← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 49

Sashe 38

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na shiga Motar Ya Usman zuciyata na min wani irin nauyi, don har sai da na sauke ajiyar zuciya a hankali. Yaya Usman ya juyo yana kallona bayan ya tada motar ya ce “Yaya dai AYSHA?” Na girgiza kai na ce bakomai. Ina bayan motarsa matarsa kuma a gaba haka muka yi tafiyar. Ina ji jefi jefi suna hirarsu wani zubin su sako ni. Sai dai bana tofa musu na yi shiru kawai saboda tunanin da y’a cika min zuciyata ba zai bar ni na yi walwalar da zan amsa musu ba.

Har muka isa potiskum ban sani ba ni dai ina zaune jigum cikin mota duka tunani na yana kan motar Ustaz da duk sanda muka zo wuce su sai na hango fuskarsa da ta Humaira fal farin ciki da walwala. Bayan motarsa kuwa Yaya Muhammad ne da Anty Khadija da ta kafe sai tazo duk da tsohon cikin da take da shi. Mune farkon isa potiskum d’in don haka Hajiya da murna da karsashi ta tare mu. Ta dafa ni ta ce “Kaga Baiwar Allah, tun d’azu nake zuba idon ganinku ina y’ar Uwar taki?” Kafin ta rufe baki Humaira da su Umma suka shigo. Hajiya ta bu’de baki cike da mamaki tana furta “Hukumullahi La ajabun…. Ikon rabbi ya shige misali wannan kam ko a hanya na ha’du da ita zan k’walla mata kira da sunan Ayshatu. Ki ga kama ba banbanci ko ka’dan…”Umma tana dariya ta ce “Aa fa Yakumbo akwai banbanci na ‘dabi’a a tattare da su, Humaira akwai d’an banzan rawar kai, da yawan surutu Aysha kuwa miskila ce ta bugawa a jarida.” Ina ji duka wajen suka shiga furta tabbas. Na d’ago ina kallon Ustaz da sam bai tofa ba yana ta danna wayarsa. Ya Muhammad ya ce “Wallahi gaskiyarki Umma, Humaira akwai sakewa da jama’a Aysha kuwa akwai nurk’ifanci.” Na turo baki na cikin jin haushi ina kallon Abba da yake murmushi shima ya ce “Humaira kam ba dama surutu fa kamar aku.” Ai kuwa Humaira ta fara turo baki tana shirin saka kuka, Yaya Faruk y’a kama hannunta yana furta “Common my friend, kada kiyi asarar hawayenki a banza, ai gwanda mai irin halinki Sun fi da’din zama. Me za’a yi da mutum mai k’unbiya k’unbiya.” Na kuwa zuba masa harara don na San wannan maganar kansa tsaye da ni yake.

Kwana guda muka yi a potiskum muka yi sallama da Hajiya da niyyar ana fara shirye shiryen biki zata taho.

Kwana biyu da dawowarmu kuwa aka fara hada hadar saka rana. Wani abu da Abba ya yi ya burgeni ha’da su Yaya Muhammad su biyar da biyar daga cikin y’an matan nan. Masu mata ya k’ara musu d’ai’daya marasa mata kuma ta basu auren d’aid’aya daga cikinsu. Yaya Ali ne kawai aka ce ya yi k’ank’anta da aure don haka sauran biyun Malaman mu suka nemi aurensu Abba kuma ya amince da su ya basu auren don haka duka yau za’a saka ranar biki ciki kuwa har da na Humaira da Ahmad Ustazu na.

Ranar kam Allah ne ka’dai ya san yanayin da zuciyata take ciki. Duk da k’wayar idanuna ta kasa b’oye nakasar da zuciyata take ciki.

Y’an saka ranar da suka zo Har da y’an gidansu Ahmad su Khadija da Aunty Doctor Khadija ta saka ni a d’aki tana tuhumata me yasa na k’i amincewa komawa gidan Ahmad? Suka ji labarin da k’anwata kuma za’a yi auren. Na bita da kallo ina sakin ajiyar zuciya kafin na ce “K’addara ce!” Duk abinda ta ce kuma na kasa bata amsa Har ta gaji ta yi shiru.

Zo kuga lefen Humaira, akwatina goma sha biyu har da na saka rana. Akwatina ne manya kuma masu masifar kyau. Kaya ne damk’ar a cikinsu masu masifar kyau da tsada. Kai daga gani ka San dukiya ta yi kuka. Wata uku aka saka cif. Humaira sai rawar kai take ita ko kunyata bata ji. Wannan iyayi da take shine abinda yake sake dugunzuma zuciyata. Hakan yasa na shige d’aki na fasa kuka mai tsima zuciya. A wannan daren kam cire duk wani girman kai da miskilanci na na yi na d’au waya na danna numberr Ustaz, yarda wayar take bugu haka k’irjina yake bugu sosai na tashin hankali tsawon lokaci kafin ta d’aga wayar……. Cikin k’arfin hali na furta “Hello Ustazu na….”

𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[10/16, 5:45 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA…..58.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

Na fa’da a hankali cikin muryar nutsuwa. Shiru ya yi kafin daga can gefen ya ce “Humaira me yasa kika d’aukar wa AYSHA waya?” Wani takaici ne da zafin k’irji na ji yana shirin babbaka zuciyata wato ya zata Humaira ce. Na cije leb’ena kafin na yi k’asa da wayar jin yana cewa “Maza Humy mayar mata da wayarta zan shigo da safe na ji damuwarki yanzu Am with my wife…” k’it na kashe wayar tafarfasa kawai zuciya ta take yi. Ban san me yasa na kasa hak’ura da Ustaz ba, alhali yanzu ta bayyana k’arara ba so na yake ba. Hankalinsa da tunaninsa kacokam yana kan Humaira. Ranar kam da ky’ar na samu na yi barci.

Da safe kuwa ban fita daga d’akin ba. Maryama ta shigo tana kallona ta ce “Sis AYSHA Abba yana kira.” Kai kawai na d’aga mata kafin na mik’e na zira hijab d’ina na fice zuwa amsa kiran Abba.

Ina saka kai gaba na na wani irin bugawa da k’arfin gaske ganin Abba ne da kafatalin y’an uwansa da alama wannan meeting d’in duk nawa ne. Kai Ni AYSHA na ga rayuwa. Cikin rawar murya da kasalar jiki da na zuciya na shiga babban parlorn kai na a k’asa. Fuskarsu sam ba annuri suke kallo na. A takure nake sosai musamman irin kallon da suke min mai sanya rashin nutsuwa ko ka’dan.

Bayan Sun amsa gaisuwata Usual murya a cunkushe sai kuma Baba Yahya ya gyara zama yana furta “Ke wannan zaman naki ne, saboda wata magana da muka ji wai zaki jingine maganar aure ki tafi wata uwa duniya karatu, haka ne?” Na d’aga kai a hankali ya gyara zamansa ya ce “To baki isa ba, kin yi ka’dan mu dai a zuri’armu kaf ba wata mace da zamu bari ta tafi karatu waje. Don haka ki bu’de kunne da kyau mu gaya Miki da zarar kin gama idda zaki fitar da miji mu Miki aure tunda ke kin kafe ba zaki koma gidan mijinki ba, har ta kai ga rabuwa an Maye masa gurbin ki da y’ar uwarki to hakan ba zai baki lasisin da zaki zauna ki mik’e k’afa ba.” K’asa furta komai na yi sai ruwan hawaye da yake ambaliya a fuskata. A haka suka sallame ni na mik’e jikina har rawa yake na tafi cikin d’aki na. Zuciyata na ke furta na shiga uku, na jawowa kai na masifa me ya kai ni furta bana son Ustaz na San halin su Baba yahya da kafaffiyar zuciya. Tunda suka furta sai na fitar da Miji abu ne mawuyaci su janye furucinsu.

Kaina ya yi dum, sakamakon rasa mafita da na yi, a lokacin kam na San tabbas na yi rashin uwa Mami na da ta nan da na San ba zata bari a k’wace min Miji a bawa Humaira ba. Ita kuwa Umma murna ma take don k’iri da muzu ina jinta ranar tana gayawa K’anwarta ita hankalinta ma zai fi kwanciya Humaira ta auri Ustaz ta San zai kula da ita da tarbiyyarta ma.

Na runtse idona hawaye na zuba kamar da bakin k’warya a idona. Numberr Mami na shiga latsawa ta can k’asa da Hajiya Mama ta bani. Cikin sa’a na samu Mami na, tana d’agawa na fashe mata da kuka ina furta “Mami na shiga wani hali, Na ga rayuwa Mami na wai Humaira za’a aurawa Ustazu na…” “What? Saboda Uban me?” Na ji Mami ta furta cikin muryar da ta bayyana tashin hankalinta. Na lumshe ido ina gaya mata duk abinda ya wakana. Sai na ji ta saki ajiyar zuciya ta ce “Ke ma AYSHA kin yi wauta, a wannan zamanin ta ya zaki furta hakan? Ustaz fa maza ne masu tsada da sai mace mai muguwar sa’a take samunsu. Ko da da kika ga ina Adawa da aurenki da Ustaz don bani da wani burin da ya wuce naga kin yi karatu ne. Amma na San ta ko ina Ahamad ba shi da makusa. Yanzu wannan nurkufancin naki zaki cire ki samu Umma ki gaya mata kina son mijinki zaki koma gidansa ita sai ta samu Abba ta gaya masa amma idan kika ce zaki shiru kina ji kina gani zaki rasa Ahamad Humairan ta aure shi…” na d’aga kai zuciyata ta amince da shawarar Mami na. Na mik’e da sauri na nufi d’akin umma. Ita da Humaira ne a zaune Humairan sai sangarta take mata. Kayan kitchen ne a gaban su suna ta warewa. Jikina a sanyaye na shiga na zauna a gefen gadon, ina nazarin fuskokinsu da suke
cike fal da walwala da alama koma zancen me suke suna cike da nisha’di.
Chapter 38 · 0% Book details