← Book details Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 49

Sashe 6

Naga Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni murna ta ta koma ciki, wani sanyi ya ziyarci zuciya da gabban jikina, na dinga jin rauni a tare da ni. Ban san ya aka yi na kai kaina bakin k’ofa ba, ina ji dai Malam yana cewa “Alhaji ku bita a hankali, tsangwama da kyara ba shi zai gyara ta ba sai addu’a da kuma janta a jiki.” Lumshe idona na yi ina datse leb’ena ba don komai ba sai don zantukan Malam sun tabbatar min da cewa, shi ma ya yarda ni d’in tantiriyar y’ar iska ce. Hakan ya sa wani hawaye ya dinga sulmiyo min na ayyana yanzu haka shi ma Yaya Usman daga rana irin ta yau ya fita daga sabgata shikkenan na tabbata Ni Ayshatu Na ga rayuwa. Umma ko ko bi ta kaina ba ta yi ba bayan wani banzan kallo da ta yi min da na fito daga parlorn Abban ta furta “An cire Sarkin Aljannun a kan ki? Haba wa ni na san ba ta yarda za’a yi Aljanni ya rab’i zuriyata ba alfahari nake ba, amma addu’oin tsarin da nake muku tun kuna ciki da girmanku ba zai bar Aljanni ya kusanceku ba, sai dai idan ke ce Aljannar kan ki.”

Tun daga ranar ban sake saka Yaya Usman a idona ba. Ba ya nemana ledar da yake kawo min ma tuni ya daina kawowa. Wannan shine abinda ya fi d’aga min hankali.

Ranar yau Asabar Anty Khadija matar Ya.Muhd da matar Ya.Sadik suka zo. Da murna ta na tare su cikin tsananin farin ciki. Anty Khadija ma da fara’ar ta rungume ni tana kallon jibgegen zanin gadon da nake wankewa da brush a tsakargida. Sai naga ta d’an jijjiga kai kawai fuskarta a tsuke ta ce “Asysha ke kike wanke wannan kuma?” Ban bata amsa ba na yi murmushi kawai na juya ina kallon matar Ya.Sadik da take bina da wani kallon banza tana yamutsa baki. “Ina yini?” Na furta cike da mamakin kallon da take min. Kamar wacce aka yi wa dole ta amsa tana d’age kai. Ba tun yau na fuskanci sam Yaya Sadik bai dacen mata ba, tana da isgili girman kai da izza. D’auke kaina na yi ina kallo ta shige cikin part d’in Umma na saki ajiyar zuciya kawai. Ji na yi AntyKhadija ta kama kafa’data ta furta “AYSHA idanunki kenan ko? Ko kunya babu ki ke kallona?” Na d’an saki baki, don ban san dalilin kalamin nata ba. Ta yi dariya ganin kamar na d’an firgita ta ce “Eh mana, yanzu yaushe k’afafunki su taka gida na? Tun ranar da Ustaz ya je ya d’auke Matarsa…” wani irin runtse ido na yi jin abinda ta ce. Sai naga ita ma ta dafa kanta ta furta “Oh Am Sorry Sisi, ni kai na bana son ambaton sunan mutumin can wallahi na tsane shi shi kuma Yayanku ya kafe ba laifinsa ba ne, ko shine a shoe d’insa abinda zai aikata kenan, yanzu dai ba wannan ba, yaushe za ki kawo min ziyara?” Ajiyar zuciya na saki, don kam ta famo min wani miki a zuciyata. Ranar d’aurin aure na da Ustaz ya je gidan Ya. Muhammad da duk abinda ya faru. Na lumshe idona kafin na bu’de su na ce “Zan zo duk ranar da Umma ta yarda.” Tana dariya ta ce “Ai kuwa yau zan tambayi Umma ta barki ki je, ko kya huta don na ga duk kin rame kamar ba Ayshatu y’ar Gaye ba.” Ta kira ni da sunan da Brothers d’ina suke kira na. Na d’an yi murmushi kawai jin abinda ta ce. A zuciyata kuwa addu’a nake Allah yasa Umma ta bar ni na je gidan Anty Khadija don macece mai karamci kuma ina sonta sosai. “Idan mun dawo d’aga kai lefe kawai sai mu yi tafiyar mu, In sha Allah zuk’eken mijinki na hanya wanda zai so ki da dukkan aibunki…” cikin mamaki nake kallonta na ce “Lefen wa za’a kai yau d’in?” Wani kallo take min ta ce “Baki san za’a kai lefen Umar da Usman ba yau?” Wasu k’walla na ji sun zubo min kawai na girgiza mata kai ina sunkuyar da kai na. Jikinta a sanyaye ta dafa ni, sai naga ta kasa magana ta cije leb’enta kawai ta shige parlorn Umman. Na runtse idona ina jin sautin zuciyata yana tashi daga normal zuwa wani irin bugu da ya dinga ba ni tsoro. Ba komai nake tsoro ba sai bana son ciwon zuciya ya kama ni. Tunani nake shi ma Ya.Usi ya daina ta tawa kenan shi yasa har aurensa zai zo bai gaya min ba. Tsabar ciwo da kaina yake da rawa da jikina yake da k’yar na samu na gama wankin na mik’e na shige d’akin da nake ina fasa wani irin kuka mai saka k’unci da ciwo a zuciya.

