Sashe 5
Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yamma kuwa ina kitchen Yaya Usman ya shigo. Ina ganinsa na saki murmushi alamar farin cikin zuciyata ya kasa b’uya. Ledar hannunsa ya mik’a min kafin ya furta “Ta samu kenan ko Aysha naga fuskarki fal fara’a.” Murmushin na sake yi ina furta “Ya.Usi dama tun safe nake nemanka.” Ya k’araso wajena yana murmushin don yanzu da sauk’i Umma ta daina hana shi yi min magana. Ya furta “Gaya min Aysha me ya faru?” Na gyara tsayuwata ina ajiye wuk’ar da nake yanka cabbage. Na ce “Ya.Usi na gano wanene ya min duk sharrin da kuke cewa na aikata…” Da sauri ya ce “Wanene Aysha gaya min na je naci Ubansa!” Na d’an girgiza kai kafin na ce “Aljanni ne Ya.Usi, Aljanni ne…” Kallon da yake min ne yasa ni ha’diye sauran maganar, gaba d’aya idanunsa sun bayyana rashin yarda da zance na. Amma sai naga ya saki murmushi ya girgiza kai ya ce “Aljanni kuma Aysha? Ta yaya kika san Aljanni ne duk ya aikata hakan?” Idona na ji suna tara k’walla kafin na fara bashi labarin mafarkin da na yi. Shiru ya yi yana kallo na kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Mafarkin Aysha zai iya zama Aljanni zai kuma iya zama ba Aljannu ba, zai iya zama wani abu Allah yake so ya nuna miki, amma duk da haka ba zan bar maganar haka ba, zan samu Umma da maganar idan yaso sai na kai ki wajen ruk’iya don a yi miki a duba idan da Aljannin ko babu..” Na d’aga kai ina furta “Na gode Ya.Usi” muryata a shak’e. Ya mik’e min ledar hannunsa abinda ya saba kawo min ne time to time yau d’in ma ya kawo min. Yoghurt ne mai sanyin gaske da kazar yahuza. Cikin farin ciki na sake masa godiya ina kallo ya juya zai tafi. Yana furta “Idan kina son mu cigaba da shiri, ina son ki zama Good girl, ki yi ta istigfari kin ji…” Gaba d’aya jikina naji ya yi sanyi ganin da gaske shima Ya.Usi bai yarda da ni ba, yana kula ni saboda shi mutum ne mai sanyin hali ba kamar sauran y’an uwana ba. Na tuna ranar da ya rutsani da son na gaya masa gaskiya. Rantsuwa na masa da girman Alk’ur’ani akan ni dai a hayyacina ba wani namiji da ya tab’a rik’e min ko hannu bayan Ustaz.” Shiru ya yi sai kuma yasa hannu yana shafe min tarin k’wallar da take zubo min. Ashe dai Yaya Usi duk abinda na fa’da har yanzu bai amince da ni ba. Yanzun ma kukan na yi na kuma share hawaye na ba tare da kowa ya lallashe ni ba.
Bayan sallahr Isha’i, sai ga shi ya shigo d’akina. Jikinsa a sanyaye ya furta “Zo Aysha mu je ki k’ara maimaita mafarkin ki a gaban Umma, ina fatan wannan ya zama k’arshen wahalar ki.” Na mik’e ina addu’a a raina, Allah ya biye bakinsa ya sa k’arshen wahalata ne ya zo.
Ko da muka isa ya fara gaya mata, kafin ya ce Aysha gaya mata irin mafarkin da kika ce kin yi..” Na gyara zama na shiga gaya wa Mami ina gaya mata murya ta tsaf ba don komai ba sai don ta yarda da ni. Wani kallo ta dinga min, kallon da ya dinga saka ni jin kamar jijoyin jikina suna tsinkewa tsabar sanyin da gab’ban jikina suka yi. Wani murmushi ta yi ta ce “Aljanni ko? Kai kuma Usmani sai ka yarda da labarin k’anzon kuregenta, mak’aryaciyar banza, ka zauna ta wahalar da kai a banza…” Yaya Usman fuskarsa ta nuna rashin jin da’din abinda Umman ta ce ya ce “A’a Umma, kada ki ce haka ki bari a je a ji ta bakin Malamin kafin ki yanke hukunci duka zancen AYSHA zai iya zama gaskiya fa….” Umma ta tab’e baki ta ce “Ai ban hanaka ba Usmanu, abu guda na sani k’arya take kuma zaka ce na gaya maka, b’ata lokacin ka kawai zaka yi… amma ma ji ma gani wai an bawa mai kaza kai.” Daga haka ta shige d’akinta ta bar mu ni da Ya.Usi fuskokin mu cike da damuwa, da gaske lamarin Umma mamaki yake ba ni.
Yaya Usman ya ja hannuna a fusace, Yana furta “Mu je Aysha, Allah ya bayyanar da gaskiya a lokacin kowa zai gane abinda aka miki baa kyauta ba.”
Wani murmushi na saki ina raya ranar kuwa da kallo don babu wanda zan ragawa, don ni ba a tausaya min ba a lokacin da nake son a tausaya min. Za su sha wuya k’warai da gaske kafin su shawo kai na.”
