna na yi tunanin ko nice a shoe d’in su irin zargin da zan yi kenan, sai na ji na samu nutsuwa, na kuma cire k’ullatar da na musu, na dinga addu’ar Allah ya bayyana gaskiya, Ya wanke ni da ni da ke daga zargin da ake mana. Alhamdulillah addu’a ta ta karb’u a lokacin da na yi tsammani.”

Na ja ajiyar zuciya bayan jin jawabin Mami. Na rungumeta a jikina ina jin tausayin abubuwan da aka dinga mata a wancan lokacin duka a kan laifin da ba nata ba. Daidai lokacin Humaira ta shigo turus ta yi sai kuma ta juya tana dariyar da ta riga ta zame mata jiki. Mami ta k’walla mata kira, Amma ta k’i dawowa ta furta “Ba ruwana Mamin AYSHA, ba mai shiga tsakanin uwa da y’a a sha hirar yaushe gamo lafiya…” muka yi dariya ni da Mami muna furta “Humaira kenan!” Mami ta ce “Ai Ummanta ta riga ta sangarta ta. Wancan satin fa kwananta bakwai a gida wai tana gudun mijin sai da Muhammad ya mata jan ido ta tafi.” Na ce “Mami ai baki ga komai ba, sai loakcin da ta dawo a bayan Umma nanik’e da ita take barci.” Mami ta ce “Ikon Allah, kamar ke kenan, da fa ba kya iya barci sai a jiki na.” Na yi murmushi kawai ina furta “Na fi samun nutsuwa ne idan ina jikin ki Mami, sai na yi barci hankali kwance,da ba kya nan fa da k’yar na Saba.” Mami ta ce “Ai hakan yana saka shak’uwa da soyayya tsakanin iyaye, idan mace ta yi aure kuma sai ta koma bayan Mijinta. Hakan yana saka soyayya mai zafi a tare da su. Ta yarda ko fa’da suka yi ba zai yi tasiri ba zasu shirya don ba zasu iya kwanciya ba tare da juna ba, ki kula da wannan Ayshatu.” Na jinjina kai. Ina rufe fuskta a jikinta. Ta d’aga kai na tana furta “Ke tsaya wai ni kike jin kunya? To ki cireta don a wannan zamanin idan uwa bata koya wa y’arta zaman aure ba tsaf za’a gurb’ata mata tunaninta don haka kika ga tun da bana jin kunyar koya Miki komai. Kada ki manta ni na koya Miki saka Bra pad da sauransu. A gabanki nake saka turaruka duka lungu da sak’o na jiki na don ki gani ki koya ke ma. Don haka ki cire wata kunya a ranki na gaya Miki.”

Sai dare suka shirya suka tafi. Duk sai na ji hankali na y’a tashi ganin za su tafin Har hawaye na yi. Ustaz ya ja hannuna duk sai na ga jikinsa a sanyaye shi ma. Sai da ya tabbbatar na ci abinci na sha magani sannan ya shiga wani bedroom na ga ya fito ya dawo ya zube a gaba na. Kansa ya saka a cinyata tsawon minti guda kafin ya d’ago. Idanunsa sun ka’da Sun yi jajur ya kama hannuna ya matse da k’arfin gaske murya na rawa ya ce “Zan tafi AYSHA!” Wani irin waro ido na yi zuciyata na bugu na ce “Zaka tafi ina?” Ya furta “Wajen Hameedah..”. Yana lumshe ido hankali na a tashe nake bin bakinsa da ya furta Hameedar da kallo. Zuciyata na ji tana wani matsanancin bugu don sai a lokacin na tuna ba ni ka’dai nake da shi ba. Cikin wata irin murya mai rauni na ce “Na shiga uku Ahmad wannan kuwa ba zai zama ajalina ba, wani abu nake ji a k’irji na….”

