← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 49

Sashe 13

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Magani Umma ta sake bani, bayan na sha tea na yi sallahr Isha’i wani barcin ne ya sake d’auke ni. Abin mamaki ban tashi farka wa ba sai da Umma ta tashe ni sallar asuba. Ina ji a cikin maganin da aka bani har da na barci tsaf na tashi kaina baya ciwon da yake min, sai dai d’an jiri da nake ji na rashin cin abinci. Sai da na idar da sallah Umma ta dubeni tana amsa gaisuwata ta ce “Abbanki yana buk’atar jin shawarar da kika yanke, akan komanki gidan Ahmad, ni dai idan har zan baki shawara ki d’auka a matsayina na wacce ta kawo ki duniya zan ce miki ki koma gidan Ahmad, ba don komai ba sai don na san zai rik’eki da mutunci, na yi mamaki ma da ya dawo neman komawa aurenki duk da abubuwan da suka faru. Saboda haka ina jin ki don jiya da zasu kawo sadaki ma ya ce a bari a ji ta bakin ki… shin kin amince?” Wani irin runtse ido na yi ina cije leb’ena da k’arfin gaske kamar zan huda su, ina ji a raina bana son Ahmad amma kuma yana yak’i da zuciyar da take son saka ni bujirewa umarnin su Abba, Nasihar Ya Usi tana ta dawo min a zuciyata. Muryar a dake na ce “Na amince..” Sai naga Umma ta saki ajiyar zuciya ta saki murmushi ka’dan ta ce “Allah ya miki albarka, yasa a ce gwara da aka yi. Alhamdulillah Allah ya k’ara shiryaki ya shirya dukkan lamarinki.” Ta mik’e ta fita cikin walwala da farin ciki ni kuma ta bar tawa zuciyar cikin matsanancin k’unci da b’acin rai, ina jin yarda yanayin bugun zuciyar tawa yake sauyawa na lumshe ido ina ji a raina na amince zan koma gidan Ustaz ba don komai ba sai don na wanke kai na daga zargin da yake min, daga ranar kuwa da ya kusanceni ya ji ni a matsayin budurwa wallahi daga ranar zan b’alle kayan yak’i na har sai ya gwammaci ki’da da karatu. Sai kawai na saki murmushi ina gyara kwanciyata. Har a zuciyata ina jin shawarar ta yi min daidai yarda nake so.

Daga ranar da na amince da auren Ustaz shikkenan na samu sakin fuska sosai daga wajen mutanen gidanmu. Ciki kuwa har da Abba aka karb’i sadaki na a karo na biyu daga iyayen Ustaz. Gefe guda ni ka’dai na san wutar da zuciyata take kunna min akan lamarin auren. Aka sake d’aura aurena da Ustaz ba tare da na sake bari ya ganni ba. Shima tunda ya zo sau d’aya na fita na mak’ale a waje ban je wajensa ba bai sake dawowa ba. Na tattara lamarinsa na watsar na dinga tunanin kalar ramuwar gayyar da zan masa. Da daddare ina zaune a d’aki Umma ta shigo tana kallo na ta ce “Gobe ki fara zuwa gyaran jiki AYSHA kin ga zuwa nan da kwana biyar za ki tare.” D’aga mata kai na yi kawai. Ta kawo wani cup cike da madara kindirmo da magani da na tabbatar na mata ne a ciki ta bani. Godiya na yi na karb’a ina sha. Idan kin gama Aysha ga turaren tsuguno nan ki zuba a garwashi ki yi.” Na d’aga mata kai kawai. Don abinda zata bani bana k’in amfani da shi don na san amfaninsu kuma da wannan damar nake son Jan Ustaz a k’asa har sai ya gane shayi ruwa ne don na yi alk’awarin auren d’and’ani haukaci Zan masa, nemana zai yi ya rasa ko na maka shi kotu ya sake ni.

Bayan fitar ta da 1 hour sai gata ta shigo. “Aysha Ki je ga Ustaz can a falon Abbanki…” Zuciya ta naji ta hassalo wato don ya san bana zuwa wajensa shine yau ya shigo har Parlorn Abba. Na tsuke fuskata kafin na yafa mayafin doguwar rigar da take jikina raina a b’ace na shiga d’akin ko sallama ban masa ba… Gani na yi ya mik’e tsam ya iso inda nake yana wani sakin murmushi. Na juya zan tafi na ji ya fisgo ni da k’arfin gaske na fa’da jikinsa. Ture shi nake da k’arfin gaske amma bai bani damar kub’uta ba, kawai na ji tattausan lips d’insa a saman nawa. Sai da tsotsa son ransa sannan ya janye jikinsa yana zama saman kujera hannayensa a cikin gashin kansa yana burkita gashin, idanunsa a lumshe. Takaici ya isheni a zafafe na ce “Allah ya isa kissing d’ina da ka yi, mugu kawai!” Ya ware birkitattun idonsa a kai na sai naga ya saki murmushi ya ce “Me ye a cikin lips d’in naki? Leb’e da k’arti suka gama tsotsewa kin zata lallab’a ki zan yi, ki shirya duk ranar da kika shigo gidana sai na fanshe wahalar da kika ba ni, kafin nan ki shiga ki saka hijabs zan kai ki gwajin H.I.V….” Cak na ji zuciyata ta tsaya da bugun da take idona da kunnena kuwa kamar basa aikin da ya kamata idanuna a burkice na nuna shi da yatsa bakina na rawa na furta “In dai kai d’an halak ne Ustaz ka sake saki na yanzun nan a karo na biyu, bana son ka ba tsaneka kuma ba zan tab’a komawa gidanka ba Ahmad ko kai ne Autan Maza!