A machine d’insa muka tafi gidan Malamin da zai min ruk’iya. Babban Malami ne k’warai da gaske,wanda ya shahara a b’angaren cire Aljannu. Muka ci sa’a kuwa babu kowa sai mutum biyu kacal a wajen. Daga ganin Malamin zaka san addini ya ratsa shi. Bayan Yaya Usman ya gama gaya masa abinda ya kawo mu, sai ya umarce ni nima akan na sake masa bayanin irin mafarkin da na yi. Ban yi nawar baki ba na sanar da shi komai. Da duk abinda na gani a cikin barcin. Cikin ta’ajjabi yake girgiza kai yana kallo na ya ce “Usmanu tabbas zai iya zama Aljannu ne da k’anwarka, zai iya kuma zama bata da Aljannin wani lamari Allah yake son bayyana mata a cikin barcin. Ba zamu gane hakan ba sai ta hanyar Ruk’ya, kana ganin a yi mata yanzu babu matsala?” Usman ya girgiza kai ya ce “Ba matsala Ya sheikh, sai dai da zai yiwu na fi son a yi a gida a gaban iyayenmu don su tabbatar duk abinda aka ce ‘din da gaske ne…” Malam ya girgiza kai ya ce “Haka ne, yanzu abinda za’a yi zuwa da safe In sha Allah ka min kwatancen gidan naku zan je na yi mata In sha Allah a can, tabbas wannan lamari akwai sark’ak’iya a cikinsa.” Ya.Usi ya yi godiya ni ma godiyar na masa, sannan muka mik’e muka tafi.
Da muka je gida wani irin kallo Umma ta mana sai kuma naga ta yi murmushi ta ce “Usmanu, har an cire Aljannun? Guda nawa aka cire?” Usman ya d’an tsuke fuskarsa murya a cunkushe ya ce “Baa mata ba sai gobe zai zo a yi a nan, amma fa Umma bana jin da’din yarda kike yiwa AYSHA sai kace ba ke kika haifeta ba, kin banzagatar da lamarinta, komai ta yi Ai kamata ya yi ki ja ta a jiki ki ji dukkan matsalolinta.” K’asa naga Umma ta yi da kanta sai naga hawaye na ‘diga a idonta ta girgiza kanta ta shige d’aki ba tare da ta yi magana ba. Ya Usman ya kalleni ya girgiza min kai kawai shima ya ce “Aysha Umma na son ki, kuma tafi kowa son dukkan abinda ya faru ya zama sharri, a hakan da kike ganinta dauriya kawai take tana cijewa abinda yake damun zuciyarta yana da yawa Aysha. A idanun Umma nake hango tausayinki da k’aunarki..” Na share hawayena Usman ya ce “Ki tashi ki tafi ki kwanta ki huta.” Ban musa masa ba, don tabbas ina buk’atar hutun na zuciya k’wak’walwa da gangar jiki gaba d’aya. Don haka na shige d’akin da ya zama mallakina.
Kashegari k’arfe tara na safe Ya.Usman ya shigo da Malam Sitroom. A tsakargida Abba ya fito daga sashensa yana furta “Ka kiyaye ni Usman, wani Aljannu ne da Aysha da zaka kawo min Malami gida?” Ya.Usman ya marairaice hakan yasa dole Abba ya shige sitroom d’in. Nima Ya.Usman ya ce na mik’e na shiga. Da sallama na shiga parlorn cikin zumbulelen hijabi na mai tsaho da fa’din gaske, irin wa’danda na saba ta’ammali da su… Malam yana kallo na ya ce Sannu Ayshatu Baiwar Allah, In sha Allah yau Ubangiji zai nuna mana gaskiyar lamari…” Sosai na ji da’din kalaman Malam, Saboda cikin tausayawa da tausasawa ya yi furucin. Na ayyana dama haka iyayena suke min da zuciyata bata shiga cikin k’unci da ciwon da take ciki yanzu ba. Malam yasa na mik’e k’afata kafin ya ce Ya.Usman ya rik’e manyan yatsuna na k’afa guda biyu. Ya dubi Abba ya ce. “Alhaji kada ka yi mamaki a ce maka duk wani abubuwan shai’danun Aljannu ne suka aikata, suna yin fiye da hakan, Ubangiji ya yassare musu wannan baiwar ta riki’da dukkan suffar da suke..” Abba ya girgiza kai yana furta “Allah yasa hakan ya kasance.” Malam ya ce hakan ne ma In sha Allahu.”
Sannan ya fara rero karatun Ruk’iyyar…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 27.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Tsawon rabin awa Malam yana karatun, sai dai ko gezau ba abinda na ji, ba kuma abinda ya canja a jikina. Malam ya dubeni ya ce “Ayshatu ba ki ji wani sauyi a jikin ki ba? Ba ki ji tsigar jikin ki ta tashi ba? Ko jiri da ciwon kai haka?” Na girgiza kai na da sauri na ce “Ban ji ba Malam.” Sai na ga ya bu’de wata kwalba ya yarfa min wani turare a cikinta.. wani irin turare mai warin gaske mai hauka kai. Tsawon mintuna biyar yana kallon cikin k’wayar idona. Sai na ga ya girgiza kai yana sakin ajiyar zuciya ya kalli Abba ya ce. “Abin mamaki, Alhaji ba Aljannu a jikin yarinyar nan.” Abba ya saki wani malalacin murmushi wanda daga ganinsa ka san na b’acin rai ne da karayar zuciya ya furta. “Dama Allah ya gafarta Mallam, don kada ka ce na k’i yarda da abinda kazo da shi ne, amma ni na san ba wani Aljanni a jikin yarinyar nan, shai’dananci ne kawai irin na yaran Zamani. Da kuma tsagwaron ta rainawa mutane hankali ta zauna ta shirya zancen wai ta yi mafarki.” Ya ciji leb’ensa yana bi na da kallo. “Ga shi nan yanzu kun yarda da kan ku, na yi mamakin kai da Usmanu da kuka yarda da tatsuniyar yarinyar nan wanda dama k’arshenta shine k’urunk’us! Ta shi ki ba mu waje Munafukar banza…”