Jikar Nashe★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA….LAST PAGE💃💃 ALHAMDULILLAH……

Godiya ta musamman ga Ahalin gida na Musamman Wanda suka yi patronising NA GA RAYUWA. Na gode k’warai Allah y’a yi muku sakamako da mafi alherin sakamako. Sai y’an comment section da basa gajiya da suburbu’da comments . AYSHA, MAMIN AYSHA DA USTAZUN AYSHA NA GODIYA. 🥰

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Wani irin kuka na saki, ba na komai ba sai na zallar farin ciki da samuwar ciki a jikin Mami, abinda aka da’de ana nema. Na rungumeta sosai a jikina ina sakin kuka mai ha’de da murmushi… ina kallo Ustaz ya d’an saki murmushi ya fita waje. Umma ma cikin dariya ta ce “To meye na kukan? Madadin ki dinga furta Alhamdulillah? Ai godewa Ubangiji shine abinda ya kamata yanzu.” Ajiyar zuciya na saki na ce “Kukan farin ciki ne Umma, wallahi ban tab’a Jin irin farin cikin da nake ji yau ba.” Umma ta ce “Na sani Aysha, haka kowa ma yake wannan farin cikin, duka gidan nan murna muke da wannan lamari mai girman gaske, wa ya isa ya maka wannan banda buwayi gagara misali a sanda ka cire rai a lokacin kuma Allah ya kawo saboda ya nuna mana komai akwai lokacinsa, fatanmu Allah ya raba su lafiya.” Na ce “Ni fa da Umma na yanke shawarar da zarar na haihu zan dank’awa Mami abinda na Haifa wallahi. Ta raine shi kamar yarda ta raine ni.” Mami murmushi ta saki ta ce “Ai ko yanzu ma zan yi farin ciki Aysha idan kika ba ni na raini jika na na farko.” Na saki murmushi na ce “In sha Allah Mami. Sai su tashi just like twins shi da Uncle d’insa.” Haka muka zauna aka dinga hirar Mami cike da farin ciki muna shirya irin gagarumin taron sunan da za’a yi. Sai dare Ustaz yazo muka tafi gida ko a gidan ma na ishi Ustaz da zancen cikin Mami. Shi dai murmushi kawai yake.

Bayan watanni shidda……..

Abubuwa da dama Sun faru Sun wuce. Wasu masu da’di wasu kuwa sai dai godiyar Allah. Sosai nake samun kulawa da tattali da soyayya wajen Ustaz da yake ji kamar ya mayar da ni ciki. Ko motsin kirki baya bari na na yi musamman girman cikin ya isa kwatance. Nauyinsa nake ji sosai, ya kumbura ni ya sauya min duk wata halitta da take jikina. Shirin tafiya yake mana zuwa Egypt don na haihu a can, tafiyar da yake shirya mana har da Mami na, da Mommynsa sai Khadija k’anwarsa da zata taya ni zama a can.

Barcin la’asar sakaliya na ke sosai a parlor kan wata kujera mai taushin gaske. Na ji kamar ana ja min hanci hakan yasa na Ware ido na ina kallon Ustaz da yake tsaye sai murmushi yake min fuskarsa cike da walwala. Ya mik’a min hannu. “Taso y’ar beauty…” dariyar da yake ne yasa na san tsokanar da y’a Saba min zai min, hakan yasa na turo bakina. Tunda cikina ya tsufa yake tsokanata da sunan Beauty. Zama ya yi yana rab’ani da jikinsa ya furta “Sowie dear, albishir fa nazo Miki da shi k’in saka zan manta.” Da sauri na kalleshi na ce “Albishri d’in me?” Ya ce “Ke dai albishirinki…” na ce “Goro.” Bakinsa ya nuna min yana murmushi hakan yasa na manna bakina da nasa don na San abinda yake nufi. Kyakykyawar kiss na bashi. Ya lumshe ido yana murmushi ya sake ja min hancina da ya tashi sosai ya furta “Aysha cikin nan ya maki kyau, ji fa hancinki da bakinki yarda suka sake doubling size d’in su.” Pillow na d’auka na wurga masa ina turo baki na ce “Ustazu bana so!” Murmushi ya saki yana furta “Ayshatu, ina so. Ba kya son na gaya Miki albishir ‘din?” Na turo bakina ido na ya yi raurau don gani nake kamar da gaske Ustazun muni na yake gani. “MAMIN AYSHA.. ta haifi twins Girls….” Wani irin waro ido na yi kafin na ce “Are serious Ustaz?” Ya d’aga min Kai yana murmushi ban San sanda na isa na rungume shi ta baya ba ina furta “Ka zo min da kyakykyawan albishir I love you dear…” Shukaran lillah.. ya furta a hankali yana pecking goshi na. Da Kansa ya zira min Hijab muka fita don zuwa wajen Mami na da nake jin kamar na yi tsuntsuwa na je wajenta.
Chapter 48 · 0% Book details