Kafin yamma kuwa gidan mu ya cika taf da mutane. Ina daga cikin d’aki ina jiyo hayaniyarsu sai dai ko da wasa ban yi gangancin shiga cikinsu ba. Na yi zama na a d’aki. Idona a lumshe don ko waya bani da ita tunda abin ya faru Abba ya saka Ya.Muhd ya k’wace wayar. Ji na yi an turo k’ofar d’akin da nake. Anty Khadija ce a tsaye tana kallona tana bin d’akin da kallo kuma duk a lokaci guda. Ta ce “Ke ba zaki fito ba ne AYSHA? Ki shirya a tafi ganin lefen da ke, wai ma me ki ke yi a store?” Wani malalacin murmushi na saki kafin na ce “Ba store ba ne, yanzu nan ne d’aki na Anty Khady.” Sai naga ta waro ido ta furta “Ah haba wasa ki ke, sai kace wacce ta yi kisan kai?” Ta d’an shigo tana sake k’arewa d’akin kallo. Ina kallon yarda take dakiya tana k’ok’arin kada k’wallar da take idonta ta zubo. “Tashi mu je, dole yau idan mutane suka watse zan yi wa Umma maganar ta bar ki koma gida na. Dama Arfa ta fara isata da saka magana ga shi kwanannan laulayi ya saka ni a gaba.” (Arfa yarinyar su ce da suka haifa na manta ban gaya muku ba.) girgiza kaina na yi na ce “Ku je kawai Anty ba inda za ni bana son shiga mutane.” Tana shirin sake magana aka turo k’ofar d’akin. Zinatu da Zaituna suna tafe suna wata irin shewa. Ina ganin su na mik’e zumbur daga tabarmar da nake kwance. Idanun su cikin nawa ba su yi magana ba har sai da suka gaishe da Anty Khady ta fice daga d’akin tukunna sannan suka juyo waje na. Zannira y’ar Umma Dije k’anwar Abba da yake bin sa. Ita kuma Zinatu y’ar k’anwar Umma ce Umma Sa’a. Da yake na gaya muku Abba da Umma first cousins ne auren zumunci aka musu. Sarai na san Zinatu da Zaituna basu da mutunci k’warai da gaske kuma a kansu Abba yake fa’da da iyayensu don kamar yarda ba su da kunya suma iyayensu ba kunyar ce da su ba. Inna ta sha fa’da min an sha fama da iyayensu suna y’an mata har sai da aka aurar da su ba shiri, sai ga shi sun haifo kwafinsu tsaf ko a ce wanda suka fi su. Ba sa wani zuwa gidan mu amma lokacin bikina suka zo suka tare a gidan sun doshi kwana goma da su aka yi komai a bikin. Duk da ban wani saba da su ba, Abba ya k’i bari na na saba da su don baya sake musu fuska.

Da murmushi na tare su, sai dai ga mamaki na sai naga sun wani zuba min harara suna min kallon banza. Zannira ta turo baki tana furta “Oh! Ikon Allah sai kuma ga karuwa a gidan Ashsheikh Imamu, waliyyin Allah!” Da sauri na waro ido ina kallon su, jin wulak’ancin da suka shirya yi min. Suka tuntsire da dariya Zinatu ta ce “Gane min hanya Zannira, yanzu kuma ban san ya zai yi ba? Mutum duk ya bi ya takura mana akan d’an shan Mintin da muke da samari, sai ga shi y’arsa tana abinda ya ci Uwar na mu, zigidir a kan cinyar saurayi da kayan maye, kai wannan abu ya yi min sugar na so na ga Idon Shehi Imamu ranar….” Wani irin kukan kura na yi na maku’reta da k’arfin gaske ina haki ina huci idona duk sun ka’da sun yi jajur, tun Zinnira na ganin kamar zata iya k’waceta ba tare da kowa ya ji ba har taga abin ya gagareta da sauri ta fita tana ihun a kawo d’auki jama’a AYSHA zata kashe Zinatu. Duk wasu jama’j da suke gidan suka yi yo dandazo zuwa d’aki na. Sai dai na k’i sakin Zinatu, ranar kam kamar an k’ara min k’arfi. A mak’ure nake da ita ina mata wani irin kallo. Anty Khadija na ji ta ja ni jikinta hakan yasa na kwanta lamo a jikin nata ina sakin wani irin kuka cikin kukan na bata labarin abinda ya faru… na kuma lumshe idona na ce “Anty a yanzu bayan Mami su ne mutane na biyu da nake zargi akan wancan vedion, ai ba k’arya na ne kowa yana fa’da ina kama da Zannira sosai da sosai jikin mu farcen mu duka iri guda ne, fuskar ce dai nake tunanin tawa suka saka a gangar jikin Zanniran!” Tsit na ji mutanen d’akin sun yi idanu kuma suka koma kan Zannira da cikin wani irin razani take ware ido tana pointing d’ina da yatsunta….

JIKAR NASHE★✍️
[10/16, 5:43 PM] Aunty Nazeefa 🥰: NA GA RAYUWA 30..

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
Chapter 6 · 0% Book details