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️

08033748387.
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 32.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Ban san me ya ce da Yaya Muhammad na dai ji Ya.Muhd ya ce “Ke Aysha!” na juyo fuskata a masifar d’aure “Ba zaki gaishe shi ba?” daga shi har Ya.Muhd d’in na musu wani banzan kallo na sake juyawa na yi wucewata cikin gida idanuwa na suna shirin zubar da hawaye. Ban bar ko Umma ta ganni ba na yiwa kaina masauki a cikin d’akina ina mayar da huci idona a runtse nake tunanin Uban me ya kawo Ustaz kuma gidan mu? Shin akwai sauran alak’a ne a tsakaninsa da gidan mu? Ban dawo daga tunanin da nake ba na ji Yaa Muhammad yana tambayar ina nake? Ina ji Umma ta ce tana cikin d’aki, wani abin ta yi ne na ga kana ta b’ata rai…” muryarsa cike da takaici ya furta “Kin ga kallon banzan da ta yiwa Ahmad, kamar wata mara hankali…” bai saurari Umma ba ya bugo door d’in d’akin da wani irin k’arfin gaske. Idanunsa a kai na yake zuba wani irin kallo, kafin ya k’arasa cikin d’akin fisgo ni ya yi da k’arfin gaske yana min kallon cikin k’wayar ido… “Wa kika gani kika wulak’anta, kina da hankali kuwa, are you out of your senses da ina maki magana zaki kalleni with your shameless eyes ki juya ki tafi…” Turo baki na na yi don kam wallahi sai dai ya kashe ni idan akan wancan mutumin ne da ko sunansa bana son na dinga ji a rayuwa ta. “Kin zata zuwa ya yi biko da kika nemi ki disgracing d’insa?” Sai na ga ya ciji bakinsa ya furta “Ba biko yazo ba, at all ma ba wajenki ya zo ba yazo kawowa su Usman gudumawar biki ne marar kunya har kika nemi wulak’anta shi…me zai yi da ke?” “Nima me Zan Yi da shi ko maza sun k’are ba zan sake kallonsa a matsayin masoyi ba sai dai gagarumin mak’iyi.” Ya.Muhd tsayawa ya yi yana kallona with a lot of surprises a kan fuskarsa sai na ga ya yi dariya kawai ya furta “Rubbish!” Ya fice daga d’akin. Ina ji yana sake bawa Umma labari, Umma bata ce komai ba ta ce Allah ya kyauta.

Da daddare sai ga Yaya Usman ya shigo d’akin da nake da fara’a fal fuskarsa ya zauna a gefen gado yana kallo na. “AYSHA ya naga mood d’inki ya canja?” Sai sannan na samu hawayen da yake idona ya fara suntiri na fara basa labarin abinda ya faru. Madadin ya ji haushi sai naga ya yi murmushi ya ce “AYSHA Ustaz fa bai cancanci haka a wajenki ba, kada kiga ya banzagatar da lamarinki kullum wallahi a cikin maganarki ya ke, har group muka ha’da na whatsapp da shi da y’an mazan gidan nan duk akan matsalarki muna so mu gano menene zahirin gaskiya, sannan da saka hannun Maminki a ciki ko bab…” Kallon da na masa ne ya saka shi jan bakinsa ya yi shiru yana dariya k’asa k’asa ya ce “Idan biko yazo Ai sai a ha’da da namu kawai a d’aura ki koma gidansa shikkenan baki alaikum…” Da sauri na ce “Ashe kuwa za’a kai Gawata gidan Ustaz don wallahi tsaf zan kashe kai na…” Ya.Usman waro ido ya yi ya ce “To Allah ya rufa asiri, yanzu ma fa zuwa na yi na gaya miki kyautar motoci ya kawo mana masu masifar kyau ni da Umar matsayin gudumawarsa da zunzurutun ku’di…..” Da sauri na saka hannu na na rufe masa bakinsa, ina girgiza kai na ce “Ya.Usman don Allah tashi ka fita, bana son jin komai….” Na fa’da idona a runtse ina zubar da wasu zafafan hawaye. Shiru Ya.Usman ya yi kafin ya mik’e jikinsa a sanyaye yana furta “Take heart AYSHA ba wai nufi na ki koma gidan Ustaz ba…” Ban bi ta kansa ba na mik’e a guje na koma cikin toilet ina mayar da wani irin nauyayyan haki.
Chapter 13 · 0% Book details